Gálatas 4
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Ina cewa muddin magaji yaro ne, babu bambancin sa da bawa, ko da yake shine mai mallakan dukan kadarorin. 2A maimakon haka, yana karkashin masu jagora da amintattu har sai lokacin da mahaifinsa ya ajiye. 3Hakannan mu ma, lokaci da muke yara, an rike mu cikin kangi na tushin ka'idojin wannan duniya. 4Amma da lokacin ya yi daidai, Allah ya aiko da dansa, haihuwar mace, haihuwar karkashin shari'a. 5Ya yi haka ne domin ya fanshi wadanda ke a karkashin shari'a, domin mu karbi diyanci a matsayin 'ya'ya. 6Domin ku 'ya'ya ne, Allah ya aiko da Ruhun Dansa cikin zuciyarmu, Ruhun wanda ke kirar, “Abba, Uba.” 7Saboda wannan dalilin kai ba kuma bawa ba ne amma da. Idan kai da ne, hakannan kuma kai ma magaji ne ta wurin Allah. 8Duk da haka a da, da ba ku san Allah ba, bayi ne ku ga alloli wadanda ainihi ba alloli ba ne ko kadan. 9Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma, yanzu da Allah ya san ku, me ya sa kuke sake komawa zuwa ga tushen ka'idodin nan mara karfi da amfani? Kuna so ku sake komawa zaman bayi kuma daga farko? 10Kuna kiyaye ranaku na musamman, sabobin watanni, lokatai, da shekaru. 11Ina ji maku tsoro. Ina tsoro cewa kamar na yi aiki cikinku a wofi. 12Ina rokon ku 'yan'uwa, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma na zama kamar ku. Ba ku yi mani laifin komai ba. 13Amma kun sani cewa saboda rashin lafiya ne na yi maku shelar bishara da farko. 14Ko da yake halin da nake ciki cikin jiki a zahiri ya sa ku cikin gwaji, ba ku raina ni ba ko kuma kuka watsar da ni. A maimakon haka, kun karbe ni kamar mala'ikan Allah, kamar ni Almasihu Yesu ne da kansa. 15Saboda haka, yanzu ina murnar taku? Domin ina shaidar ku, idan mai yiwuwa ne, da kun kwakulo idanunku, kun ba ni. 16To kenan, na zama makiyin ku ne saboda na gaya maku gaskiya? 17Suna neman ku da himma ba domin wani alheri ba ne. Suna so su raba ni da ku domin ku bi su. 18Yana da kyau ko yaushe a yi himma domin dalilai masu kyau, ba kuma kawai sa'adda ina tare da ku ba. 19'Ya'yana kanana, sabili da ku ina cikin zafin nakuda kuma sai Almasihu ya samu kafuwa cikinku. 20Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canza muryata, domin ina damuwa a kanku kwarai. 21Ku gaya mani, ku da kuke marmarin ku zo karkashin shari'a, ba ku ji abin da shari'ar ta ce ba? 22A rubuce yake cewa, Ibrahim yana da 'ya'ya maza biyu, daya dan baiwa ne, dayan kuma dan 'yantaciyar mace ne. 23Abin lura anan, dan baiwar an haife shi ta hanyar mutuntaka ne, amma dan 'yantaciyar macen, an haife shi ta wurin alkawari ne. 24Ana iya bayyana abubuwan nan a hanyar kwatanci kamar haka, wadannan mata na kama da alkawarai ne guda biyu. Dayan alkawarin daga dutsen Sinayi ne. Ta haifi 'ya'ya da ke bayi ne su. Ita ce Hajaratu. 25Yanzu fa, Hajaratu ita ce dutsen Sinayi da ke Arebiya. Misali ce na Urushalima na yanzu, domin tana cikin bauta tare da 'ya'yanta. 26Amma Urushalima da ke bisa 'yantacciya ce, ita ce mahaifiyarmu. 27Kamar yadda yake a rubuce, “Ki yi murna, ke bakarariya, ke da ba ki taba haihuwa ba. Ki yi shewa na farinciki, ke da ba ki dandana haihuwan da ba. Domin 'ya'yan bakarariya da yawa suke, fiye da ta mace mai miji.” 28Yanzu fa, 'yan'uwa, kamar yadda Ishaku yake, haka muke, wato 'ya'yan alkawari. 29A lokacin can, shi wanda aka haife shi ta hanyar mutuntaka ya tsananta wa wanda aka haife shi ta hanyar Ruhu. Haka yake har yanzu. 30Amma menene nassi ya ce? “Ka kori baiwar nan tare da danta. Domin dan baiwar nan ba za ya ci gado tare da dan macen nan da ke 'yantacciya ba.” 31Saboda haka 'yan'uwa, mu ba 'ya'yan baiwa ba ne, a maimakon haka, mu 'ya'yan macen nan ne da ke 'yantacciya.

Você sabia?
Já não escravos, mas filhos
- Este capítulo diz que Abraão teve dois filhos, um da escrava e outro da mulher livre, e que as duas mulheres representam duas alianças. Agar, a escrava, era egípcia, serva de Sara, dada a Abraão como segunda esposa; seu filho foi Ismael. Isaque, único filho de Abraão com Sara, é o filho da promessa ao qual o capítulo compara seus leitores.Fontes: o próprio texto bíblico · Hagar · Isaac
- O capítulo identifica Agar com o monte Sinai, na Arábia, montanha também chamada Horebe. O Dicionário Bíblico de Easton (1897) descreve essa região montanhosa como o lugar a que os hebreus chegaram no terceiro mês depois do Êxodo, onde acamparam cerca de um ano, e situa a península do Sinai na Arábia Ocidental.Fontes: o próprio texto bíblico · Mount Sinai · Arabia
- O capítulo contrapõe a Jerusalém do seu próprio tempo, que diz estar escravizada com os seus filhos, à Jerusalém do alto, que chama de livre. O Dicionário Bíblico de Easton (1897) a chama de cidade santa e de cidade de Deus, e diz que o nome, na forma dual, significa posse da paz ou fundação da paz, referindo-se provavelmente aos montes Sião e Moriá ou, como alguns supõem, à cidade alta e à cidade baixa.Fontes: o próprio texto bíblico · Jerusalem
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Arabia · Hoje: Arabia Petraea · 30.070, 35.350 · versículo 25
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 25, 26
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org