Gálatas 3
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Ku Galatiyawa marasa wayo! Wanne mugun ido ya cuce ku? Ashe, ba Yesu Almasihu gicciyayye aka nuna a gaban idon ku ba? 2Ina so in gane wannan daga wurin ku ne kawai. Kun karbi Ruhun ta wurin ayyukan doka ne ko ta wurin ba da gaskiya ga abin da kuka ji? 3Rashin wayonku ya yi yawa haka ne? Kun fara da Ruhu, sai kuma yanzu ku karasa a cikin jiki? 4Kun fuskanci abubuwa da yawa a banza ne - har idan a banza ne? 5To, shi wanda ya ba ku Ruhun, da ayyuka masu iko a tsakanin ku, ya yi ne ta wurin ayyukan shari'a ko ta wurin ji tare da bangaskiya? 6Ibrahim ''ya ba da gaskiya ga Allah, kuma an lisafta mashi wannan a matsayin adalci.'' 7Ta wannan hanya ku fahimta su wadanda suka ba da gaskiya, 'ya'yan Ibrahim ne. 8Nassi ya riga ya hangi gaba cewa, ta wurin bangaskiya Allah zai baratar da Al'ummai. An yi wa Ibrahim shelar bishara tuntuni: ''A cikinka ne dukan al'ummai za su yi albarka.'' 9Saboda haka, wadanda suka ba da gaskiya, masu albarka ne tare da Ibrahim wanda ke da bangaskiya. 10La'ana na kan wadanda sun dangana ga ayyukan shari'a. Gama a rubuce yake, ''La'ananne ne kowanne mutum da bai tsaya ga duk abin da ke a rubuce cikin littafin shari'a ba, ya kuma aikata shi duka.”' 11Yanzu a sarari yake, Allah ba ya baratar da kowa ta wurin shari'a, domin ''Mai adalci zai rayu ta bangaskiya.'' 12Doka ba daga bangaskiya take ba, 'Amma a maimakon haka, “Shi wanda ke yin wadannan abubuwa cikin shari'a, zai yi rayuwa ta wurin shari'a.'' 13Almasihu ya fanshe mu daga la'anar shari'a da ya zama la'ananne saboda mu. Kamar yadda yake a rubuce, ''La'ananne ne duk wanda aka sargafe a bisa itace.'' 14Dalilin shine, albarkan da ke bisan Ibrahim ta zo ga al'ummai cikin Almasihu Yesu, domin mu samu karban alkawarin Ruhu ta wurin bangaskiya. 15'Yan'uwa, ina magana bisa ga ka'idojin mutane. Idan mutane sun yi yarjejeniya, babu mai kawar da shi ko a kara shi. 16Yanzu fa, an fada alkawaran nan ne ga Ibrahim da zuriyarsa. Bai ce, ''ga zuriya ba'' da manufar masu yawa; amma a maimakon haka ga daya kadai, ''ga zuriyar ka,'' wanda shine Almasihu. 17Yanzu na fadi wannan. Shari'a, wadda ta zo shekaru 430 daga baya, ba ta kawar da alkawarin da Allah ya tabbatar da shi ba tun a baya. 18Domin idan da gadon ya zo ta dalilin shari'a ne, da ba za ya zo kuma ta dalilin alkawari ba. Amma Allah ya ba da shi ga Ibrahim kyauta ta wurin alkawari. 19Me ya sa kenan aka ba da shari'a? An kara ta ne saboda laifuffuka, har sai zuriyar Ibrahim din nan ta zo ga wadanda aka yi masu alkawarinta. An kaddamar da ikon shari'ar ta wurin mala'iku, ta hannun matsakaici. 20Yanzu dai matsakanci yana nufin mutum fiye da daya, duk da haka Allah daya ne. 21Shari'a tana tsayayya da alkawaran Allah kenan? Ko kadan! Domin idan da an ba da shari'a da ke iya bayar da rai, babu shakka da adalci ya zo ta wurin wannan shari'a. 22A maimakon haka, nassi ya kulle abubuwa duka a karkashin zunubi. Allah ya yi wannan domin alkawarin sa na ceton mu ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ya samu a ba da shi ga wadanda suka gaskanta. 23Amma kafin bangaskiya cikin Almasihu ta zo, an kulle mu kuma aka tsare mu da shari'a har zuwa ga wahayin bangaskiya. 24Daga nan shari'a ta zama mana jagora har sai da Almasihu ya zo, domin mu samu baratarwa ta wurin bangaskiya. 25Yanzu da bangaskiya ta zo, ba mu kuma a karkashin jagora. 26Domin dukanku 'ya'yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Almasihu Yesu. 27Dukanku da aka yi wa baftisma cikin Almasihu, kun suturce kanku da Almasihu. 28Babu Bayahude ko Baheline, bawa ko 'yantacce, babu na miji ko mace, domin dukanku daya ne cikin Almasihu Yesu. 29Idan ku na Almasihu ne, ku zuriyar Ibrahim ne kenan, magada bisa ga alkawarin.

Você sabia?
A fé, a promessa e a lei
- Este capítulo diz que Abraão creu em Deus e que isso lhe foi creditado como justiça, e que os que têm fé são filhos de Abraão e herdeiros segundo a promessa. Um verbete de dicionário o chama de herdeiro das promessas e diz que ele foi nomeado antes dos irmãos mais velhos, Naor e Harã, porque ocupava esse lugar.Fontes: o próprio texto bíblico · Abraham
- O capítulo ensina que uma aliança humana, uma vez ratificada, não pode ser anulada nem alterada, e que a lei, vinda 430 anos depois, não revoga a promessa que Deus já havia concedido a Abraão. Uma cronologia data a peregrinação em Canaã e no Egito como iniciada em 1920 a.C. e com duração de 430 anos.Fontes: o próprio texto bíblico · Sojourn in Canaan and Egypt
- O capítulo diz que a Escritura previu que Deus justificaria os gentios pela fé e anunciou de antemão a Abraão o evangelho de que todas as nações seriam abençoadas por meio dele. Chamado pai de uma multidão, ele viveu na Caldeia até os setenta anos, depois deixou Ur por causa de um chamado de Deus e ficou quinze anos em Harã, cerca de 300 milhas ao norte.Fontes: o próprio texto bíblico · Abraham
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org