Gálatas 5
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Saboda 'yanci ne Almasihu ya yantar da mu. Sai ku dage kada ku sake komawa cikin kangin bauta. 2Duba, ni Bulus, ina gaya maku cewa idan an yi maku kaciya, Almasihu ba zai zama da amfani a gare ku ba a kowace hanya. 3Haka kuma, na shaida ga ko wanda mutum wadda aka yi masa kaciya ya zama dole ya yi biyayya da dukan shari'a. 4Kun rabu da Almasihu, dukanku wadanda aka “baratar” ta wurin shari'a. Kun fadi daga alheri. 5Domin ta wurin Ruhu, cikin bangaskiya, muna jira gabagadi na adalci. 6A cikin Almasihu kaciya ko rashin kaciya ba shi da ma'ana. Bangaskiya kadai mai aiki ta wurin kauna ita ce mafi muhimmanci. 7Da kuna tsere da kyau, wanene ya tsayar da ku daga yin biyayya da gaskiya? 8Rinjayarwa da ke sa yin wannan, ba daga wanda ya kira ku ba ne 9Ai karamin yisti shi yake sa dukan kulli ya kumbura. 10Ina da wannan gabagadin game da ku cikin Ubangiji cewa ba za ku yi tunani a wata hanya daban ba. Shi wanda ya rikita ku zai sha hukunci ko wanene shi. 11'Yan'uwa, idan har yanzu wa'azin kaciya nake yi, don me har yanzu ake tsananta mani? Inda haka ne dutsen sanadin tuntube game da gicciye da ya ragargaje. 12Ina fata wadanda suke badda ku su maida kansu babani. 13'Yan'uwa, domin Allah ya kira ku zuwa ga yanci, kada dai ku mori yancin nan ya zama zarafi domin jiki. A maimakon haka ta wurin kauna ku yi wa juna hidima. 14Saboda dukan shari'a ta cika ne a cikin doka guda daya; “Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.” 15Amma idan kuna cizo da hadiye juna, ku lura kada ku hallakar da junanku. 16Na ce, ku yi tafiya cikin Ruhu, ba za ku cika sha'awoyin jiki ba. 17Domin jiki yana gaba mai karfi da Ruhu, Ruhu kuma yana gaba da jiki. Domin wadannan akasin juna suke. Sakamakon shine ba za ku iya yin abin da kuke so ba. 18Amma idan Ruhu ne ke bishe ku, ba ku karkashin shari'a. 19Yanzu ayyukan jiki a bayyane suke. Sune al'amuran lalata, rashin tsarki, sha'awoyi, 20bautar gumaka, sihiri, yawan fada, jayayya, kishi, zafin fushi, gasa, tsattsaguwa, hamayya, 21hassada, buguwa, buguwa da tarzoma, da dai sauran irin wadannan abubuwa. Na gargade ku, kamar yadda a da na gargade ku, cewa wadanda suke aikata wadannan abubuwa ba za su gaji mulkin Allah ba. 22Amma 'ya'yan Ruhu kauna ne, farinciki, salama, hakuri, kirki, nagarta, bangaskiya, 23tawali'u, da kamun kai. Babu wata shari'a da ke gaba da wadannan abubuwa. 24Wadanda suke na Almasihu Yesu sun giciye halin jiki tare da marmarin sa da miyagun sha'awoyi. 25Idan muna zaune cikin Ruhu, mu yi tafiya da Ruhu. 26Kada mu zama masu girman kai, ko muna cakunar juna, ko muna kishin juna.

Você sabia?
A liberdade, a lei e o Espírito
- Quem fala identifica-se como Paulo e adverte que, se aqueles a quem se dirige se deixarem circuncidar, Cristo de nada lhes valerá, e que todo homem que se faz circuncidar fica obrigado a cumprir toda a lei. Um relato biográfico diz que o nome de circuncisão de Paulo era Saulo e que o nome Paulo provavelmente lhe foi dado na infância para uso no mundo dos gentios, enquanto Saulo seria o nome hebraico que ele usaria em casa.Fontes: o próprio texto bíblico · Paul
- A liberdade é contraposta a um jugo de escravidão: o capítulo diz que Cristo os libertou e manda que permaneçam firmes e não voltem a ser sobrecarregados por esse jugo. Foram chamados à liberdade, não como ocasião para a carne, mas para servir uns aos outros em amor, e toda a lei se cumpre no único preceito de amar o próximo como a si mesmo.Fontes: o próprio texto bíblico
- Andar pelo Espírito é contrastado com satisfazer os desejos da carne, que se opõem um ao outro. Se as pessoas são guiadas pelo Espírito, não estão debaixo da lei; o capítulo lista as obras da carne e o fruto do Espírito, e diz que contra essas coisas não há lei.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org