Efésios 5
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Saboda haka ku zama masu koyi da Allah, kamar kaunatattun 'ya'yansa. 2Ku yi zama cikin kauna kamar yadda Almasihu ya kaunace mu, ya kuma mika kansa sadaka da hadaya ga Allah dominmu, hadaya mai kanshi abin karba ga Allah. 3Fasikanci ko kowacce irin kazamta, ko kazamar lalata kada a ambace su a tsakaninku, don haka ya dace ga masu bi. 4Kada a ambaci batsa, maganar wauta ko alfasha wadanda ba su dace ba. Maimakon haka, mu zama masu godiya. 5Domin wannan kun sani cewa ba fasiki, ko mara tsarki, ko mai hadama wato mai bautar gumaka zai sami gado cikin mulkin Almasihu da Allah. 6Kada kowa ya rude ku da maganganun wofi. Saboda wadannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa kan kangararrun 'ya'ya. 7Kada ku yi tarayya tare da su. 8Domin da ku duhu ne, amma yanzu ku haske ne cikin Ubangiji. Sai ku yi tafiya kamar 'ya'yan haske. 9Saboda amfanin haske shine dukan alheri, adalci da gaskiya. 10Kuna bidar abin da Ubangiji ke murna da shi. 11Kada ku sa hannu ga ayyuka marasa amfani da ayyukan duhu amma gara a tone su. 12Don abubuwan da suke yi a boye abin kunya ne a bayyana su. 13Dukan abu, idan haske ya bayyana su, za a gan su. 14Domin duk abin da aka bayyana ya zama haske. Saboda haka aka ce, “Ka farka, kai mai barci, ka tashi daga cikin matattu; Almasihu kuwa zai haskaka bisanka”. 15Saboda haka, ku maida hankali yadda kuke rayuwar ku, ba kamar mutane marasa hikima ba amma kamar masu hikima. 16Ku yi lura yadda kuke amfani da lokaci don kwanakin miyagu ne. 17Kada ku zama wawaye. Maimakon haka, ku fahimci ko menene nufin Ubangiji. 18Kuma Kada ku bugu da ruwan inabi, don yana iya lalata rayuwa. Maimakon haka, ku cika da Ruhu Mai Tsarki. 19Kuna magana da junanku cikin zabura da wakoki da wakokin ruhaniya, kuna rairawa da yabo da zuciyarku ga Ubangiji. 20Kullum kuna ba da gaskiya domin dukan abubuwa cikin sunan Ubangiji Yesu ga Allah Uba. 21Kuna sarayadda kanku ga juna cikin girmama Almasihu. 22Mata, ku yi biyayya ga mazan ku kamar ga Ubangiji. 23Domin miji shine shugaban matarsa kamar yadda Almasihu yake shugaban ikilisiya. Shine kuma mai ceton jiki. 24Amma kamar yadda ikilisiya take biyayya ga Almasihu, haka kuma dole mata suyi ga mazajen su cikin kowanne abu. 25Mazaje, ku kaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya har ya ba da kansa dominta, 26Ya yi wannan domin ya tsarkake ta. Ya wanke mu da ruwan wanki ta wurin kalma. 27Ya yi wannan domin ya mika ma kansa ikilisiya mai daraja, ba tare da tabo ko cikas ko wani abu kamar wadannan, amma ta zama da tsarki da kuma mara aibi. 28Hakannan kuma, mazaje su kaunaci matansu kamar jikunnansu. Wanda yake kaunar matarsa yana kaunar kansa. 29Ba wanda ya taba kin jikinsa. Amma, yakan ciyadda shi yana kaunarsa, kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya. 30Domin mu gabobin jikinsa ne. 31“Domin wannan mutum zai rabu da ubansa da uwarsa ya manne wa matarsa, su biyu su zama nama daya”. 32Wannan asirin gaskiyar, da girma yake, amma ina magana ne game da Almasihu da ikilisiyarsa. 33Duk da haka, kowannenku dole ya kaunaci matarsa kamar kansa, matar kuma dole ta girmama mijinta.

Você sabia?
Amor, luz e o lar
- Efésios 5 começa chamando os leitores a imitar a Deus como filhos amados e a andar em amor, assim como Cristo os amou e se entregou por eles como oferta sacrificial de aroma agradável a Deus.Fontes: o próprio texto bíblico
- O capítulo diz que os leitores antes eram trevas, mas agora são luz no Senhor, e que o fruto da luz consiste em toda bondade, justiça e verdade. Cita também um dito que chama quem dorme a despertar e a levantar-se dentre os mortos, prometendo que Cristo brilhará sobre essa pessoa.Fontes: o próprio texto bíblico
- Um chamado a que uns se submetam aos outros por reverência a Cristo introduz as instruções para esposas e maridos. Diz-se aos maridos que amem suas esposas como Cristo amou a igreja e se entregou por ela, e o capítulo chama a união de marido e mulher de mistério profundo que diz respeito a Cristo e à igreja.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org