Nations Bible

Efésios 4

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Saboda haka a matsayi na na dan sarka saboda Ubangiji; ina rokon ku ku yi zaman rayuwa da ta cancanci kiran da Allah ya kiraye ku. 2Ku zamna da matukar tawali'u da sahihanci da hakuri. Ku karbi juna cikin kauna. 3Ku yi kokarin zaman dayantaka cikin Ruhu kuna hade cikin salama. 4Akwai jiki daya da kuma Ruhu daya, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan daya. 5Ubangiji daya, bangaskiya daya, da kuma baftisma daya. 6Allah daya ne da Uban duka. Shine bisa duka, ta wurin duka, da kuma cikin duka. 7Ko wannenmu an ba shi baiwa bisa ga awon baiwar Almasihu. 8Kamar yadda nassi ya ce, “Da ya haye zuwa cikin sama, ya bi da bayi cikin bauta. Ya kuma yi wa mutane baye baye. 9Menene ma'anar, “Ya hau?” Ana cewa kenan ya sauka har cikin zurfin kasa. 10Shi da ya sauka shine kuma wanda ya hau birbishin sammai. Ya yi wannan domin ya cika dukan abubuwa. 11Almasihu ya ba da baye baye kamar haka: manzanni, annabawa, masu shelar bishara, makiyaya, da masu koyarwa. 12Ya yi haka domin ya shiryar da masu bi saboda hidima, domin gina jikin Almasihu. 13Ya yi haka har sai mun kai dayantakar bangaskiya da sanin Dan Allah. Ya yi haka har sai mun kai ga manyanta, kamar wadanda suka kai cikakken matsayin nan na falalar Almasihu. 14Wannan ya zamanto haka domin kada mu kara zama kamar yara. Kada a yi ta juya mu. Wannan haka yake domin kada mu biye wa iskar kowacce koyarwa ta makirci da wayon mutane masu hikimar yin karya. 15Maimakon haka za mu fadi gaskiya cikin kauna domin mu yi girma cikin dukan tafarkun da ke na sa, shi da yake shugaba, Almasihu. 16Almsihu ya hada dukan jikin masu ba da gaskiya. Jikin yana hade ta wurin kowanne gaba, domin jikin ya yi girma ya gina kansa cikin kauna. 17Saboda haka ina yi maku gargadi cikin Ubangiji cewa, kada ku sake yin rayuwa irin ta al'ummai da suke yi cikin azancin wofi marar amfani. 18Sun duhunta cikin tunaninsu. Bare suke da rai irin na Allah, ta wurin jahilcin da ke cikinsu da ta wurin taurare zukatansu. 19Basa jin kunya. Sun mika kansu ga mutumtaka ta yin kazamtattun ayyuka da kowacce zari. 20Amma ba haka kuka koyi al'amuran Almasihu ba. 21Ina zaton kun rigaya kun ji a kansa. Ina zaton an koyar da ku cikinsa, kamar yadda gaskiyar Yesu ta ke. 22Dole ku yarda halin ku na da, wato tsohon mutum. Tsohon mutumin ne ya ke lalacewa ta wurin mugun buri. 23Ku yarda tsohon mutum domin a sabonta ku cikin ruhun lamirinku. 24Ku yi haka domin ku yafa sabon mutum, mai kamanin Allah. An hallitta shi cikin adalci da tsarki da gaskiya. 25Saboda haka ku watsar da karya. “Fadi gaskiya ga makwabcin ka”, domin mu gabobin juna ne. 26“Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi.” Kada ku bari rana ta fadi kuna kan fushi. 27Kada ku ba shaidan wata kofa. 28Duk mai yin sata, kada ya kara yin sata kuma. Maimakon haka, ya yi aiki. Ya yi aiki da hannuwan sa domin ya sami abin da zai taimaka wa gajiyayyu. 29Kada rubabbun maganganu su fito daga cikin bakinku. Maimakon haka, sai ingantattu da za su ba da alheri ga masu ji. 30Kada ku bata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai domin ta wurin sa ne aka hatimce ku domin ranar fansa. 31Sai ku watsar da dukan dacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da reni tare da dukan mugunta. 32Ku yi wa juna kirki, ku zama da taushin zuciya. Ku yafe wa juna, kamar yadda Allah cikin Almasihu ya gafarta maku.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Um só corpo e uma vida digna

  • O capítulo começa com o autor chamando a si mesmo de prisioneiro no Senhor e exortando os leitores a andar de modo digno da vocação que receberam, com humildade, mansidão, paciência e diligência para preservar a unidade do Espírito pelo vínculo da paz.Fontes: o próprio texto bíblico
  • Esse apelo se apoia em realidades compartilhadas nomeadas no capítulo: um só corpo, um só Espírito, uma só esperança, um só Senhor, uma só fé, um só batismo e um só Deus e Pai de todos, que está sobre todos, por meio de todos e em todos. O mesmo trecho diz que aquele que subiu deu uns para apóstolos, outros para profetas, outros para evangelistas e outros para pastores e mestres, a fim de capacitar os santos e edificar o corpo.Fontes: o próprio texto bíblico
  • O capítulo então descreve uma vida mudada como o ato de despir-se do modo de vida anterior, o velho eu, e de revestir-se do novo eu. Diz aos leitores que abandonem a mentira e falem a verdade, pois são membros uns dos outros; que fiquem irados sem pecar e não deixem o sol se pôr sobre a ira; e que não entristeçam o Espírito Santo de Deus, no qual foram selados para o dia da redenção.Fontes: o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.