Nations Bible

Efésios 6

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1'Ya'ya, ku yi biyayya ga iyayenku chikin Ubangiji, domin wannan daidai ne. 2“Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka” (Doka ta fari kenan da alkawari), 3“ta haka za ku yi albarka, domin kwanakinku su yi tsawo a duniya”. 4Hakanan, ku ubanni kada ku cakuni 'ya'yan ku har su yi fushi, amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargadinsa. 5Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya tare da girmamawa da tsoro da zuciya mai gaskiya. Ku yi masu biyayya kamar ga Almasihu. 6Ku yi masu biyayya ba don lallai suna kallonku ba domin ku faranta masu rai. Maimakon haka, ku yi biyayya kamar bayi ga Almasihu. Ku yi nufin Allah daga zuciya. 7Ku yi hidima da dukan zuciya, kamar kuna bautar Ubangiji ba mutane ba. 8Sai ku sani cewa duk abinda mutum ya yi zai karbi sakamako daga wurin Ubangiji, ko shi bawa ne ko 'yantacce. 9Ku kuma iyayengiji, ku yi irin wannan ga barorin ku. Kada ku razana su. Kun sani shi wanda ke Ubangijinsu da ku daya ne yana sama. Kun sani tare da shi baya nuna tara. 10A karshe, ku karfafa cikin Ubangiji da cikin karfin ikonsa. 11Ku dauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa gaba da dabarun shaidan. 12Gama yakinmu ba da nama da jini bane. Amma, da ikoki da mulkoki da mahukuntan wannan zamani mai duhu da rundunai masu duhu na mugunta cikin sammai. 13Don haka ku dauki dukan makamai na Allah, domin ku iya tsayawa da karfi cikin muguwar rana. Bayan kun yi komai za ku tsaya da karfi. 14Saboda haka ku tsaya da karfi. Ku yi wannan bayan kun yi damara cikin gaskiya kuna yafa sulke na adalci. 15Ku yi wannan bayan kun daure kafafunku da shirin kai bisharar salama. 16Cikin dukan abu ku dauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku kashe dukan kibau masu wuta na mugun. 17Ku dauki kwalkwalin ceto da takobin Ruhu, wanda shine maganar Allah. 18Tare da kowacce irin addu'a da roko kuna addu'a kullum cikin Ruhu. Da wannan lamiri, kuna tsare wannan da iyakacin kula da dukan juriya da roko saboda dukan masu bi. 19Ku yi mani addu'a, domin in karbi sako duk sa'adda na bude bakina. Ku yi addu'a in sami gabagadin bayyana boyayyar gaskiyar bishara. 20Saboda bishara nake jakada cikin sarkoki, yadda a cikinta zan yi magana gabagadi yadda takamata. 21Amma domin ku san rayuwa ta, da yadda nake, Tikikus, dan'uwa kaunatacce da amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai sanar da ku dukan abu. 22Saboda wannan dalili na aiko shi gare ku, domin ku san al'amuran mu, kuma domin ku sami ta'aziya a zukatan ku. 23Bari salama ta kasance tare da 'yan'uwa, kauna da bangaskiya daga wurin Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu. 24Alheri ya kasance tare da wadannan da suke kaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu tare da kauna mara mutuwa.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Deveres da casa, a armadura de Deus e Tíquico

  • Este capítulo apresenta o mandamento de honrar pai e mãe como o primeiro que vem com uma promessa: que tudo vá bem e que se tenha longa vida na terra. Também pede aos pais que não provoquem os filhos à ira, mas que os criem na disciplina e na instrução do Senhor.Fontes: o próprio texto bíblico
  • O capítulo diz que a luta não é contra carne e sangue, mas contra governantes, autoridades, os poderes das trevas deste mundo e as forças espirituais do mal nas regiões celestiais. Os leitores são chamados a tomar toda a armadura de Deus — o cinto da verdade, a couraça da justiça, os pés preparados com a prontidão do evangelho da paz, o escudo da fé, o capacete da salvação e a espada do Espírito, que é a palavra de Deus — para ficarem firmes quando chegar o dia do mal.Fontes: o próprio texto bíblico
  • Quem escreve pede oração para anunciar o evangelho sem medo, como embaixador em cadeias, e envia Tíquico, o irmão amado e servo fiel no Senhor, para contar aos leitores como ele está e animá-los. Tíquico é descrito como um cristão da Ásia que, com Trófimo, acompanhou Paulo em parte da viagem da Macedônia a Jerusalém e esteve com Paulo em Roma, de onde foi enviado a Éfeso, provavelmente para edificar e encorajar a igreja.Fontes: o próprio texto bíblico · Tychicus

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.