Revelation 11
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Aka bani sanda in yi amfani da ita kamar sandar awo. Aka ce mani, “Tashi ka auna haikalin Allah da bagadi, da wadanda ke sujada a cikinsa. 2Amma kada ka auna harabar haikalin, domin an ba da shi ga Al'ummai. Za su tattake birnin mai tsarki har wata arba'in da biyu. 3Zan ba shaidu na biyu iko su yi anabci na kwanaki dubu daya da dari biyu da sittin, sanye da tsummoki. 4Wadannan shaidu sune itatuwan zaitun biyu da kuma fitilu biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya. 5Idan wani ya yi niyyar cutar da su, wuta na fitowa daga bakinsu ta lashe makiyansu. Duk mai son cutar da su, dole a kashe shi ta wannan hanya. 6Wadannan shaidu suna da iko su kulle sama domin kada a yi ruwa a lokacin da suke anabci. Suna da iko su juya ruwaye su zama jini, su kuma bugi duniya da kowacce irin annoba duk lokacin da suka ga dama. 7Sa'adda suka gama shaidarsu, dabban da ke fitowa daga rami marar iyaka zai yi yaki da su. Zai ci nasara da su ya kashe su. 8Gawawwakinsu zasu kwanta kan hanyar babban birnin nan (wanda ma'anar sa ake kira Saduma da Masar) inda aka gicciye Ubangijinsu. 9Wajen kwana uku da rabi wadansu daga dukan mutane, da kabila, da harshe, da al'umma za su yi kallon gawawwakinsu. Za su ki yarda a sa su cikin kabari. 10Mazaunan duniya zasu yi murna da biki a kansu. Har za su aika wa juna kyautai saboda annabawan nan biyu da suka azabtar da mazaunan duniya. 11Amma bayan kwana uku da rabi, numfanshin rai daga wurin Allah zai shiga cikinsu sa'annan za su tsaya a kan kafafunsu. Matsanancin tsoro zata fado kan wadanda za su gansu. 12Sa'annan zasu ji murya mai kara daga sama tana ce masu, “Ku hauro nan!” Sa'annan za su tafi sama cikin gajimarai, makiyansu suna kallo. 13A waccan sa'a za a yi babbar girgizar kasa, sai kashi daya cikin goma na garin ya fadi. Mutane dubu bakwai za su mutu a girgizar kasar, wadanda suka tsira kuwa za su tsorata su ba da daukaka ga Allah na sama. 14Annoba ta biyu ta wuce. Duba! Annoba ta uku tana zuwa nan da nan. 15Sa'annan mala'ika na bakwai ya busa kahonsa, sai muryoyi masu kara suka yi magana cikin sama cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa. Zai yi mulki har abada abadin.” 16Sa'annan dattawan nan ashirin da hudu da ke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fadi fuskokinsu na kasa. Suka yi wa Allah sujada. 17Suka ce, “Mun yi maka godiya, Ubangiji Allah, Madaukaki, wanda yake yanzu da wanda yake a da, saboda ka dauki ikonka mai girma ka fara mulki. 18Al'ummai suka fusata, amma hasalar ka ta zo. Lokaci ya zo da za a yi wa mattatu sharia, da zaka ba da sakamako ga bayinka annabawa, da masu ba da gaskiya, da wadanda suka ji tsoron sunanka, karami da babba. Lokaci kuma ya yi da za ka hallaka wadanda ke hallakar da duniya.” 19Sa'annan aka bude haikalin Allah da ke sama, sai aka ga akwatin alkawarinsa a cikin haikalinsa. Sai ga hasken walkiya, da rugugi, da aradu, da girgizar kasa, da manyan duwatsun kankara.

Did you know?
The Two Witnesses and the Great City
- Revelation 11 says that the bodies of the two witnesses will lie in the street of the great city, figuratively called Sodom and Egypt, where their Lord was also crucified. A dictionary entry explains Sodom as Burning, or the walled, a city destroyed by fire from heaven because of its inhabitants' wickedness, a destruction that Scripture frequently recalls. Egypt, the land of the Nile and the pyramids, is likewise described as holding great significance in Scripture.Sources: the Bible text itself
- The two witnesses are empowered to prophesy for 1,260 days, clothed in sackcloth. They are the two olive trees and the two lampstands that stand before the Lord of the earth, and they have power to shut the sky so that no rain falls, to turn the waters into blood, and to strike the earth with every kind of plague.Sources: the Bible text itself
- When the two witnesses finish their testimony, the beast that comes up from the Abyss overpowers and kills them. For three and a half days, peoples, tribes, tongues, and nations view their bodies and will not permit them to be laid in a tomb, while the earth's inhabitants gloat over them, celebrate, and send one another gifts, because the two prophets had tormented them. After that, the breath of life from God enters them; they stand on their feet and go up to heaven in a cloud as their enemies watch.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org