Revelation 12
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Aka ga wata babbar alama a sama: wata mace ta yi lullubi da rana, kuma wata na karkashin kafafunta; rawanin taurari goma sha biyu na bisa kanta. 2Tana da ciki, tana kuma kuka don zafin nakuda - a cikin azabar haihuwa. 3Sai aka ga wata alama cikin sama: Duba! Akwai wani katon jan maciji mai kawuna bakwai da kahonni goma, sai kuma ga kambi guda bakwai bisa kawunansa. 4Wutsiyarsa ta share daya bisa uku na taurari a sama ta zubo su kasa. Diragon nan ya tsaya a gaban matar da ta kusan haihuwa, domin lokacin da ta haihu ya lankwame yaronta. 5Sai ta haifi da, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al'ummai da sandar karfe. Aka fizge yaron ta zuwa ga Allah da kursiyinsa, 6matar kuwa ta gudu zuwa jeji inda Allah ya shirya mata domin a iya lura da ita kwanaki 1, 260. 7A lokacin sai yaki ya tashi a sama. Mika'ilu da mala'ikunsa suka yi yaki da diragon, sai diragon da nasa mala'iku suka yake su su ma. 8Amma diragon ba shi da isashen karfin da zai ci nasara. Don haka, shi da mala'ikunsa ba su kara samun wuri a sama ba. 9Sai aka jefa katon diragon nan tare da mala'ikunsa kasa, wato tsohon macijin nan da ake kira Iblis ko Shaidan wanda ke yaudarar dukan duniya. 10Sai na ji wata murya mai kara a sama: “Yanzu ceto ya zo, karfi, da mulkin Allahnmu, da iko na Almasihunsa. Gama an jefar da mai sarar 'yan'uwanmu a kasa - shi da yake sarar su a gaban Allah dare da rana. 11Suka ci nasara da shi ta wurin jinin Dan Ragon da kuma shaidar maganarsu, gama ba su kaunaci ransu ba, har ga mutuwa. 12Don haka, yi farinciki, ya ku sammai da duk mazauna da ke cikinsu. Amma kaito ga duniya da teku saboda iblis ya sauko gare ku. Yana cike da mummunan fushi, domin ya san lokacin sa ya rage kadan. 13Da diragon ya ga an jefar da shi kasa, sai ya fafari matar nan da ta haifi da namiji. 14Amma aka ba matar nan fukafukai biyu na babbar gaggafa domin ta gudu zuwa inda aka shirya mata a jeji. A wannan wuri ne za a lura da ita na dan lokaci, da lokatai, da rabin lokaci - a lokacin da babu macijin. 15Macijin ya kwararo ruwa daga bakin sa kamar kogi, don ya kawo ambaliyar da zai kwashe ta. 16Amma kasa ta taimaki matar. Kasa ta bude bakinta ta hadiye kogin da diragon ya kwararo daga bakinsa. 17Sai diragon ya fusata da matar, sai ya tafi ya yi yaki da sauran zuriyarta, wadanda suka yi biyayya da umarnan Allah suna kuma rike da shaida game da Yesu. 18Sai diragon ya tsaya a kan yashi, a gaban teku.
Did you know?
The Woman, the Dragon, and War in Heaven
- In this chapter the huge red dragon is named outright as the ancient serpent called the devil and Satan, the deceiver of the whole world. Easton's Bible Dictionary (1897) explains that Satan means adversary or accuser, and that in the New Testament the name is used interchangeably with devil. A voice in heaven then calls him the accuser of our brothers, who accuses them day and night before God.Sources: the Bible text itself · Satan
- Michael and his angels fight the dragon in this chapter. Easton's Bible Dictionary (1897) calls Michael one of the chief angels and says he had special charge of Israel as a nation. The same entry links him with the old serpent called the devil and Satan, who deceives the whole world, citing Revelation 12:7-9.Sources: the Bible text itself · Michael
- Easton's Bible Dictionary (1897) lists the dragon and the old serpent among Satan's titles, citing Revelation 12:9. The chapter itself moves between those images: after the dragon is hurled down, the woman is given two wings of a great eagle to flee the serpent, and water like a river pours from the serpent's mouth to sweep her away.Sources: Satan · the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org