Revelation 10
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Sa'anan na ga wani babban mala'ika yana zuwa daga sama. Yana lullube cikin girgije, a bisa kansa akwai bakangizo. Fuskarsa kamar rana, kafafunsa kamar ginshikan wuta. 2Yana rike da karamin littafi a hannunsa, da aka bude, sai ya sa kafarsa ta dama a bisa teku, kafarsa ta hagu kuma a kan kasa. 3Sai yayi ihu da babbar murya kamar zaki mai ruri. Lokacin da ya yi ihu, tsawan nan bakwai suka yi magana da karar su. 4Da tsawan nan bakwai suka yi magana, ina dab da rubutu, amma na ji wata murya daga sama cewa, “Ka rike asirin abin da tsawan nan bakwai suka fada. Kada ka rubuta shi.” 5Sai mala'ikan da na gani tsaye bisa teku da kasa, ya daga hannun damarsa sama. 6Sai ya rantse da wannan da ke raye har abada abadin - wanda ya halicci sama da duk abinda ke cikinsa, da duniya da duk abin da ke a kanta, da teku da dukan abin da ke cikinsa, sai mala'ikan ya ce, “Babu sauran jinkiri. 7Amma a ranar da mala'ika na bakwai yana dab da busa kahonsa, a lokacin ne asirin Allah zai cika, daidai da yadda ya sanar wa bayinsa annabawa.” 8Muryar da na ji daga sama ta sake magana da ni: “Tafi, ka dauki budadden littafin da ke hannun mala'ikan da ke tsaye bisa teku da kan kasa.” 9Sai na tafi wurin mala'ikan na ce da shi ka bani karamin littafin. Yace dani, “Dauki littafin ka ci. Zai sa cikinka ya yi daci, amma a bakinka zai yi zaki kamar zuma.” 10Na dauki karamin littafin daga hannun mala'ikan na ci. Ya yi zaki sosai a bakina kamar zuma, amma da na ci, sai cikina ya zama da daci. 11Wani yace mani, “Dole ka sake yin annabci kuma game da mutane masu yawa, da al'ummai, da harsuna da sarakuna.”

Did you know?
The Angel, the Sealed Thunders, and the Scroll
- A mighty angel comes down from heaven, wrapped in a cloud, with a rainbow above his head, a face like the sun, and legs like pillars of fire. He holds a small scroll that lies open, and he places his right foot on the sea and his left foot on the land.Sources: the Bible text itself
- When the angel cries out like a roaring lion, seven thunders speak. The narrator is about to write down what they said, but a voice from heaven commands that it be sealed and not written down. Standing on the sea and on the land, the angel lifts his right hand to heaven and swears by the One who lives forever and ever, who created heaven and everything in it, the earth and everything in it, and the sea and everything in it, that there will be no more delay, yet in the days when the seventh angel is about to sound his trumpet the mystery of God will be fulfilled, just as He proclaimed to His servants the prophets.Sources: the Bible text itself
- A voice from heaven tells the narrator to take the small open scroll from the angel’s hand. The angel says to eat it, warning that it will be sweet as honey in the mouth but bitter in the stomach. The narrator eats it and finds it so, and is then told to prophesy again about many peoples, nations, tongues, and kings.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org