Matthew 16
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Sai Farisawa da Sadukiyawa suka zo su gwada shi suka roke shi ya nuna masu alama daga sama. 2Amma ya amsa ya ce masu, “Lokacin da yamma ta yi, sai ku ce, 'Za a yi yanayi mai kyau, domin sama ta yi ja,' 3Kuma da safe ku ce, 'Zai zama yanayi mara kyau a yau, domin sama ta yi ja ta kuma gama gari, kun san yadda za ku bayyana kammanin sararin sama, amma ba ku iya bayyana alamun lokaci ba. 4Mugun zamani, maciya amana suna neman alama, amma babu wata alama da za a nuna sai ta Yunusa.” Daga nan sai Yesu ya tafi. 5Almajiran suka zo daga wancan gefe, amma sun manta su dauki gurasa, 6Yesu ya ce masu, “Ku kula ku kuma mai da hankali da yisti na Farisawa da Sadukiyawa.” 7Sai almajiran suka fara magana da junansu suka ce, “Ko saboda bamu kawo gurasa bane.” 8Yesu yana sane da wannan sai ya ce, “Ku masu karancin bangaskiya, don me ku ke magana a tsakaninku cewa ko don bamu kawo gurasa bane? 9Ba ku gane ko tuna da gurasa guda biyar da aka ciyar da mutum dubu biyar, kuma kwando nawa kuka tara ba? 10Ko gurasa bakwai ga mutum dubu hudu, da kuma kwanduna nawa kuka dauka ba? 11Yaya kuka kasa fahimta cewa ba game da gurasa nake yi maku magana ba? Ku yi hankali ku kuma lura da yistin Farisawa da Sadukiyawa.” 12Sa'annan suka fahimta cewa ba yana gaya masu su yi hankali da yistin da ke cikin gurasa ba ne, amma sai dai su yi lura da koyarwar Farisawa da Sadukiyawa. 13A lokacin da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, ya tambayi almajiransa, cewa, “Wa mutane ke cewa Dan Mutum yake? 14Suka ce, “Wadansu suna cewa Yahaya mai baftisma; wadansu Iliya, saura suna cewa Irmiya, ko daya daga cikin annabawa.” 15Ya ce masu, “Amma ku wa kuke ce da ni?” 16Sai Saminu Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu, Dan Allah mai rai.” 17Yesu ya amsa ya ce masa, “Mai albarka ne kai, Saminu dan Yunusa, don ba nama da jini ba ne ya bayyana maka wannan, amma Ubana wanda ke cikin sama. 18Ina kuma gaya maka cewa kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikilisiya ta. Kofofin hades ba za su yi nasara da ita ba. 19Zan ba ka mabudan mulkin sama. Duk abin da ka kulla a duniya zai zama abin da an kulla a cikin sama, kuma duk abinda ka warware a duniya a warware yake cikin sama,” 20Sai Yesu ya umarci almajiransa kada su gaya wa kowa cewa shi ne Almasihu. 21Daga lokacin nan Yesu ya fara gaya wa almajiransa cewa dole ne ya tafi Urushalima, ya sha wahala mai yawa a hannun dattawa, da manyan firistoci da malaman attaura, a kashe shi, a tashe shi zuwa rai a rana ta uku. 22Sai Bitrus ya kai shi a gefe ya tsauta masa, cewa, “Wannan ya yi nesa da kai, Ubangiji; wannan ba zai taba faruwa da kai ba.” 23Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka koma bayana, Shaidan! Kai sanadin tuntube ne gare ni, domin ba ka damuwa da abubuwan da suke na Allah, amma sai abubuwan mutane.” 24Sa'annan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk wanda yake so ya bi ni, lallai ne ya ki kansa, ya dauki gicciyensa, ya bi ni. 25Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi. Duk wanda ya rasa ransa domina zai same shi. 26Domin wace riba mutum zai samu in ya sami dukan duniya ya rasa ransa? Me mutum zai iya bayarwa a maimakon ransa? 27Domin Dan Mutum zai zo ne cikin daukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. Sa'annan ne zaya biya kowane mutum bisa ga ayyukansa. 28Gaskiya ina gaya maku, akwai wadansun ku da ke tsaye a nan, da ba za su dandana mutuwa ba sai sun ga Dan Mutum na zuwa cikin mulkinsa.”

Did you know?
Peter's confession and the way of the cross
- Caesarea Philippi, where Jesus asked who people said the Son of Man was, stood near the base of Mount Hermon at the upper source of the Jordan, 20 miles north of the Sea of Galilee and 120 miles north of Jerusalem. Easton's Bible Dictionary (1897) calls this the northern limit of his public ministry. According to some, the place had earlier been a Canaanite sanctuary of Baal; it was afterwards called Paneas.Sources: Caesarea Philippi · the Bible text itself
- When the Pharisees and Sadducees asked for a sign from heaven, Jesus said that a wicked and adulterous generation would be given only the sign of Jonah. Easton's Bible Dictionary (1897) describes Jonah, son of Amittai of Gath-hepher, as a prophet of Israel sent as a missionary to Nineveh, and presents him as a type of the Son of Man.Sources: Jonah · the Bible text itself
- Simon, whom Jesus here calls Peter, was a fisherman from Bethsaida and the son of Jonah. Easton's Bible Dictionary notes that Simon, meaning "hearing," was a very common Jewish name in the New Testament. When Peter rebuked the saying that Jesus must go to Jerusalem, suffer, be killed, and be raised on the third day, Jesus answered, "Get behind me, Satan"; the same dictionary defines Satan as "adversary" or "accuser," a name it also uses for the one who tempted Jesus in the wilderness.Sources: Simon Peter · Satan · the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org