Nations Bible

Matthew 15

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Sai wadansu Farisawa da malamai suka zo wurin Yesu daga Urushalima. Su ka ce, 2“Meyasa almajiranka suke karya al'adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci.” 3Yesu ya amsa masu ya ce, “Kuma don me ku ke karya dokar Allah saboda al'adunku? 4Domin Allah ya ce, 'Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka; 'Shi wanda ya yi muguwar magana ga mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lallai zai mutu. 5Amma kun ce, “Duk wanda ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, “Kowanne taimako da za ka samu daga gare ni yanzu baiko ne ga Allah,'” 6wannan mutum ba ya bukatar ya girmama mahaifinsa. Ta wannan hanya kun maida maganar Allah wofi saboda al'adunku. 7Ku munafukai, daidai ne Ishaya ya yi annabci akan ku da ya ce, 8“ Wadannan mutane girmama ni da baki kawai suke yi, amma zukatansu nesa suke da ni. 9Suna mani sujada a banza, domin suna koyar da dokokin mutane a matsayin rukunansu.” 10Sai ya kira taron mutane zuwa gare shi ya ce masu, “Ku saurara ku fahimta, 11ba abin da ke shiga baki ke kazantar da mutum ba. Sai dai, abin da ke fitowa daga baki, wannan shi ya ke kazantar da mutum.” 12Sai al'majiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisawa ba su ji dadi ba da suka ji maganan nan?” 13Yesu ya amsa ya ce, “Kowace shuka wadda ba Ubana na sama ya shuka ba za a tuge ta. 14Ku kyale su kawai, su makafin jagora ne. In makaho ya ja wa wani makaho gora dukan su za su fada rami.” 15Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ka bayyana wannan misali a garemu,” 16Yesu ya ce, “Ku ma har yanzu ba ku da fahimta? 17Ko baku gani ba duk abin da ke shiga baki zuwa ciki ta haka yake fita zuwa salga? 18Amma abubuwan da ke fita daga baki suna fitowa ne daga zuciya. Su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. 19Domin daga zuciya mugayen tunani suke fitowa, kisan kai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, da zage-zage. 20Wadannan su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. Amma ci da rashin wanke hannu baya kazantar da mutum.” 21Sai Yesu ya tafi daga nan ya nufi yankin biranen Taya da Sidon. 22Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce,” Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani.” 23Amma Yesu bai ce mata kome ba. Almajiransa suka zo suka roke shi, suna cewa, “Ka sallame ta, domin tana bin mu da ihu.” 24Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba a aike ni gun kowa ba sai dai ga batattun tumakin gidan Isra'ila.” 25Amma ta zo ta durkusa a gabansa, tana cewa, “Ubangiji ka taimake ni.” 26Ya amsa ya ce, “Ba daidai bane a dauki gurasar yara a jefa wa kananan karnuka. 27Ta ce, “I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida.” 28Sai Yesu ya amsa ya ce mata, “Mace, bangaskiyarki tana da girma. Bari ya zamar maki yadda ki ke so.”'Yarta ta warke a lokacin. 29Yesu ya bar wurin ya tafi kusa da tekun Galili. Sai ya hau tudu ya zauna a can. 30Taro mai yawa suka zo gunsa. Suka kawo masa guragu, makafi, bebaye da nakasassun mutane da yawa, da wadansu marasa lafiya. Suka kawo su gaban Yesu, sai ya warkar da su. 31Don haka mutane da yawa suka yi mamaki a lokacin da suka ga bebaye suna magana, nakasassu sun warke, guragu suna tafiya, makafi suna gani. Sai suka daukaka Allah na Isra'ila. 32Yesu ya kira almajiransa zuwa gun sa sai ya ce, “Ina jin tausayin taron, sun kasance tare da ni kwana uku ke nan kuma ba su da abin da za su ci. Bana so in sallame su ba tare da sun ci abinci ba, domin kada su suma a hanya.” 33Almajiran suka ce masa, “A ina zamu sami isasshiyar gurasa a wannan wuri da babu kowa har ta ishi babban taron nan.” 34Yesu ya ce masu, “Gurasa nawa ku ke da ita?” Suka ce, “Bakwai da 'yan kifi marasa yawa.” 35Sai Yesu ya umarci taron su zauna a kasa. 36Ya dauki gurasar nan bakwai da kifin, bayan ya yi godiya, ya kakkarya gurasar ya bada ita ga almajiran Sai almajiran suka ba taron. 37Jama'a duka suka ci suka koshi. Suka tattara gutsattsarin abincin da ya rage, kwando bakwai cike. 38Wadanda suka ci su dubu hudu ne maza, banda mata da yara. 39Sai Yesu ya sallami taron ya shiga cikin jirgin ruwa ya tafi yankin Magadan.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Tradition, the coast of Tyre, and bread by the lake

  • Pharisees and scribes came from Jerusalem and asked why Jesus’ disciples ate without washing their hands, treating that as a break with the tradition of the elders. He answered by quoting Isaiah, whom Easton's Bible Dictionary (1897) identifies as the son of Amoz and places in the reigns of Uzziah, Jotham, Ahaz, and Hezekiah, on people who honor God with their lips while their hearts are far away.Sources: the Bible text itself · Isaiah
  • Jesus then withdrew to the district of Tyre and Sidon, where a Canaanite woman begged him to heal her daughter and called him Son of David. Sidon, on the Mediterranean coast north of Tyre, took its name from Zidon, Canaan’s eldest son and ancestor of the Sidonians and Phoenicians. It was the oldest Phoenician city and the mother city of Tyre; it lay in Asher’s allotment but was never subdued.Sources: the Bible text itself · Sidon · Tyre · Canaan
  • Jesus then went along the Sea of Galilee, sat on a mountain, and healed people laid at his feet, before feeding four thousand men, besides women and children, with seven loaves and a few small fish. Easton's Bible Dictionary (1897) notes that John calls the lake the Sea of Tiberias and places its surface 682 feet below the Mediterranean. The same dictionary says the boat crossing ended at Magadan, a name found only in this chapter and called Dalmanutha in Mark, on the west shore of the lake.Sources: the Bible text itself · Sea of Galilee · Magadan

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 1
  • Galilee · 32.760, 35.527 · verse 21
  • Sidon · Today: Sandikli archaeological site in Sidon · 33.561, 35.372 · verse 21
  • Tyre · 33.271, 35.196 · verse 21
  • Canaan · 32.767, 35.333 · verse 22
  • Sea of Galilee · 32.819, 35.590 · verse 29

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.