Matthew 17
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus da Yakubu, da Yahaya dan'uwansa, ya kai su kan wani dutse mai tsawo su kadai. 2Kamanninsa ya canja a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, kuma rigunansa suka yi kyalli fal. 3Sai ga Musa da Iliya sun bayyana garesu suna magana da shi. 4Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke a wurin nan. In kana so, zan yi bukkoki uku daya dominka, daya domin Musa, daya domin Iliya.” 5Sa'adda yake cikin magana, sai, girgije mai haske ya rufe su, sai murya daga girgijen, tana cewa, “Wannan kaunattacen Dana ne, shi ne wanda yake faranta mani zuciya. Ku saurare shi.” 6Da almajiran suka ji haka, suka fadi da fuskokinsu a kasa, saboda sun tsorata. 7Sai Yesu ya zo ya taba su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” 8Amma da suka daga kai ba su ga kowa ba sai Yesu kadai. 9Yayin da suke saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su, ya ce, “Kada ku fadawa kowa wannan wahayin, sai Dan Mutum ya tashi daga matattu.” 10Almajiransa suka tambaye shi, suka ce, “Don me marubuta ke cewa lallai ne Iliya ya fara zuwa?” 11Yesu ya amsa ya ce, “Hakika, Iliya zai zo ya maido da dukan abubuwa. 12Amma ina gaya maku, Iliya ya riga ya zo, amma ba su gane shi ba. A maimakon haka, suka yi masa abin da suka ga dama. Ta irin wanan hanya, Dan Mutum kuma zai sha wuya a hannunsu. 13Sa'annan almajiransa suka fahimci cewa yana yi masu magana a kan Yahaya mai Baftisma ne. 14Da suka iso wurin taron, wani mutum ya zo gunsa, ya durkusa a gaban sa, ya ce, 15“Ubangiji, ka ji tausayin yarona, domin yana da farfadiya, kuma yana shan wuya kwarai, domin sau da yawa yana fadawa cikin wuta ko ruwa. 16Na kawo shi wurin almajiran ka, amma ba su iya su warkar da shi ba.” 17Yesu ya amsa ya ce, “Marasa bangaskiya da karkataccen zamani, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan jure da ku? Ku kawo shi nan a wurina.” 18Yesu ya tsauta masa, sai aljanin ya fita daga cikinsa. Yaron ya warke nan take. 19Sai almajiran suka zo wurin Yesu a asirce suka ce, “Me ya sa muka kasa fitar da shi?” 20Yesu ya ce masu, “Saboda karancin bangaskiyarku. Domin hakika, ina gaya maku, in kuna da bangaskiya ko da kamar kwayar mastad, za ku ce wa wannan dutse, 'Matsa daga nan ka koma can,' zai kuwa matsa kuma ba abin da zai gagare ku. 21[Irin wannan aljanin bashi fita sai tare da addu'a da azumi]. 22Suna zaune a Galili, Yesu ya ce wa almajiransa, “Za a bada Dan Mutum ga hannun mutane. 23Kuma za su kashe shi, a rana ta uku zai tashi.” Sai almajiransa suka yi bakin ciki kwarai. 24Da suka iso Kafarnahum, mutane masu karbar haraji na rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku na ba da rabin shekel na haraji?” 25Sai ya ce, “I.” Amma da Bitrus ya shiga cikin gida, Yesu ya fara magana da shi yace, “Menene tunaninka Saminu? Sarakunan duniya, daga wurin wa suke karbar haraji ko kudin fito? Daga talakawansu ko daga wurin baki?” 26Sai Bitrus ya ce, “Daga wurin baki,” Yesu ya ce masa, “Wato an dauke wa talakawansu biya kenan. 27Amma don kada mu sa masu karbar harajin su yi zunubi, ka je teku, ka jefa kugiya, ka cire kifin da ya fara zuwa. Idan ka bude bakinsa, za ka sami shekel. Ka dauke shi ka ba masu karbar harajin nawa da naka.
Did you know?
The Transfiguration and the Return to Galilee
- Jesus took Peter, James, and John alone up a high mountain, where he was transfigured before them. Easton's Bible Dictionary identifies James as a son of Zebedee, an elder brother of the apostle John, and a fisherman in partnership with Peter, and notes that the three were present at the transfiguration. Peter, also called Simon, had been brought up by the Sea of Galilee and trained as a fisher.Sources: the Bible text itself · James (Son of Zebedee) · Simon Peter
- Moses and Elijah appeared and talked with Jesus. Easton's Bible Dictionary identifies Elijah as 'the Tishbite,' the 'Elias' of the New Testament, the figure the disciples asked about when they questioned the scribes' saying that Elijah must come first. The disciples understood Jesus' reply—that Elijah had already come and had not been recognized—to refer to John the Baptist, whose mission the dictionary connects with prophecy, including Malachi 3:1.Sources: the Bible text itself · Elijah · John the Baptist
- In Galilee, Jesus said the Son of Man was about to be delivered into the hands of men, killed, and raised to life on the third day. Easton's Bible Dictionary notes that the region was called 'Galilee of the Gentiles,' and that Capernaum—'Nahum's town'—became Jesus' 'own city' after his expulsion from Nazareth; there, collectors of the two-drachma tax asked Peter whether his teacher paid it.Sources: the Bible text itself · Galilee · Capernaum
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Galilee · 32.760, 35.527 · verse 22
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org