Nations Bible

Luke 17

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Sai Yesu ya ce wa almajiransa, 'Babu shakka akwai sanadodin tuntube da za su sa mu yin zunubi amma kaiton wanda shine sanadin su! 2Zai gwammaci a rataya masa dutsen nika a wuyansa, a jefar da shi a cikin teku fiye da wanda zai zama sanadiyar tuntube ga wadannan kananan. 3Ku kula da kanku. Idan dan'uwanka ya yi laifi, ka tsauta masa, in kuwa ya tuba ka yafe masa. 4Idan ya yi maka laifi sau bakwai a rana daya sa'annan ya juyo wurinka sau bakwai ya ce, 'Na tuba,' ya wajabta ka yafe masa!” 5Sai Manzannin suka ce wa Ubangiji, 'Ka kara mana bangaskiya.' 6Ubangiji kuwa ya ce, “In kuna da bangaskiya kamar kwayar mastad, za ku ce wa wannan durumin, 'Ka tuge, ka kuma dasu a cikin teku,' zai yi biyayya da ku. 7Amma wanene a cikinku, idan yana da bawa mai yin masa noma ko kiwon tumaki, da zarar ya dawo daga jeji, zai ce masa, 'Maza zo ka zauna ka ci abinci'? 8Ba zai ce masa, 'Ka shirya mani wani abu domin in ci ka kuma yi damara, ka yi mini hidima har in gama ci da sha. Bayan haka sai ka ci ka sha'? 9Ba zai yi wa bawan nan godiya ba domin ya yi biyayya da abubuwan da aka umarce shi ya yi, ko zai yi haka? 10Haka kuma, idan kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, 'Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da yake wajibi ne kurum.'” 11Wata rana yana tafiya zuwa Urushalima, sai ya bi iyakar kasar Samariya da Galili. 12Yayin da yana shiga wani kauye kenan, sai wadansu kutare maza guda goma suka tarye shi suna tsaye daga nesa da shi 13sai suka daga murya suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka yi mana jinkai.” 14Da ya gan su, ya ce masu, “Ku je ku nuna kanku a wurin firistoci.” Ya zama sa'adda suke tafiya, sai suka tsarkaka. 15Daya daga cikinsu da ya ga an warkar da shi, ya koma, yana ta daukaka Allah da murya mai karfi. 16Ya fadi a gaban Yesu, yana masa godiya. Shi kuwa Basamariye ne. 17Yesu ya amsa ya ce, “Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina sauran taran? 18Babu wani da ya dawo ya girmama Allah sai wannan bakon kadai?” 19Sai ya ce masa, “Tashi, kayi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.” 20Da Farisawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai bayyana, Yesu ya amsa masu ya ce, “Mulkin Allah ba lura ake yi da shi ba. 21Ba kuwa za a ce, 'Gashi nan!' Ko kuwa, 'Ga shi can ba!' domin mulkin Allah yana tsaknaninku.” 22Yesu ya ce wa almajiran, “Kwanaki na zuwa da za ku yi begen ganin rana daya cikin ranakun Dan Mutum, amma ba zaku gani ba. 23Za su ce maku, 'Duba can! 'Duba nan!' Amma kada ku je kuna dubawa, ko kuwa ku bi su. 24Kamar yadda walkiya take haskakawa daga wannan bangaren sararin sama zuwa wancan bangaren, haka ma dan mutum zai zama a ranar bayyanuwarsa. 25Amma lalle sai ya sha wahaloli dabam dabam tukuna, mutanen zamanin nan kuma su ki shi. 26Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka kuma zai faru a lokacin bayyanar Dan Mutum. 27Ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har zuwa ga ranar da Nuhu ya shiga jirgi - ruwan tufana kuma ya zo, ya hallaka su duka. 28Haka ma aka yi a zamanin Lutu, ana ci, ana sha, ana saye, ana sayarwa, ana shuke-shuke da gine-gine. 29Amma a ranar da Lutu, ya fita daga Saduma, aka zubo wuta da kibiritu daga sama, aka hallaka su duka. 30Haka kuma zai zama a ranar bayyanuwar Dan Mutum. 31A ranar nan fa, wanda yake kan soro kada ya sauka domin daukan kayansa daga cikin gida. Haka kuma wanda yake gona kada ya dawo. 32Ku tuna fa da matar Lutu. 33Duk mai son ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai same shi. 34Ina gaya maku, a wannan dare za a sami mutum biyu a gado daya. Za a dauka daya, a kuma bar dayan. 35Za a sami mata biyu suna nika tare. Za a dauka daya a bar daya.” 36[“Za a ga mutum biyu a gona. Za a dauki daya a bar daya.”] 37Sai suka tambaye shi, “Ina, Ubangiji?” Sai ya ce masu, “Duk in da gangar jiki yake, a nan ungulai sukan taru.”

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Ten lepers and the day of the Son of Man

  • Luke says that, on the way to Jerusalem, Jesus was passing between Samaria and Galilee when ten lepers met him as he entered a village. Easton's Bible Dictionary (1897) traces the name Samaria to Shomeron, a hill in the mountains of Israel that King Omri bought from Shemer and where he built his capital, and explains Galilee, meaning “circuit,” as a land long occupied by its original inhabitants and so called “Galilee of the Gentiles.” Of the ten who were healed, only a Samaritan returned, and Jesus called him a foreigner.Sources: the Bible text itself · Samaria · Galilee
  • Jesus says that the day of the Son of Man will be like the days of Noah, when people were eating and drinking, marrying and being given in marriage, until Noah entered the ark and the flood destroyed them all. Easton's Bible Dictionary (1897) explains the name Noah as “rest” and identifies him as the son of Lamech and the father of Shem, Ham, and Japheth.Sources: the Bible text itself · Noah
  • Jesus also recalls the days of Lot, when people were eating and drinking, buying and selling, planting and building, until the day Lot left Sodom and fire and sulfur rained down from heaven. Easton's Bible Dictionary (1897) explains the name Sodom as “burning” or “the walled” and places the city in the vale of Siddim, where it says fire from heaven destroyed it. In the same warning, Jesus tells anyone on a housetop or in a field not to turn back for possessions, and adds, “Remember Lot's wife!”Sources: the Bible text itself · Sodom

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Galilee · 32.760, 35.527 · verse 11
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 11
  • Samaria · Today: Samaria 2 · 32.276, 35.195 · verse 11

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.