Nations Bible

Luke 16

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Akwai wani mai arziki da yake da wakili, sai aka yi karan sa da cewa wannan wakili yana fallasar masa da dukiya. 2Sai mai arziki ya kira shi ya ce masa, 'Labarin me nake ji game da kai? Kawo lissafin wakilcin ka, don ba za ka sake zama wakili na ba.' 3Sai wakilin ya ce a ransa, 'Kaka zan yi, da yake maigida na zai karbe wakilci daga hannuna? Gashi, ba ni da karfin noma ina kuwa jin kunya in yi roko. 4Na san abin da zan yi domin idan an fitar da ni daga wakilcin, mutane su karbe ni a gidajensu. 5Sai wakilin ya kira kowanne daya da maigidansa ke bi bashi, yace wa na farkon, 'Nawa maigida na yake bin ka?' 6Ya ce, 'Garwan mai dari.' Sai ya ce masa, 'Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubuta hamsin.' 7Ya kuma ce wa wani, 'Nawa ake binka?' Ya ce, 'Buhu dari na alkama.' Ya ce masa, 'Ga tarkardarka, ka rubuta tamanin.' 8Sai maigida ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama 'ya'yan zamanin nan a ma'ammalar su da mutanen zamaninsu sun fi 'ya'yan haske wayo. 9Ina gaya maku ku yi abuta ta dukiya ta rashin gaskiya, saboda idan ya kare, su karbe ku a gidaje masu dauwama. 10Wanda yake da aminci a karamin abu, mai aminci ne a babban abu, wanda yake marar gaskiya a karamin abu, marar gaskiya ne a babban abu. 11Idan fa ba ku yi aminci da dukiya mara adalci ba, wa zai amince maku da dukiya ta gaskiya? 12Idan kuma ba ku yi aminci da kudin wani ba, wa zai ba ku kudin da ke naku? 13Ba bawan da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ki daya, ya so daya ko kuwa ya amince wa dayan, ya raina dayan. Ba za ku iya bauta wa Allah ku kuma bauta wa dukiya ba.” 14Da Farisawa da ke da kaunar kudi suka ji dukan wadannan abubuwa, suka yi masa ba'a. 15Sai ya ce masu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abin da mutane suke girmamawa kwarai abin kyama ne a gun Allah. 16Attaura da litattafan annabawa suna nan har zuwan Yahaya. Tun daga lokacin nan ake yin bisharar mulkin Allah, kowa kuma yana kokarin kutsawa zuwa cikinta. 17Duk da haka, zai fi sauki sama da kasa su shude, da ko digo daya na attaura ya shude. 18Duk wanda ya saki matansa ya auri wata ya aikata zina, kuma wanda ma ya auri sakakkiya ya aikata zina. 19Akwai wani mai arziki, mai sa tufafi na alfarma masu tsada yana shagalin sa kowace rana. 20Aka ajiye wani gajiyayye a kofarsa, mai suna liazaru wanda duk jikinsa miki ne, 21Shi kuwa yana marmarin ya koshi da barbashin da ke fadowa daga teburin mai arzikin nan har ma karnuka sukan zo suna lasar mikinsa. 22Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, malaiku kuma suka dauke shi suka kai shi wurin Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi, 23yana cikin hades yana shan azaba, sai ya daga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a kirjinsa. 24Sai ya yi kira ya ce, 'Baba Ibrahim, ka ji tausayi na, ka aiko Li'azaru ya tsoma dan yatsansa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.' 25Amma Ibrahim ya ce, 'Yaro, ka tuna fa a zamanka na duniya ka sha duniyarka, ka kuma karba abubuwa masu kyau, amma Li'azaru kuma sai wahala. Amma yanzu dadi ake bashi a nan, kai kuwa kana shan azaba. 26Banda haka ma, akwai rami mai zurfi, domin wadanda suke son ketarewa zuwa wurinku kada su iya, kada kuma kowa ya ketaro zuwa wurinmu daga can.' 27Sai mai arziki ya ce, 'To ina rokonka, Baba Ibrahim, ka aike shi zuwa gidan mahaifina - 28domin ina da 'yan'uwa maza biyar, ya je ya yi masu gargadi kada su ma su zo wurin azaban nan.' 29Amma Ibrahim ya ce, 'Suna da Musa da annabawa; bari su saurare su.' 30Sai mai arziki ya amsa, 'A'a, Baba Ibrahim, idan wani daga cikin matattu ya je wurinsu, zasu tuba.' 31Amma Ibrahim ya ce masa, 'In dai har basu saurari Musa da na annabawa ba, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su rinjayu ba.'”

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Wealth, two masters, and Lazarus

  • In Jesus' words about the rich man and Lazarus, the rich man cries out, 'Father Abraham,' and Abraham answers, 'Child.' Easton's Bible Dictionary (1897) explains the name Abraham as 'Father of a multitude' and describes him as the heir of the promises.Sources: the Bible text itself · Abraham
  • Speaking to Pharisees who were scoffing at him, Jesus says that the Law and the Prophets were proclaimed until John, and that since then the gospel of the kingdom of God is being preached. Easton's Bible Dictionary (1897) calls John the Baptist the 'forerunner of our Lord,' says that his mission was the subject of prophecy, including Isaiah 40:3 and Malachi 3:1, and states that his birth took place six months before that of Jesus.Sources: the Bible text itself · John the Baptist
  • A manager accused of wasting his master's possessions is told to turn in an account and give up his position. He has the debtors rewrite their bills, reducing a hundred measures of olive oil to fifty and a hundred measures of wheat to eighty, and the master commends the dishonest manager because he had acted shrewdly. Jesus then says that no servant can serve two masters, and that no one can serve both God and money.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.