Luke 18
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a kada kuma su karaya, 2yace, “A wani gari an yi wani alkali mara tsoron Allah, kuma baya ganin darajan mutane. 3Akwai wata mace gwauruwa a wannan garin, wadda ta rika zuwa wurinsa, tana ce masa, 'Ka taimake ni yanda zan sami adalci a kan abokin gaba na.' 4An dade bai so ya taimaka mata, amma daga baya sai ya ce a ransa, 'ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma darajanta mutane, 5duk da haka saboda gwauruwar nan ta dame ni, zan taimake ta domin ta sami adalci, yadda ba za ta gajiyar da ni da zuwanta wurina ba.'” 6Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alkalin nan marar gaskiya ya fada. 7A yanzu Allah ba zai biya wa zababbunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne? 8Ina gaya maku, zai biya masu hakkin su da wuri. Amma sa'adda Dan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya?” 9Ya sake ba da misalin nan ga wadansu masu amincewa da kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, 10“Wadansu mutane biyu suka shiga haikali domin yin addu'a - daya Bafarise, dayan kuma mai karbar haraji ne. 11Sai Bafarisen ya mike, ya yi addu'a a kan wadannan abubuwa game da kansa, 'Allah, na gode maka, da cewa ni ba kamar sauran mutane dake mazambata ba, ko marasa adalci, ko mazinata, ko kamar wannan mai karbar harajin. 12Duk mako ina azumi sau biyu. Nakan bayar da zakkar dukan abin da na samu.' 13Amma mai karbar harajin kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya daga kai sama ba, sai dai yana bugun kirjin sa, yana cewa, 'Allah, ka yi mini jinkai, ni mai zunubi.' 14Ina gaya maku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar dayan ba, domin dukan wanda ya daukaka kansa, za a kaskantar da shi, amma duk wanda kaskantar da kansa kuwa daukaka shi za a yi.” 15Sai mutanen suka kawo masa jariransu, domin ya taba su, da almajiransa suka ga haka, sai suka kwabe su. 16Amma Yesu ya kira su wurinsa, ya ce, “Ku bar yara kanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai mulkin Allah na irin su ne. 17Gaskiya ina gaya maku, duk wanda bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, lallai ba zai shige shi ba.” 18Wani shugaban jama'a ya tambaye shi ya ce “Malam managarci, me zan yi in gaji rai Madawwami?” 19Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Babu wani managarci sai Allah kadai. 20Ka dai san dokokin - kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar karya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.” 21Sai shugaban ya ce, “Dukan wadannan abubuwa na kiyaye su tun a kuruciya ta.” 22Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Abu daya ne kadai ya rage maka. Dole ne ka sayar da dukan mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka kuma sami wadata a sama - sa'annan ka zo ka biyoni.” 23Amma da mai arzikin ya ji wadannan abubuwa, sai yayi bakin ciki kwarai, don shi mai arziki ne sosai. 24Yesu kuwa, da ya ga ransa ya baci, sai ya ce, “Yana da wuya masu dukiya su shiga mulkin Allah! 25Zai zama da sauki rakumi ya shiga kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.” 26Wadanda suka ji wannan magana suka ce, “Idan hakane wa zai sami ceto kenan?” 27Yesu ya amsa, “Abin da ya fi karfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.” 28Sai Bitrus ya ce, “To, ga shi mun bar mallakarmu, mun bi ka.” 29Yesu ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko 'yan'uwansa, ko iyayensa, ko kuma 'ya'yansa, saboda mulkin Allah, 30sa'annan ya kasa samun ninkin ba ninkin a duniyan nan, da rai na har abada a duniya mai zuwa.” 31Bayan da ya tara su goma sha biyun nan, ya ce masu, “Ga shi, muna tafiya zuwa Urushalima, duk abubuwan da aka rubuta game da Dan Mutum ta hannun annabawa zasu tabbata. 32Gama za a bashe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa miyau. 33Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma zai tashi.” 34Amma ba su fahimci ko daya daga cikin wadannan abubuwa ba, domin zancen nan a boye yake daga garesu, ba su ma gane abin da aka fada ba. 35Da ya kusato Yariko, ga wani makaho zaune a gefen hanya, yana bara, 36da ya ji taro na wucewa, sai ya tambaya ko menene. 37Suka ce masa Yesu Banazarat ne yake wucewa. 38Sai makahon ya ta da murya mai karfi, ya ce, “Yesu, Dan Dauda, ka yi mani jinkai.” 39Sai wadanda suke gaba suka kwabe shi, suna gaya masa ya yi shiru. Amma ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, “Dan Dauda, ka yi mani jinkai.” 40Sai Yesu ya tsaya, ya umarta a kawo shi wurinsa. Da makahon ya zo kusa, sai Yesu ya tambaye shi, 41“Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ubangiji, ina so in samu gani.” 42Yesu ya ce masa, “Karbi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai.” 43Nan take ya samu gani, ya bi Yesu, yana daukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.

Did you know?
Prayer, Humility, and Mercy on the Way
- As Jesus draws near Jericho, a blind man sits begging beside the road. Easton's Bible Dictionary (1897) calls Jericho a “place of fragrance”: a fenced city amid a vast grove of palm trees on the plain of the Jordan, about five miles west of the river, and the most important city of that valley.Sources: the Bible text itself · Jericho
- The crowd tells the blind man that Jesus of Nazareth is passing by, and he cries out, “Son of David, have mercy on me.” David, whose name is explained as “beloved,” was the eighth and youngest son of Jesse and a citizen of Bethlehem; Nazareth, which is not mentioned in the Old Testament, was the home of Joseph and Mary.Sources: the Bible text itself · David · Nazareth
- Jesus takes the Twelve aside and tells them they are going up to Jerusalem, where everything the prophets wrote about the Son of Man will be fulfilled. The name is in a dual form meaning “possession of peace” or “foundation of peace,” probably referring to the mountains Zion and Moriah on which the city was built, though some connect it with the upper and lower city; Jerusalem is also called the holy city and described as a mountain city.Sources: the Bible text itself · Jerusalem
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 31
- Jericho · Today: Tell el Alayiq · 31.852, 35.436 · verse 35
- Nazareth · 32.702, 35.298 · verse 37
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org