Nations Bible

John 6

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Bayan waddannan abubuwa, Yesu ya ketare tekun Galili, wanda a ke kira tekun Tibariya. 2Sai taro mai yawa suka bi shi domin suna ganin alamu da yake yi akan marasa lafiya. 3Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa. 4(Kuma da idin Ketarewa, wato idin Yahudawa, ya kusato.) 5Da Yesu ya daga kai sai ya ga babban taro yana zuwa wurinsa, sai ya ce ma Filibus, “Ina za mu sayi gurasar da Mutanen nan za su ci?” 6( Ya fadi haka ne domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi.) 7Filibus ya amsa masa, “gurasar dinari biyu ma ba zata ishi kowannensu ya samu ko kadan ba.” 8Daya daga cikin almajiransa, wato Andarawus, dan'uwan Siman Bitrus, ya ce masa, 9“Ga wani dan yaro nan da dunkule biyar na sha'ir, da kifi biyu. Amma menene wadannan za su yi wa mutane masu yawa?” 10Yesu ya ce, “ku sa mutane su zauna.”( wurin kuwa akwai ciyawa.) Sai mazajen suka zauna, sun kai wajen dubu biyar. 11Sai Yesu ya dauki gurasar, bayan da ya yi godiya, sai ya rarraba wa wadanda suke zaune. Haka kuma ya rarraba kifin gwargwadon abin da zai ishe su. 12Da Mutanen suka ci suka kuma koshi, sai ya ce wa almajiransa, ku tattara gutsattsarin da suka rage, kada ya zama asara.” 13Sai suka cika kwanduna goma sha biyu da gutsattsarin gurasar nan biyar da ya rage bayan da kowa ya ci. 14Da jama'a suka ga alamar da ya yi, sai suka ce, “ Hakika wannan shi ne annabin nan mai zuwa cikin duniya. 15“Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su dauke shi da karfi da yaji su nada shi sarki, sai ya sake komawa kan dutsen da kansa. 16Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara teku. 17Suka shiga cikin jirgi, suka haye teku zuwa kafarnahum. (A lokacin duhu ya yi, Yesu kuwa bai riga ya iso wurinsu ba tukuna.) 18Iska mai karfin gaske tana kadawa, kuma tekun yana hargowa. 19Bayan da almajiran suka yi tuki na wajen kimanin mil ashirin da biyar ko talatin, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan teku ya kuma kusa da jirgin, sai suka firgita. 20Amma ya ce masu, “Ni ne! kada ku firgita.” 21Sa'an nan suka yarda suka karbe shi a cikin jirgin, kuma nan da nan jirgin ya kai gacci. 22Kashe gari, sauran taron da suke tsaye a dayan hayin tekun suka ga cewa babu wani jirgi a wajen sai dayan, Yesu kuma bai shiga ciki da almajiransa ba, amma almajiransa suka tafi su kadai. 23Sai dai, akwai wadansu jirage da suka zo daga Tibariya kusa da wurin da taron suka ci gurasa bayan da Ubangiji ya yi godiya. 24Sa'anda taron suka gane cewa Yesu da almajiransa ba su wurin, su da kansu su ka shiga cikin jiragen suka tafi Kafarnahum neman Yesu. 25Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Mallam, yaushe ka zo nan?” 26Yesu ya amsa masu, da cewa, “ hakika, kuna nema na ne, ba don kun ga alamu ba, amma domin kun ci gurasar nan kun koshi. 27Ku daina yin wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama wanda zai kaiku ga rai madawwami wanda Dan Mutum zai ba ku, domin Ubangiji Allah ya sa hatiminsa a kansa.” 28Sai suka ce Masa, “Me za mu yi, domin mu aikata ayyukan Allah? 29Yesu ya amsa, “Wannan shi ne aikin Allah: wato ku gaskata da wanda ya aiko.” 30Sai suka ce masa, “To wace alama za ka yi, don mu gani mu gaskata ka? 31Me za ka yi? Kakanninmu sun ci manna a jeji, kamar yadda aka rubuta, “Ya ba su gurasa daga sama su ci.” 32Sa'an nan Yesu ya ce masu, “hakika, hakika, ina gaya maku ba Musa ne ya ba ku gurasa nan daga sama ba, amma Ubana ne ya baku gurasa ta gaskiya daga sama. 33Gurasar Allah itace mai saukowa daga sama mai kuma bada rai ga duniya,” 34Sai suka ce masa, “Mallam, ka rika ba mu irin wannan gurasa kodayaushe.” 35Yesu ya ce masu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo wurina ba zai ji yunwa ba, wanda kuma ya gaskanta da ni ba zai kara jin kishi ba. 36Amma na gaya maku cewa, hakika kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba. 37Duk wanda Uba ya bani zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kadan. 38Gama na sauko daga sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 39Wannan shi ne nufin wanda ya aiko ni, kada in rasa ko daya daga cikin wadannan da ya bani, sai dai in tashe su a ranar karshe. 40Gama wannan shi ne nufin Ubana, duk wanda yake ganin Dan ya kuma gaskata da shi zai sami rai madawwami, ni kuma zan tashe shi a ranar karshe. 41Sai Yahudawa suka yi gunaguni akansa, domin ya ce, “Nine Gurasar da ta sauko daga sama.” 42Suka ce, “Ba wannan ne Yesu Dan Yusufu, wanda Ubansa da Uwarsa mun san su ba? Ta yaya yanzu zai ce, 'Na ya sauko daga sama'? 43Yesu ya amsa, ya ce masu, “Kada ku yi gunaguni a junanku. 44Ba mai iya zuwa wurina sai dai in Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta karshe. 45A rubuce yake cikin litattafan anabawa cewa, 'Dukkansu Allah zai koya masu'. Duk wanda ya ji ya kuma koya daga wurin Uba, ya kan zo gare ni. 46Ba cewa wani ya taba ganin Uban ba, sai shi wanda yake daga wurin Allah - shine ya ga Uban. 47Hakika, hakika, wanda ya bada gaskiya, yana da rai Madawwami. 48Ni ne Gurasa ta rai. 49Ubanninku sun ci manna cikin jeji, suka kuma mutu. 50Ga gurasa da ta sauko daga sama, domin mutum ya ci daga cikinta ba kuwa zai mutu ba. 51Ni ne gurasa mai rai da ya sauko daga sama. Duk wanda ya ci daga gurasar, zai rayu har abada. Wannan gurasar da zan bayar jiki na ne don ceton duniya.” 52Sai Yahudawa suka fusata a tsakanin junansu suka kuma fara gardama, cewa, “Yaya mutumin nan zai iya bamu naman jikinsa mu ci? 53Sai Yesu ya ce masu, “ hakika, hakika, in ba ku ci naman jikin Dan mutum ba, ba ku kuma sha jininsa ba, ba za ku sami rai a cikin ku ba. 54Dukan wanda ya ci nama na ya kuma sha jinina yana da rai Madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar karshe. 55Domin namana abinci ne na gaske, jinina kuma abin sha ne na gaskiya. 56Duk wanda ya ci namana, ya kuma sha jinina yana zamne a ciki na, ni kuma a cikinsa. 57Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda ya ci namana, zai rayu sabo da ni. 58Wannan itace gurasar da ta sauko daga sama, ba irin wadda Ubanninku suka ci suka mutu ba. Dukan wanda ya ci gurasar zai rayu har abada.” 59Yesu ya fadi wadan nan abubuwa a cikin majami'a sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum. 60Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan Magana yana da karfi, wa zai iya jinta?” 61Yesu, kuwa da yake ya sani a ransa da cewa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce masu, “Wannan ya zamar maku laifi? 62Yaya Ke nan in kun ga Dan Mutum yana hawa inda yake a da? 63Ruhu shine mai bayar da rai; Jiki ba ya amfana komai. Kalmomin da na fada maku ruhu ne, da kuma rai. 64Amma fa akwai wadansun ku da ba su ba da gaskiya ba. Domin tun farko Yesu ya san wadanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bashe shi. 65Ya fada cewa, “shiyasa na gaya maku, ba mai iya zuwa wurina, sai ta wurin Uban.” 66Bayan haka, da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su kara tafiya tare da shi ba. 67Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, “ku ba kwa so ku tafi, ko ba haka ba? 68Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? kai kake da maganar rai madawwami. 69Mu kwa mun gaskata mun kuma sani kai ne mai tsarkin nan na Allah.” 70Yesu ya ce masu, “Ba ni na zabe ku, goma sha biyu ba, amma dayanku Iblis ne?” 71Wato yana magana akan Yahuda dan Siman Iskariyoti, shi kuwa daya daga cikin sha-biyun ne, wanda zai ba da Yesu.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

The Bread of Life

  • In this chapter John calls the lake both the Sea of Galilee and the Sea of Tiberias. Easton's Bible Dictionary describes it as twelve and a half miles long and from four to seven and a half miles wide, with its surface 682 feet below the Mediterranean. Tiberias, on the western shore, is said to have been founded by Herod Antipas in A.D. 16 and named for the emperor Tiberius; some boats from that city landed near the place where the people had eaten the bread.Sources: the Bible text itself · Sea of Galilee · Tiberias
  • That evening the disciples set out by boat for Capernaum, and the next day the crowd crossed and found Jesus there. He delivered the teaching about the bread of life in the synagogue at Capernaum. Easton's Bible Dictionary notes that the city, not mentioned in the Old Testament, became Jesus' own city after his expulsion from Nazareth and was the scene of many episodes in his ministry.Sources: the Bible text itself · Capernaum
  • As the crowd drew near, Jesus asked Philip where they could buy bread, a question the narrative says was meant to test him, for Jesus already knew what he would do. Philip, like Andrew and Peter, was from Bethsaida; he answered that two hundred denarii would not buy enough for each person to have a small piece. Andrew, Peter's brother, then pointed out a boy with five barley loaves and two small fish, and Easton's Bible Dictionary, citing this exchange among other passages, says Philip seems to have held a prominent place among the apostles.Sources: the Bible text itself · Phillip the Apostle · Andrew · Simon Peter

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Sea of Galilee · 32.819, 35.590 · verse 1
  • Tiberias · 32.774, 35.544 · verse 23

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.