Nations Bible

John 5

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Bayan haka akwai idi na yahudawa, kuma Yesu ya tafi Urashalima. 2To a cikin Urashilima kusa da kofar tumaki akwai tabki, wanda ake kira Baitasda da harshen Ibraniyanci, yana da shirayi biyar. 3Taron mutane dayawa masu ciwo da, makafi da guragu da shanyayyu suna kwance a wurin [suna jira a dama ruwan]. 4Gama mala'ikan Ubangiji kan sabko a cikin tabkin ya dama ruwan, wanda ya fara taba ruwan sai ya warke komai cutar da yake da ita. 5Akwai wani mutum a bakin tabki yana kwance yana da rashin lafiya har shekara talatin da takwas. 6Da Yesu ya gan shi yana kwance a wurin sai ya gane ya dade a wurin, sai ya ce masa, “ Ko kana so ka warke?” 7Sai mai rashin lafiyar ya amsa ya ce, “Malam, bani da kowa da zai sa ni a cikin tabkin idan ruwan ya motsa. Yayinda na ke kokari sai wani ya riga ni.” 8Yesu ya ce masa,” Ka tashi ka dauki shimfidarka ka tafi.” 9Nan dan nan Mutumin ya warke, ya dauki shimfidarsa ya tafi. Ranar kuwa Asabar ce. 10Sai Yahudawa suka ce da wanda aka warkar din, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka dauki shimfidarka ba.” 11Sai ya amsa ya ce, “Ai wanda ya warkar da ni, shine ya ce mani 'Dauki shimfidarka, ka tafi.” 12Suka tambaye shi, “wane mutum ne ya ce maka, 'Dauki shimfidar ka yi tafiya'?” 13Sai dai, shi wanda aka warka din, ba san ko wanene ya warkar da shi ba, domin Yesu ya riga ya tafi aboye, saboda akwai taro a wurin. 14Bayan haka, Yesu ya same shi a Haikalin, ya ce masa, “ka ga fa, ka warke. To, kada ka kara yin zunubi don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.” 15Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahuduwa cewa Yesu ne ya warkar da shi. 16To saboda haka Yahudawa suka fara tsanantawa Yesu, don ya yi wadannan abubuwa ran Asabar. 17Yesu kuwa ya amsa masu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki.” 18Saboda haka, Yahudawa suka kara nema su kashe shi ba don ya keta Asabar kadai ba, amma kuma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato yana maida kansa dai-dai da Allah. 19Yesu ya amsa masu ya ce, hakika hakika, ina gaya maku, Dan ba ya yin kome shi kadai, sai abin da ya ga Uba yana yi. 20Domin Uban na kaunar Dan, yana kuma nuna masa dukan abinda shi da kansa yake yi, kuma zai nuna masa abubuwan da suka fi wadannan, domin ku yi mamaki. 21Gama kamar yadda Uba yakan tada matattu ya kuma basu rai, haka Dan ma yake bada rai ga duk wanda ya nufa. 22Gama Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya damka dukan hukunci ga Dan, 23domin kowa ya girmama Dan, kamar yadda suke girmama Uban. Shi wanda ba ya girmama Dan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi. 24Hakika, hakika, duk mai jin Maganata, yana kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami ba kuma za a kashe shi ba, domin ya ratse daga mutuwa zuwa rai. 25Hakika hakika, ina gaya maku, lokaci na zuwa, har ma ya yi da matattatu za su ji muryar Dan Allah, wadanda suka ji kuwa za su rayu. 26Kammar yada Uba ya ke da rai a cikinsa, haka ya ba Dan don ya zama da rai cikin kansa. 27Uban ya kuma ba Dan ikon zartar da hukunci, saboda shi ne Dan Mutum. 28Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk wadanda suke kaburbura za su ji muryarsa, 29su kuma fito: wadanda suka aikata nagarta zawa tashi na rai, wadanda suka aikata mugunta kuwa zuwa tashi na hukunci. 30Ba na iya yin kome ni da kai na. Yadda na ke ji, haka nake yin hukunci, Hukunci na kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 31Idan zan yi shaida game da kaina, shaidata baza ta zama gaskiya ba. 32Akwai wani wanda ya ke bada shaida game da ni, na kuwa sani shaidar da yake bayarwa game da ni gaskiya ce. 33Kun aika zuwa wurin Yahaya, shi kuma ya yi shaidar gaskiya. 34Duk da haka shaidar da na karba bata mutum bace. Na fadi wadanan abubuwa domin ku sami ceto. 35Yahaya fitila ne mai ci, mai haske ne kuma, kun yarda ku yi farinciki da haskensa dan lokaci kadan. 36Amma shaidar da ni ke da ita ta fi ta Yahaya karfi. Domin ayyukan da Uba ya bani ni in yi, wato ainihin ayyukan da nake yi, su ne suke shaida ta cewa, Uba ne ya aiko ni. 37Uba wanda ya aiko ni, shi da kansa ya shaide ni. Ba ku taba jin muryar sa ba, ko ganin kamanninsa. 38Maganarsa kuwa ba ta zaune a zuciyarku, domin baku gaskata da wanda ya aiko ni ba. 39Kuna nazarin littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai Madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata. 40kuma baku niyyar zuwa wurina domin ku sami rai. 41Ba na karbar yabo daga wurin mutane, 42amma na sani baku da kaunar Allah a zuciyarku. 43Na zo a cikin sunan Ubana, amma ba ku karbe ni ba. Idan wani ya zo da sunan kansa, za ku karbe shi. 44Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karban yabo daga junanku, amma ba ku neman yabon dake zuwa daga wurin Allah? 45Kada ku yi tunani zan zarge ku a wurin Uba. Mai zargin ku shine Musa, wanda kuka sa begenku a cikin sa. 46Inda kun gaskata Musa, da kun gaskata da ni domin ya yi rubutu game da ni. 47Idan kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?”

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

A Sabbath healing at Bethesda

  • Near the Sheep Gate, in the eastern wall of Jerusalem, there was a pool with five covered colonnades, called Bethesda in Hebrew, a name meaning 'house of mercy.' The Greek word for the pool means a swimming bath or reservoir, and a great number of the sick, the blind, the lame, and the paralyzed lay under its colonnades, waiting for the water to be stirred. It is also called Bethsaida and Beth-zatha; the historian Eusebius, writing in A.D. 330, calls it the sheep-pool, and Easton's Bible Dictionary (1897) identifies it with the so-called Fountain of the Virgin in the Kidron valley, near the Pool of Siloam.Sources: Bethesda · Sheep Gate · the Bible text itself
  • A chronology of the event places the healing at Bethesda in A.D. 28, and the Gospel says it took place on the Sabbath. Those whom the account calls the Jews told the healed man that it was unlawful to carry his mat that day. When Jesus answered that his Father was still working and that he himself was working, they sought all the more to kill him, because they heard him calling God his own Father and making himself equal with God.Sources: Bethesda pool healing · the Bible text itself
  • In the discourse that follows, Jesus appeals to the testimony of John the Baptist, whom Easton's Bible Dictionary (1897) calls the forerunner of the Lord and whose mission, the dictionary says, was the subject of prophecy. Jesus describes him as a lamp that burned and gave light, in which the people were willing for a time to rejoice, though he says he has a greater testimony than John's: the works the Father has given him to do.Sources: John the Baptist · the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 1, 2
  • Bethesda · Today: Pool of Bethesda · 31.781, 35.236 · verse 2
  • Sheep Gate · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 2

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.