John 7
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Bayan wadannan abubuwa Yesu ya zagaya cikin Gallili, saboda baya so ya shiga cikin Yahudiya domin Yahudawa suna shirin su kashe shi. 2To Idin Bukkoki na Yahudawa ya kusa. 3Sai 'yan'uwansa suka ce da shi, “ka tashi ka tafi Yahudiya, domin almajiranka su ga ayyukan da kake yi su ma. 4Ba wanda ya ke yin wani abu a boye idan dai yana so kowa da kowa ya san shi. Da yake ka na yin wadannan abubuwa sai ka nuna kan ka a fili ga duniya. 5Domin ko 'yan'uwansa ma basu bada gaskiya gare shi ba. 6Yesu ya ce dasu, “lokaci na bai yi ba tukuna, amma ku koyaushe lokacin ku ne. 7Duniya baza ta iya kin ku ba, amma ta ki ni saboda ina fadin cewa ayyukanta ba su da kyau. 8Ku ku je wurin idin, ni ba zan je wurin idin ba domin lokacina bai yi ba tukuna. 9Bayan da ya gaya masu wadannan abubuwa, ya tsaya a cikin Gallili. 10Amma bayan da 'yan'uwansa su ka tafi wurin idin shi ma ya tafi, amma a asirce ba a fili ba. 11Saboda Yahudawa suna neman sa a wurin idin, su na cewa “Ina yake?” 12Akwai maganganu dayawa a kansa cikin taron. Wadansu suna cewa, “shi mutumin kirki ne.” Wadansu kuma suna cewa,”A'a yana karkatar da hankalin jama'a.” 13Amma duk da haka ba wanda ya yi magana a fili a kansa saboda suna jin tsoron Yahudawa. 14Sa'anda aka kai rabin idin, sai Yesu ya shiga cikin haikali ya fara koyarwa. 15Yahudawa suna mamaki suna cewa,”Yaya aka yi wannan mutum ya sami ilimi dayawa haka? Shi kuwa bai je makaranta ba.” 16Yesu ya ba su amsa ya ce,”Koyarwata ba tawa ba ce, amma ta wanda ya aiko ni ce.” 17Idan wani yana so ya yi nufinsa, za ya gane koyarwannan ko daga wurin Allah ta zo, ko ko tawa ce ta kaina. 18Ko wanene yake maganar kansa, yana neman darajar kansa kenan, amma ko wanene ya nemi darajar wanda ya aiko ni, wannan mutum mai gaskiya ne, babu rashin adalci a cikin sa. 19Ba Musa ya baku dokoki ba? Amma duk da haka ba mai aikata dokokin. Me yasa ku ke so ku kashe ni? 20Taron suka ba shi amsa, “Ka na da aljani. Wanene yake so ya kashe ka?” 21Yesu ya amsa ya ce masu, “Nayi aiki daya, dukan ku kuna mamaki da shi. 22Musa ya baku kaciya, {ba kuwa daga Musa take ba, amma daga kakannin kakanni ta ke}, kuma a ranar Asabar kukan yi wa mutum kaciya. 23Idan mutum ya karbi kaciya ranar Asabar, domin kada a karya dokar Musa, don me kuka ji haushi na saboda na mai da mutum lafiyayye sarai ranar Asabar? 24Kada ku yi shari'a ta ganin ido, amma ku yi shari'a mai adalci.” 25Wadansun su daga Urushalima suka ce, “wannan ba shine wannan da suke nema su kashe ba?” 26Kuma duba, yana magana a fili, sannan ba wanda ya ce da shi komai. Ba zai yiwu ba mahukunta su sani cewa wannan Kristi ne, ko ba haka ba? 27da haka, mun san inda wannan mutum ya fito. Amma sa'anda Kristi za ya zo, ba wanda zai san inda ya fito.” 28Yesu yayi magana da karfi a haikali, yana koyarwa ya na cewa, “Kun san ni kuma kun san inda na fito. Ban zo domin kaina ba, amma wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, ku kuwa baku san shi ba. 29Ni na san shi domin daga wurinsa na fito, kuma shine ya aiko ni.” 30Suna kokari su kama shi, amma ba wanda ya iya sa masa hannu domin sa'arsa ba ta yi ba tukuna. 31Duk da haka wadansu dayawa a cikin taron suka bada gaskiya gare shi suka ce,”Sa'anda Kristi ya zo, zai yi alamu fiye da wadanda wannan mutum ya yi?” 32Farisawa suka ji tattarmukan suna yin rada a kan wadannan abubuwa game da Yesu, Sai manyan malamai da Farisawa su ka aika jami'ai su kama shi. 33Sa'annan Yesu yace ma su,” jimawa kadan ina tare ku, sa'annan in tafi wurin wanda ya aiko ni. 34Za ku neme ni ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba.” 35Yahudawa fa su ka cewa junan su, “Ina wannan mutum zai je inda ba za mu iya samun sa ba? Ko za ya tafi wurin Helinawa na warwatsuwa ya koyawa Helinawa? 36Wace kalma ya ke fadi haka, 'za ku neme ni amma ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba'?” 37To a rana ta karshe, babbar rana ta idin, Yesu ya mike ya yi magana da karfi cewa, “Idan kowa yana jin kishi, ya zo wuri na ya sha. 38Shi wanda ya bada gaskiya gare ni kamar yadda nassi ya fadi, daga cikin sa rafukan ruwa na rai za su bulbulo.” 39Amma ya fadi haka a kan Ruhu, wanda wadanda suka bada gaskiya gare shi za su karba; ba a ba da Ruhun ba tukuna, saboda ba a rigaya an daukaka Yesu ba. 40Wadansu a cikin taron, sa'anda suka ji wadannan kalmomi, suka ce, “Wannan lallai annabi ne.” 41Wadansu suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma wadansu suka ce, “Almasihu zai fito daga Gallili ne.? 42Ba nassi ya ce Almasihu zai fito daga cikin dangin Dauda daga Baitalami ba, daga kauyen da Dauda ya fito?” 43Sai aka sami rabuwa a cikin taron saboda shi. 44Da wadansun su sun kama shi, amma ba wanda ya sa masa hannu. 45Sa'annan jami'an suka dawo wurin manyan Fristoci da Farisawa, wadanda suka ce,” me yasa ba ku kawo shi ba?” 46Jami'an su ka amsa, “Ba mutumin da ya taba yin magana kamar haka.” 47Farisawa suka amsa masu, “kuma an karkatar da ku? 48Ko wani daga cikin mahukunta ya bada gaskiya gare shi, ko kuwa daga cikin Farisawa? 49Amma wannan taro da basu san shari'a ba, la'anannu ne.” 50Nikodimus ya ce masu, (shi wanda ya zo wurin Yesu da, daya daga cikin Farisawa), 51“ Ko shari'armu bata hana hukunta mutum ba, sai ta ji daga gare shi ta kuma san abin da ya aikata ba?” 52Suka amsa masa suka ce,”kai ma daga Galili ka fito? Ka yi bincike ka gani ba annanbin da zai fito daga Galili.” 53Daga nan sai kowa ya tafi gidansa.

Did you know?
Jesus at the Feast of Tabernacles
- As the Jewish Feast of Tabernacles, a seven-day feast, drew near, Jesus stayed in Galilee and avoided Judea, where people were trying to kill him. In his time Judea was the southernmost of the three Roman divisions of Palestine, distinct from Galilee and Samaria; he later went up to the feast in secret and taught in the temple courts.Sources: the Bible text itself · Feast of Tabernacles · Judea
- The crowds were divided over where the Christ would come from. Some said that Scripture places him in David's line and in Bethlehem, the village where David, the eighth and youngest son of Jesse, lived; others objected that he could not come from Galilee, a region long called Galilee of the Gentiles, and the Pharisees insisted that no prophet comes from there.Sources: the Bible text itself · David · Galilee
- Nicodemus, a Pharisee and a member of the Sanhedrin, had earlier come to Jesus at night. When the officers sent to arrest Jesus returned without him, Nicodemus protested and asked whether their law condemned a man before hearing him and finding out what he had done.Sources: the Bible text itself · Nicodemus
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Galilee · 32.760, 35.527 · verses 1, 3, 9, 41, 52
- Judea · Today: Judea 1 · 31.777, 35.234 · verses 1, 3
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 25
- Bethlehem · 31.704, 35.208 · verse 42
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org