1 Timothy 5
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Kada ka tsauta wa dattijo. Sai dai ka gargade shi kamar mahaifi. Ka gargadi samari kamar 'yan'uwa. 2Gargadi dattawa mata kamar iyaye mata, 'yan mata kamar 'yan'uwa mata cikin dukkan tsarki. 3Ka girmama gwamraye, gwamraye na gaske. 4Amma gwamruwar da take da 'ya'ya ko jikoki, bari su fara nuna bangirma cikin danginsu. Bari su sakawa iya-yensu, domin Allah yana jin dadin haka. 5Amma gwamruwa ta gaske da ke ita kadai, ta kafa begenta ga Allah. Kullum tana tsananta yin roke-roke da addu'o'i dare da rana. 6Amma, mace mai son zaman annashuwa ta riga ta mutu, ko da shike tana raye. 7Kuma ka yi wa'azin wadannan al'amura donsu zama marasa abin zargi. 8Amma idan mutum bai iya biyan bukatun 'yan'uwansa ba, musamman iyalin gidansa, ya musunci bangaskiya, kuma gara marar bi da shi. 9Bari a lisafta mace gwamruwa idan ba ta kasa shekara sittin ba, matar miji daya. 10A san ta da kyawawan ayyuka, ko ta kula da 'ya'yanta, ko tana mai karbar baki, ko mai wanke kafafun masubi, ko mai taimakon wadanda ake tsanantawa, mai naciya ga kowanne kyakkyawan aiki. 11Amma game da gwamraye masu kuruciya, kada a sa su cikin lissafi. Domin idan suka fada cikin sha'awoyin jiki da ke gaba da Almasihu, sukan so su yi aure. 12Ta wannan hanya ce sun tara wa kansu tsarguwa saboda sun tada alkawarinsu na fari. 13Sun saba da halin ragwanci, suna yawo gida gida. Ba zama raggwaye kawai su ka yi ba. Amma sun zama magulmata, masu shishshigi, masu karambani. Suna fadin abin da bai dace ba. 14Saboda haka ina so gwamraye masu kuruciya su yi aure, su haifi 'ya'ya, su kula da gida, domin kada a ba magabci zarafin zargin mu ga aikata mugunta. 15Domin wadansu sun rigaya sun kauce zuwa ga bin shaidan. 16Idan wata mace mai bada gaskiya tana da gwamraye, bari ta taimakesu, don kada a nawaita wa Ikilisiya, domin Ikilisiya ta iya taimakon gwamraye na gaske. 17Dattawa wadanda suke mulki da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman wadanda suke aiki da kalma da kuma koyarwa. 18Gama nassi ya ce, “Kada a sa takunkumi a bakin takarkari lokacin da yake sussukar hatsi,” kuma “Ma'aikaci ya cancanci a biya shi hakinsa.” 19Kada ka karbi zargi game da dattijo sai shaidu sun kai biyu ko uku. 20Ka tsauta wa masu zunubi gaban kowa domin sauran su ji tsoro. 21Na umarce ka a gaban Allah, da Almasihu Yesu, da zababbun mala'iku ka kiyaye ka'idodin nan ban da hassada kuma kada ka yi komai da nuna bambanci. 22Kada ka yi garajen dibiya wa kowa hannuwa. Kada ka yi tarayya cikin zunuban wani. Ka tsare kanka da tsabta. 23Kada ka ci gaba da shan ruwa. Amma, maimakon haka ka sha ruwan inabi kadan saboda cikinka da yawan rashin lafiyarka. 24Zunuban wadansu mutane a bayyane suke, sun yi gaba da su cikin hukunci. Amma wadansu zunubansu na bin baya. 25Haka kuma, wadansu kyawawan ayyukansu a bayyane suke, amma wadan sun ma ba su boyuwa.

Did you know?
Caring for Widows and Honoring Elders
- This chapter separates widows who are truly alone from those who still have children or grandchildren to care for them. A widow was to be enrolled only if she was at least sixty, had been the wife of one man, and was known for good deeds such as bringing up children, welcoming strangers, washing the feet of the saints, and helping the afflicted. Younger widows were not to be enrolled; they were advised to marry, have children, and manage their households.Sources: the Bible text itself
- The advice to younger widows is meant to deny the adversary any occasion for slander, and the chapter notes that some have already turned aside to follow Satan. Satan’s name means adversary or accuser, and in the New Testament it is used interchangeably with Diabolos, or the devil, more than thirty times.Sources: the Bible text itself · Satan
- Elders who lead well are called worthy of double honor, especially those who work hard at preaching and teaching. The chapter supports that with two sayings: an ox should not be muzzled while treading out the grain, and the worker is worthy of his wages. An accusation against an elder was not to be received except on the testimony of two or three witnesses.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org