Nations Bible

1 Timothy 6

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Bari duk wadanda ke bayi a karkashin karkiya su ga iyayengijinsu sun cancanci dukan daraja. Su yi haka domin kada a sabawa sunan Allah da koyarwarsa. 2Bayin da suke da iyayengiji da ke masu ba da gaskiya kada su rena su saboda su 'yan'uwa ne. A maimakon haka, su yi masu hidima da kwazo. Gama iyayengijin da suke cin ribar aikinsu masu bi ne, kaunattatu kuma. Ka koyar ka kuma bayyana wadannan abubuwa. 3Idan ya kasance wani na koyar da wani abu dabam bai kuma yarda da amintaciyar koyarwa ba, wato maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu. Alal misali ba su amince da koyarwa da ke kai ga Allahntaka ba. 4Wannan mutum mai girman kai ne, kuma bai san komai ba. A maimakon haka, yana da matukar jayayya da gardama game da kalmomi. Wadannan kalmomi na kawo kishi, da husuma, da zage-zage, da miyagun zace-zace, da 5yawan rashin jituwa tsakanin mutane masu rubabbun hankula. Sun bijire wa gaskiya. Suna tunani cewa ibada hanya ce ta yin arziki.” Ka zame daga wadannan abubuwa. 6Yanzu bin Allah tare da dangana babbar riba ce. 7Gama ba mu kawo komai a duniya ba, ba zamu iya fita cikinta da komai ba. 8A maimakon haka, mu dangana da abinci da kuma sutura. 9To wadanda ke son zama mawadata su kan fada cikin jaraba, cikin tarko. Suna fadawa cikin abubuwan wauta da sha'awoyi masu illa da kowanne abu da ke sa mutane su dulmaya cikin lallacewa da hallaka. 10Gama son kudi shine tushen kowacce irin mugunta. Wadansu mutane garin neman kudi sun kauce daga bangaskiya, sun kuma jawowa kansu bakin ciki mai yawa. 11Amma kai, mutumin Allah, ka guji wadannan abubuwa, ka bi adalci, ibada, aminci, kauna, jimiri, da tawali'u. 12Ka yi fama, fama mai kyau na bangaskiya. Ka kama rai madawami da aka kira ka gare shi. A kan wannan ne ka ba da shaida a gaban shaidu masu yawa game da abin da ke da kyau. 13Ina ba ka wannan umarni a gaban Allah wanda ke rayar da dukan abubuwa, da gaban Almasihu Yesu, wanda ya fadi abin da ke gaskiya ga Bilatus Babunti. 14Ka bi doka daidai, babu abin zargi har bayanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 15Allah zai nuna bayyanuwarsa a daidai lokaci- Allah, mai albarka, Makadaicin iko, Sarkin da ke sarauta, Ubangiji mai mulki. 16Shine kadai marar mutuwa, mai zama cikin hasken da ba ya kusantuwa. Ba wanda ke ganinsa, ko ya iya hango shi. Girma ya tabbata a gare shi da kuma madawwamin iko. Amin. 17Ka gaya wa masu dukiya a cikin wannan duniya kada su daga kai, kada su sa bege ga arziki mara dawwama. Maimamakon haka, su sa begensu ga Allah wanda ke ba mu wadatar gaske domin jin dadin mu. 18Gaya masu su yi nagarta su arzurta a ayyuka nagari, su zama masu bayarwa hannu sake. 19Ta haka za su ajiye wa kansu harsashi mai kyau kan abin da ke zuwa domin su amshi rayuwa ta kwarai. 20Timoti, ka kare abin da aka ba ka. Ka nisanci maganar wauta da gardamomin da ke sabawa juna wanda ake kira ilimi a karyace. 21Wadansu mutane suna shelar wadannan abubuwa, don haka sun kauce wa bangaskiyar. Bari alheri ya kasance tare da kai.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Godliness, Contentment, and Timothy's Charge

  • This chapter's solemn charge recalls that Christ Jesus made the good confession in his testimony before Pontius Pilate. Pilate was the sixth Roman procurator of Judea, from A.D. 26 to 36, with headquarters at Caesarea, though he often went up to Jerusalem; his time in office covered the ministries of John the Baptist and of Jesus, and his name is remembered especially in connection with Jesus' trial.Sources: the Bible text itself · Pontius Pilate
  • The chapter addresses Timothy as a man of God and tells him to guard what has been entrusted to him. The name Timotheus means honoring God. He was a young disciple and Paul's companion on many journeys; his mother Eunice and his grandmother Lois are mentioned as eminent for their piety, and his father was a Greek.Sources: the Bible text itself · Timotheus

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.