1 Timothy 4
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1To Ruhu ya fada a fili cewa, a zamanin karshe wadansu mutane za su kauce daga bangaskiya, su mai da hankalin su ga ruhohi masu rudi, da koyarwar aljannu, 2cikin karya da munafunci. Lamirinsu zai yi kanta. 3Za su haramta aure da karbar abincin da Allah ya halitta, domin su raba da godiya a cikin wadanda suka bada gaskiya suka kuma san gaskiyar. 4Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau. Domin duk abin da muka karba da godiya, bai kamata mu ki shi ba. 5Gama an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da addu'a. 6Idan ka tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa za ka zama bawan kirki na Almasihu. Domin ana gina ka ne ta wurin maganar bangaskiya da kuma kyakkyawar koyarwa wadda ka bi. 7Amma ka guji labaran almara wadanda tsofaffin mata ke so. Maimakon haka sai ka hori kanka cikin bin Allah. 8Domin horon jiki ya na da amfani kadan. Amma horon kai cikin bin Allah yana da amfani ga dukkan abubuwa. Gama a cikinsa akwai alkawari domin wannan rayuwar da kuma rayuwa mai zuwa. 9Maganan nan amintacciyace ta isa a karbe ta dungum. 10Dalilin da ya sa kenan mu ke aiki tukuru. Domin muna sa bege ga Allah mai rai, mai ceton dukkan mutane, musamman masu ba da gaskiya. 11Ka yi shela ka kuma koyar da wadannan abubuwa. 12Kada ka yarda kowa ya rena kuruciyarka. Maimakon haka, ka zama abin koyi ga dukkan masubi: a furci, hali, kauna, aminci da kuma tsarki. 13Har sai na zo, ka himmatu da yin karatu, da wa'azi, da kuma koyarwa. 14Kada ka yi sakaci da baiwar da ka ke da ita wadda aka baka ta wurin anabci sa'ad da dattawa suka dibiya maka hannayensu. 15Ka kula da wadannan abubuwa. Ka himmatu a cikinsu. Domin ci gabanka ya zama sananne a idanun kowa. 16Ka kula da kanka da kuma koyawarka. Ci gaba a cikinsu. Domin ta yin haka ne za ka ceci kanka da masu sauraronka.

Did you know?
False Teaching and Godly Training
- The chapter says the Spirit expressly states that in later times some will abandon the faith to follow deceitful spirits and the teachings of demons. They are influenced by the hypocrisy of liars whose consciences are seared with a hot iron, and they will prohibit marriage and require abstinence from certain foods.Sources: the Bible text itself
- The letter answers those demands by saying God created such foods to be received with thanksgiving by those who believe and know the truth. Every creation of God is good, and nothing received with thanksgiving should be rejected, because it is sanctified by the word of God and prayer.Sources: the Bible text itself
- The writer urges the young person he addresses not to let anyone despise his youth, but to set an example in speech, conduct, love, faith, and purity. Until the writer comes, he is to devote himself to the public reading of Scripture, to exhortation, and to teaching, and not neglect the gift given through prophecy when the elders laid hands on him. Physical exercise, the letter adds, is of limited value, while godliness is valuable in every way, holding promise for the present life and the life to come, a saying the letter calls trustworthy and worthy of full acceptance.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org