Nations Bible

1 Timothy 3

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Wannan magana tabattaciya ce: Idan wani na da marmari ya zama shugaban Ikilisiya, ya na marmarin aiki mai kyau. 2Don haka, wajibi ne shugaban Ikilisiya ya zama mara abin zargi. Ya zama mai mace daya. Wajibi ne ya zama mai kamewa, mai hankali, mai natsuwa mai karbar baki. Wajibi ne ya iya koyarwa. 3Kada ya zama mashayin giya, da mai tankiya. A maimakon haka ya zama da natsuwa, mai salama. Ba mai son kudi ba. 4Wajibi ne ya iya lura da gidansa da kyau, 'ya'yansa su zama masu yi masa biyayya da dukkan bangirma. 5Gama idan mutum bai iya sarrafa gidansa ba, ta yaya zai iya lura da Ikkilisiyar Allah? 6Bai kamata ya zama sabon tuba ba, domin kada ya kumbura da girman kai, kada ya fadi cikin irin hukunci da aka yi wa Ibilis. 7Wajibi ne kuma ya kasance mai kyakyawar shaida a cikin wadanda ba masubi ba, domin kada ya fadi cikin kunya da kuma tarkon Ibilis. 8Hakanan kuma Dikinoni su kasance da halin mutunci, ba masu magana biyu ba. Bai kamata su zama mashayan giya ko masu hadama ba. 9Su zama masu rikon bayyananniyar gaskiyar bangaskiya da lamiri mai tsabta. 10Daidai ne kuma a fara tabbatar da su, daga nan su fara hidima domin basu da abin zargi. 11Hakanan ma mata su zama masu mutunci. Bai kamata su zama magulmanta ba, amma masu kamewa da aminci cikin komai. 12Tilas Dikinoni su zama masu mata daya daya. Su iya kulawa da 'ya'yansu da gidajensu. 13Gama wadanda suka yi hidima da kyau sun sami tsayawa mai kyau da gabagadi cikin bangaskiyar da ke cikin Almasihu Yesu. 14Ina rubuta maka wadannan abubuwa, da sa zuciya zan zo wurin ka ba da jimawa ba. 15Amma idan na yi jinkiri, ina rubuta maka ne domin ka san yadda za ka gudanar da al'amuranka a cikin gidan Allah, wato Ikklisiyar Allah rayyayiya, ginshiki da kuma mai tallafar gaskiya. 16Babu musu an bayyana cewa ibadarmu ta gaskiya da girma take: “Ya bayyana kansa cikin jiki, Ruhu ya baratar da shi, mala'iku suka gan shi, aka yi shelarsa a cikin al'ummai, aka gaskanta shi a duniya, sa'an nan aka dauke shi sama cikin daukaka.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Overseers, Deacons, and God's Household

  • The chapter says that anyone who aspires to be an overseer desires a noble task, yet he must be above reproach: the husband of one wife, temperate, hospitable, able to teach, gentle, and free from the love of money, among other qualities. He must manage his own household and keep his children under control with complete dignity, for the writer asks how someone who cannot do that can care for the church of God. He must not be a recent convert, or he may become conceited and fall under the same condemnation as the devil, and he must have a good reputation with outsiders.Sources: the Bible text itself
  • Deacons must be dignified, not double-tongued, not given to much wine, and not greedy for money, and they must hold the mystery of the faith with a clear conscience. They are to be tested first and may serve only if above reproach; like the overseer, a deacon must be the husband of one wife and manage his children and his own household well. The chapter also says that the women must be dignified, not slanderers, but temperate and faithful in all things, and that those who serve well as deacons gain a high standing and great confidence in the faith that is in Christ Jesus.Sources: the Bible text itself
  • The writer hopes to come soon, but writes in case of delay, so that the recipient will know how each one must conduct himself in God's household, the church of the living God, the pillar and foundation of the truth. The chapter closes with a common confession that the mystery of godliness is great: he appeared in the flesh, was vindicated by the Spirit, was seen by angels, was proclaimed among the nations, was believed in throughout the world, and was taken up in glory.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.