Romanos 3
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1To ina fifikon da bayahude yake dashi? Kuma ina ribar kaciya? 2Akwai muhimmancinsu ta kowacce hanya. Tun farko dai, yahudawa ne aka dankawa wahayi daga Allah. 3Idan wasu yahudawa basu bada gaskiya ba fa? Rashin bangaskiyarsu zai hana amincin Allah aiki? 4Bazai taba zama haka ba. Maimakon haka, bari Allah ya zama mai gaskiya, ko da kowanne mutum makaryaci ne. Kamar yadda aka rubuta, “Domin a nuna kai mai adalci cikin maganganunka, kuma kayi nasara a lokacin da aka kawo ka gaban shari'a.” 5Amma idan rashin adalcinmu ya nuna adalcin Allah, to me zamu ce? Allah ba marar adalci ba ne, wanda ke aiwatar da fushinsa, ko kuwa? Ina magana bisa ga tunanin mutuntaka. 6Bazai taba zama haka ba. Domin idan haka ne ta yaya Allah zai shar'anta duniya? 7Amma idan gaskiyar Allah ta wurin karyata ta habaka yabonsa, To me yasa ake shar'anta ni a matsayin mai zunubi? 8To me zai hana ace kamar yadda ake fadin zancen karya a kanmu, wasu kuma sun dauka cewa mun fadi hakan, “Bari muyi mugunta, domin nagarta tazo?” Hukuncin su halal ne. 9To me kenan? Zamu ba kanmu hujja ne? ko kadan. Domin mun riga munyi zargin yahudawa da hellinawa, da cewar dukkansu, suna karkashin zunubi. 10Kamar yadda aka rubuta, babu wani mai adalci, babu ko daya. 11Babu wani mai fahimta. Babu wani mai neman Allah. 12Dukansu sun kauce hanya, dukansu gaba daya sun zama marasa amfani. Babu mai aikin nagarta, a'a, babu ko da guda daya. 13Makogwaronsu a bude yake kamar kabari. Harsunansu na dauke da cuta. Dafin macizai na karkashin lebunansu. 14Bakunansu cike suke da la'ana da daci. 15Sawayensu na saurin zuwa zubar da jini. 16Tafarkinsu wahala ce da lalacewa. 17Wadannan mutane basu san hanyar salama ba. 18Babu tsoron Allah a idanunsu.” 19To mun san dai duk abin da shari'a tace, shari'a na magana ne da wadanda ke karkashinta, domin a rufe kowanne baki, domin dukan duniya ta bada amsa a gaban Allah. 20Domin a gabansa babu wanda zai barata ta wurin ayukan shari'a. Domin ta wurin shari'a ne sanin zunubi yazo. 21Amma yanzu ba tare da shari'a ba an bayyana sanin adalcin Allah, wanda shari'a da annabawa suke shaidawa. 22Wato, adalcin Allah ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ga dukkan wadanda ke bada gaskiya. Domin babu bambanci: 23Domin duk sun yi zunubi sun kuma kasa kaiwa ga darajar Allah, 24Da alherinsa an baratar da mu ta wurin fansar dake cikin Yesu Almasihu. 25Amma Allah ya bayar da Yesu Almasihu wanda yake hadayar fansa ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya mika Almasihu a matsayin tabbacin hukuncinsa, sabo da kuma ketarewar zunubanmu na baya 26cikin hakurinsa. Duk wannan ya faru ne domin a bayyana adalcinsa cikin wannan zamani, domin ya tabbatar da kansa mai hukunci, kuma ya nuna shine mai baratar da kowa saboda bangaskiya cikin Yesu. 27To ina fahariya? An fitar da ita. A kan wane dalilin? Don ayyuka? A'a, amma ta dalilin bangaskiya. 28Domin wannan muka kammala cewar ana baratar da mutum ta wurin bangaskiya ba tare da ayyukan shari'a ba. 29Ko kuwa Allah Allahn yahudawa ne kadai? Shi ba Allahn al'ummai bane? I, na al'ummai ne kuma. 30Idan dai lallai Allah daya ne, zai baratar da mai kaciya ta wurin bangaskiya, da marar kaciya kuma ta wurin bangaskiya. 31Mun kawar da shari'a kenan ta wurin bangaskiya? ba zai taba kasancewa haka ba. Maimako ma, muna inganta shari'a kenan.
Você sabia?
Todos sob o pecado, justificados pela fé
- Romanos 3 começa perguntando qual é a vantagem de ser judeu e qual é o valor da circuncisão. A resposta é que há muita vantagem em todos os sentidos e, antes de tudo, que lhes foram confiadas as próprias palavras de Deus. O capítulo argumenta, então, que, se alguns não tiveram fé, essa falta de fé não anula a fidelidade de Deus.Fontes: o próprio texto bíblico
- Para sustentar a acusação de que judeus e gregos estão igualmente sob o pecado, o capítulo reúne trechos introduzidos por “como está escrito”: não há justo, ninguém entende nem busca a Deus, a fala é descrita como engano e veneno, os pés se apressam para derramar sangue, e não há temor de Deus. O texto diz que a lei fala aos que estão debaixo dela, para que toda boca se cale e o mundo inteiro seja responsável diante de Deus, e que ninguém é justificado pelas obras da lei, porque a lei traz o conhecimento do pecado.Fontes: o próprio texto bíblico
- Com as palavras “Mas agora”, o capítulo afirma que, à parte da lei, a justiça de Deus foi revelada, testemunhada pela Lei e pelos Profetas, e que ela vem pela fé em Jesus Cristo a todos os que creem, sem distinção. Todos pecaram e ficam aquém da glória de Deus, e são justificados gratuitamente pela sua graça, por meio da redenção que há em Cristo Jesus. A vanglória fica excluída pelo princípio da fé, não das obras; há um só Deus, que justifica os circuncidados pela fé e os incircuncisos por essa mesma fé, e o capítulo diz que essa fé sustenta a lei em vez de anulá-la.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org