Nations Bible

Romanos 2

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Saboda da haka baka da hujja, kai mutum, kai mai shara'antawa, domin kuwa abinda kake shara'antawa akan wasu kana kada kanka da kanka. Domin kuwa kai mai shar'antaawa kana aikata wadannan abubuwa. 2Amma mun san cewa shari'ar Allah ta gaskiya ce sa'adda zata fado wa masu aikata wadannan irin abubuwa. 3Amma ka lura da wannan, ya kai mutum, mai shara'anta masu aikata wadannan ababuwa. Duk da shike kaima kana aikatawa. Kana jin zaka kubucewa hukuncin Allah? 4Ko kana raina falalar alheransa da yake yi ta wajen jinkirin hukuncinsa, da hakurinsa? Baka san cewa alheransa musanman domin su kai ka ga tuba bane? 5Amma saboda taurin kanka da zuciyarka marar tuba, kana tanadarwa kanka fushi, a ranar fushi, wato ranar bayyanuwar shari'ar adalci ta Allah. 6Zai baiwa kowanne mutum daidai sakamakon ayyukansa: 7Ga wadanda kuma suka nace da yin ayyukan alheri ba fasawa, sun samarwa kansu, yabo da daraja, da rai na har'abada. 8Amma ga masu son kai, wadanda suka ki yin biyayya ga gaskiya, suka yiwa rashin adalci biyayya, fushi da hasala mai zafi zai afko masu. 9Allah kuma zai sauko da bala'i da bakin ciki ga dukkan rayukan da suka aikata mugunta, ga Yahudawa da fari, sannan kuma Hellinawa. 10Amma yabo daraja da salama zasu kasance ga dukkan wadanda suka aikata ayukan alheri, ga Yahudawa da fari sannan Hellanawa. 11Domin kuwa Allah ba mai tara bane. 12Ga wadanda suka yi zunubi batare da shari'aba, zasu hallaka ba tare da shari'a ba, ga wadanda suka yi zunubi cikin shari'a kuma za'a hukunta su bisa ga shari'a. 13Domin kuwa ba masu jin shari'ar ne masu adalci agaban Allah ba, amma masu aikatawa ne zasu samu barata. 14Gama al'umai da basu san shari'a ba, bisa ga dabi'a sun yi abinda ke na shari'a, sun kuma zame wa kansu shari'a, koda shike basu da shari'ar. 15Dalilin haka kuwa sun nuna cewa ayukan da shari'a take bukata na nan a rubuce a zuciyarsu. lamirinsu kuma na yi masu shaida, tunanainsu kuma, ko dai yana kashe su, ko kuma yana karesu. 16hakanan kuma ga Allah. Wannan zai faru ranar da Allah zai shara'anta asiran boye na dukkan mutane, bisa ga bishara ta cikin Yesu Almasihu. 17Da shike kana kiran kanka Bayahude, kana zaune akan shari'a, kana alfahari cikin Allah, 18ka san nufinsa, ka kuma san abubuwan da suka bambanta da hakan, ka kuma sami koyarwa cikin shari'ar. 19Da shike kana da gabagadi akan cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga wadanda suke cikin duhu, 20mai horo ga marasa hikima, mai koyar da jarirai, kuma a cikin shari'ar kana da abin da ya shafi sani da kuma gaskiya. 21ku da kuke koyar da wadansu, ba ku koyar da kanku? ku da kuke wa'azi kada ayi sata, ba ku yin sata? 22Ku da ke wa'azi kada ayi zina, ba ku yin zina? ku da ke hana bautar gumaka, ba ku yin sata a haikali? 23ku masu murna da tinkaho cikin shari'ar, ba kwa wulakanta Allah cikin kurakuranku na rashin bin shari'a? 24''Domin kuwa an wulakanta sunan Allah cikin Al'umai sabili da ku,'' kamar yadda aka riga aka rubuta. 25Lallai kuwa kaciya tana da riba a gare ku, idan kuka kiyaye doka, amma idan ku marasa bin doka ne kaciyarku ta zama rashin kaciya. 26domin kuwa idan mutum marar kaciya zai kiyaye dukkan bukatun doka, baza'a iya daukan rashin kaciyarsa a matsayin mai kaciya ba? 27Sannan idan mutum marar kaciya ta jini zai kiyaye dukkan dokoki, ba zai iya shara'anta ku masu kaciya ta shari'a ba? Haka kuma ya kasance ne domin kuna da shari'a a rubuce da kuma kaciya amma ba kwa bin doka! 28Domin shi kuwa ba Bayahude bane a waje; ba kuwa mai kaciyar da aka tsaga fata ba. 29Amma Bayahude ne ta ciki, sanna kuma mai kaciyar zuciya da kuma ruhu ba wasika ba, irin wanna mutumin yabonsa ba daga wurin mutane yake zuwa ba, amma daga Allah.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Julgamento sem favoritismo

  • Romanos 2 adverte que quem julga os outros enquanto faz as mesmas coisas condena a si mesmo, porque o julgamento de Deus se baseia na verdade. O capítulo diz que Deus não mostra favoritismo: haverá tribulação e angústia para todo ser humano que pratica o mal, e glória, honra e paz para todo aquele que pratica o bem, primeiro para o judeu e depois para o grego.Fontes: o próprio texto bíblico
  • O capítulo distingue quem peca sem a lei de quem peca debaixo da lei: os primeiros também perecerão sem a lei, e os segundos serão julgados pela lei. Diz que não são os ouvintes da lei que são justos diante de Deus, mas os que a praticam. Os gentios que não têm a lei, mas por natureza fazem o que ela exige, são lei para si mesmos e mostram que a obra da lei está escrita em seus corações, enquanto a consciência testemunha e os pensamentos os acusam ou os defendem.Fontes: o próprio texto bíblico
  • Falando a quem se chama judeu, confia na lei e está convencido de que é guia e mestre, o capítulo pergunta se ele ensina a si mesmo — se rouba, comete adultério ou saqueia templos enquanto condena esses atos. A circuncisão tem valor se a lei é observada, mas, se a lei é transgredida, a circuncisão se tornou incircuncisão. O homem é judeu interiormente, e a circuncisão é questão do coração, pelo Espírito, não pelo código escrito; o louvor dele não vem dos homens, mas de Deus.Fontes: o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.