Nations Bible

Apocalipse 19

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Bayan wadannan abubuwa na ji wata karar da ta yi kamar muryar mutane masu yawa a sama suna cewa, “Halleluya. Ceto, daukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu. 2Hukunce - hukuncensa gaskiya ne da adalci, domin ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta kazamtar da duniya da fasikancinta. Ya dauki fansar jinin bayinsa, wadda ita da kanta ta zubar.” 3Suka yi magana a karo na biyu: “Halleluya! Hayaki na tasowa daga wurinta har abada abadin.” 4Dattawan nan ashirin da hudu da rayayyun halittun nan hudu, suka fadi suka yi wa Allah sujada shi da yake zaune a kan kursiyin. Suna cewa, “Amin. Halleluya!” 5Sai wata murya ta fito daga kursiyin tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku bayinsa, ku da kuke tsoronsa, da duk marasa iko da masu iko.” 6Sai na ji murya kamar na kasaitaccen taron mutane, kamar rurin kogi na ruwaye masu yawa, kuma kamar tsawar aradu, cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji yana mulki, Allah mai iko duka. 7Bari mu yi murna, mu yi farinciki matuka mu kuma ba shi daukaka domin bikin auren Dan Ragon ya zo, amaryarsa kuma ta shirya kanta. 8An yardar mata ta sa kaya masu haske da tsabta na lilin mai laushi” (domin lilin mai laushi shine ayyukan adalci na tsarkaka). 9Mala'ika ya ce mani, “Rubuta wannan: Masu albarka ne wadanda aka gayyace su zuwa bikin auren Dan Ragon.” Ya kuma ce mani, “Wadannan kalmomin Allah na gaskiya ne.” 10Na fadi a gaban kafafunsa domin in yi masa sujada, amma ya ce mani, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne tare da kai da 'yan'uwanka wadanda ke rike da shaida game da Yesu. Yi wa Allah sujada, domin shaida game da Yesu shine ruhun annabci.” 11Sai na ga sama a bude, na kuma duba sai ga wani farin doki. Mahayinsa ana kiransa amintacce da gaskiya. Yana shari'a da adalci yana yaki. 12Idanunsa kamar harshen wuta suke, a kansa akwai kambuna da yawa. Yana da suna a rubuce a jikinsa wanda ba wani da ya sani sai dai shi da kansa. 13Yana sanye da riga da aka tsoma a cikin jini, kuma ana kiran sunansa Kalmar Allah. 14Rundunonin sama suna biye da shi a kan fararen dawakai, suna sanye da lilin mai laushi, fari mai tsabta. 15Daga cikin bakinsa takobi mai kaifi na fitowa, da ita yake sarar al'ummai, zai kuma mulke su da sandar karfe. Yana tattake wurin matsar ruwan inabi da matsananciyar fushin Allah Mai iko duka. 16Yana da suna a rubuce a rigarsa da cinyarsa: “Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.” 17Na ga mala'ika tsaye a rana. Yayi kira da murya mai karfi ga dukan tsuntsaye da ke firiya a sama. 18“Ku zo, ku tattaru saboda babban bukin Allah. Ku zo ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaki, da naman manyan mutane, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman dukan mutane, yantattu da bayi, marasa iko da masu iko.” 19Na ga dabban da sarakunan duniya da rundunoninsu. Suna tattaruwa domin su yi yaki da wanda ke bisa doki da rundunarsa. 20Aka kama dabban tare da makaryatan annabawa da suka yi ayyukan al'ajibai a gabansa. Da wadannan alamu ya yaudari wadanda suka karbi alamar dabbar da wadanda suka yi wa siffarta sujada. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin farar wuta mai ci. 21Sauran aka karkashe su da takobin da ke fitowa daga bakin mahayin dokin. Dukan tsuntsaye suka ci gawarwakinsu.

Você sabia?

O aleluia do céu e as bodas do Cordeiro

  • Este capítulo registra quatro vezes o grito “Aleluia”. Ouve-se um som como o de uma grande multidão no céu, que louva a Deus porque os seus juízos são verdadeiros e justos: ele julgou a grande prostituta que corrompeu a terra com a sua imoralidade e vingou o sangue dos seus servos, derramado pela mão dela. Os vinte e quatro anciãos e os quatro seres viventes se prostram e adoram a Deus, que está sentado no trono, dizendo “Amém, Aleluia”, e uma voz vinda do trono chama a louvá-lo todos os que o servem e o temem, pequenos e grandes.Fontes: o próprio texto bíblico
  • A multidão anuncia que chegaram as bodas do Cordeiro e que a sua noiva já se preparou. Ela recebe vestes de linho fino, resplandecente e puro, e o próprio texto explica que esse linho fino são os atos justos dos santos. Um anjo manda que João escreva que são bem-aventurados os convidados à ceia das bodas do Cordeiro e declara que essas são as verdadeiras palavras de Deus.Fontes: o próprio texto bíblico
  • João cai aos pés do anjo para adorá-lo, mas o anjo não permite. Diz que é conservo de João e dos irmãos de João que se apoiam no testemunho de Jesus, e ordena que adore a Deus, pois o testemunho de Jesus é o espírito da profecia. Em seguida o céu se abre, e João vê um cavaleiro num cavalo branco, chamado Fiel e Verdadeiro, cujo nome é a Palavra de Deus; da sua boca sai uma espada afiada, e no manto e na coxa está escrito Rei dos reis e Senhor dos senhores.Fontes: o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.