Nations Bible

Apocalipse 18

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Bayan wadannan abubuwa sai na ga wani mala'ika yana saukowa daga sama. Yana da babban iko sosai, duniya kuwa ta haskaka da daukakarsa. 2Ya yi kira da kakkarfar murya cewa, “Ta fadi, Babila mai girma ta fadi! Ta zama mazaunin aljannu, da matattarar kowanne kazamin ruhu da kuma mazaunin kowanne kazami da kyamataccen tsuntsu. 3Gama dukan al'ummai sun sha ruwan innabin fasikancinta. Sarakunan duniya sun aikata fasikanci da ita. Attajiran duniya sun arzuta da ikon rayuwar annashuwarta.” 4Sai na ji wata murya daga sama ta ce, “Ku fito daga cikinta, mutanena, domin kada kuyi zunubi irin na ta, domin kuma kada bala'inta ya auko maku. 5Zunubanta sun taru sun yi tsayi har sama. Allah kuma ya tuna da miyagun ayyukanta. 6Ku saka mata gwargwadon yadda ta saka wa wadansu, ku biya ta ninki biyu na abin da ta yi; a cikin kokon da ta dama, ku dama mata ninki biyu. 7Kamar yadda ta daukaka kanta ta yi ta annashuwa, ku wahalsheta da azaba da bakin ciki haka. Domin ta ce a zuciyarta, 'Ina zaune kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taba yin makoki ba,' 8Saboda haka a rana daya bala'inta zai auko mata; mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta za ta kona ta kurmus, domin Ubangiji Allah mai iko ne, kuma shine mai hukuntata.” 9Sarakunan duniya da suka yi fasikanci, har suka baude tare da ita, za su yi kuka da kururuwa domin ta sa'adda suka ga hayakin kunarta. 10Za su tsaya can nesa suna tsoron azabarta, suna cewa, “Kaito, kaiton babban birni, Babila, birni mai iko! Domin cikin sa'a guda hukuncinta ya zo.” 11Manyan 'yan kasuwan duniya za su yi kuka da bakin ciki dominta, da shike ba wanda ke sayan kayanta kuma - 12kayan zinariya, azurfa, da duwatsun alfarma, da lu'u-lu'u, da lilin mai laushi, da hajja mai ruwan jar garura, da siliki, da jar alharini da itacen kamshi iri iri, da kayan da aka sassaka da itace mai tsada, da na tagulla, da na bakin karfe, da na dutse mai sheki, 13da kirfa, da kayan yaji, da turaren wuta, da mur da lubban, da ruwan innabi, da mai, da garin alkama, da alkama, da shanu, da tumaki, da dawakai, da kekunan doki, da bayi, da rayukan 'yan adam. 14Amfanin da kika kwallafa rai da duk karfinki sun fice daga gareki. Duk annashuwarki da darajarki sun bace, ba za a kara samunsu ba kuma. 15Manyan 'yan kasuwa na wadannan kaya da suka azurta ta wurinta, za su tsaya can nesa da ita, sabili da tsoron azabarta, kuka da kururuwar bakin ciki. 16Za su ce, “Kaito, kaito ga babban birni da take sanye da lilin mai laushi da tufafi masu jar garura da kuma jan alharini, da ta ci ado da kayan zinariya, da duwatsu masu daraja da lu'u-lu'u! 17A cikin sa'a guda duk dukiyan nan ta lallace. Kowanne matukin jirgin ruwa, da fasinjoji, da masu tuki da duk wadanda suke samun biyan bukatun rayuwarsu daga ruwa, suka tsaya can nesa. 18Suka yi kuka sa'anda suka ga hayakin kunarta. Suka ce, “Wanne birni ne ya yi kama da babban birnin?” 19Suka watsa kura a kawunansu, suka yi kuka da karfi, da kururuwa da bakin ciki, “Kaito, kaiton babban birnin nan inda duk masu jiragen ruwa suka azurta daga dukiyarta. Domin a sa'a guda an hallakar da ita.” 20“Ku yi murna a kanta, sama, ku masu ba da gaskiya, manzanni, da annabawa, domin Allah ya kawo hukuncinku a kanta!” 21Wani kakkarfan mala'ika ya dauki wani dutse mai kama da dutsen nika, ya jefa shi cikin teku yana cewa, “Ta wannan hanya, Babila, babban birnin, za a jefar da ita kasa da karfi, ba za a kara ganinsa ba. 22Muryar masu kidar molaye, mawaka, masu busa sarewa, da na masu busa algaita, ba za a kara ji a cikinta ba. Babu wani mai kowanne irin sana'a da za a samu a cikinta. Ba za a kara jin karar nika a cikinta ba. 23Hasken fitila ba za ya kara haskakawa a cikin ki ba. Ba za a kara jin muryoyin ango da na amarya a cikinki ba, domin attajiranki sune 'ya'yan masu mulki a duniya, kuma ta wurin sihirinki kika yaudari al'ummai. 24A cikinta aka sami jinin annabawa da na masu ba da gaskiya, da jinin duk wadanda aka kashe a duniya.”

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

A queda da grande Babilônia

  • “Babilônia”, neste capítulo, é a forma grega do nome Babel. Um dicionário bíblico apresenta a forma semítica Babilu, que significa “a porta de Deus”, e observa que as tábuas assírias a chamam de “a cidade da dispersão das tribos”. A mesma entrada situa a cidade junto ao Eufrates, cerca de duzentas milhas acima da confluência desse rio com o Tigre.Fontes: Babylon · o próprio texto bíblico
  • O capítulo mostra a riqueza de Babilônia por meio de quem lucrava com ela. Os reis que viveram no luxo com ela, e os capitães de navio, marinheiros e outros que viviam do mar, ficam à distância e choram ao ver a fumaça do fogo que a consome. Os mercadores pranteiam porque já não há quem compre sua carga, que vai do ouro, da púrpura, da seda e das especiarias até o gado, os cavalos, os carros e escravos e almas de homens.Fontes: o próprio texto bíblico
  • A queda é apresentada como súbita e definitiva. No coração, a cidade diz que se assenta como rainha, que não é viúva e que jamais verá pesar; o capítulo, porém, diz que morte, pesar e fome chegam num só dia e que ela é consumida pelo fogo, enquanto os que observam de longe clamam que o desastre chegou numa só hora. Um anjo poderoso lança ao mar uma pedra do tamanho de uma grande mó e declara que Babilônia será derrubada com a mesma violência e nunca mais será vista; cessam a música, o trabalho dos artesãos, o som da mó, a luz das lâmpadas e as vozes da noiva e do noivo.Fontes: o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Babylon · Hoje: Rome · 41.892, 12.485 · versículos 2, 10, 21

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.