Mateus 28
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Da daddare ranar Asabaci, rana ta fari ga mako ta fara gabatowa, Maryamu Magadaliya da daya Maryamun suka zo don su ziyarci kabarin. 2Sai aka yi girgizar kasa mai karfi, saboda mala'ikan Ubangiji ya sauko daga sama ya kuma murgine dutsen ya zauna a kai. 3Kamanninsa kamar walkiya, tufafinsa kuma fari fat kamar suno. 4Masu tsaron suka razana don tsoro suka zama kamar matattun mutane. 5Mala'ikan ya yi wa matan magana cewa, “Kada ku ji tsoro, nasan kuna neman Yesu wanda aka gicciye. 6Baya nan, amma ya tashi kamar yadda ya fada. Ku zo ku ga wurin da aka kwantar da shi. 7Ku hanzarta ku gaya wa almajiransa, 'Ya tashi daga matattu. Duba, ya tafi Galili, can zaku same shi.' Gashi ni kuwa na fada maku.” 8Matan suka yi hanzari suka bar kabarin da tsoro da murna, suka ruga domin su sanar wa almajiransa. 9Sai ga Yesu ya tare su, yace masu, “A gaishe ku.” Sai matan suka kama kafar sa, suka kuma yi masa sujada. 10Sai Yesu yace masu, “Kada ku ji tsoro. Ku je ku fada wa 'yan'uwana su je Galili. Can zasu ganni.” 11Sa'adda matan suke tafiya, sai wadansu masu tsaro suka shiga gari suka fada wa Shugabanin Firistoci dukan abin da ya faru. 12Firistocin suka hadu da dattawa suka tattauna al'amarin, sai suka bada kudi masu yawa ga sojojin 13Sukace masu, “Ku gaya wa sauran cewa, “Almajiran Yesu sun zo da daddare sun sace gangar jikinsa lokacin da muke barci.” 14Idan wannan rahoto ya isa wurin gwamna, za mu lallashe shi mu ja hankalinsa mu raba ku da damuwa.” 15Sai sojojin suka karbi kudin suka yi abinda aka umarcesu. Wannan rahoto ya bazu a tsakanin Yahudawa, ya ci gaba har zuwa yau. 16Amma almajiran sha daya suka tafi Galili, kan dutsen da Yesu ya umarcesu. 17Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma wadansu suka yi shakka. 18Yesu ya zo wurin su ya yi masu magana, yace, “Dukan iko dake sama da kasa an ba ni. 19Sai kuje ku almajirantar da dukan al'ummai. Kuna yi masu baftisma cikin sunan Uba da na Da da na Ruhu Mai Tsarki. 20Ku koya masu su kiyaye dukan abin da na umarce ku. Duba, ni kuma kullum ina tare da ku har karshen zamani.”

Você sabia?
A ressurreição e a Galileia
- Maria Madalena, que foi ao túmulo ao amanhecer com a outra Maria, tem um sobrenome derivado de Magdala, o lugar onde nasceu, para distingui-la das outras Marias dos Evangelhos. Um verbete de dicionário considera equivocada a noção de que ela era a mulher chamada pecadora em Lucas 7.Fontes: Mary Magdalene · o próprio texto bíblico
- O anjo e, em seguida, Jesus disseram às mulheres que ele iria adiante dos discípulos para a Galileia, e os onze foram depois a um monte ali que ele havia designado. Os judeus chamavam a região de Galil; como ela permaneceu por muito tempo ocupada por seus habitantes originais, passou a ser chamada Galileia dos gentios e também Alta Galileia, para distingui-la de um amplo acréscimo feito mais tarde em direção ao sul, geralmente chamado Baixa Galileia.Fontes: Galilee · o próprio texto bíblico
- O capítulo registra que alguns dos guardas contaram aos chefes dos sacerdotes o que havia acontecido e que os chefes dos sacerdotes, depois de se reunirem com os anciãos, deram aos soldados uma grande soma em dinheiro para que dissessem que os discípulos vieram de noite e roubaram o corpo enquanto os guardas dormiam. Acrescenta que esse relato tem circulado entre os judeus até o dia de hoje.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org