Nations Bible

Mateus 27

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Da gari ya waye, duk manyan firistoci da dattawan jama'a suka shirya yadda zasu kulla makirci domin su kashe shi. 2Suka daure shi, suka mika shi ga gwamna Bilatus. 3Sa'adda Yahuza, wanda ya bashe shi, ya ga an zartarwa Yesu hukuncin kisa, ya nemi tuba ya kuma mayar da azurfar talatin ga manyan firistocin da dattawan, 4yace, “Na yi zunubi ta wurin cin amanar mara laifi.” Amma sukace, “Ina ruwan mu? Ka ji da shi da kanka?” 5Sai ya jefar da kwandalolin azurfar a kasa cikin haikalin ya kuma bar su, ya tafi ya rataye kansa. 6Sai babban firist ya dauki kwandalolin azurfar ya ce, “Ba daidai bane bisa ga shari'a musa wannan cikin ma'aji, saboda kudin jini ne.” 7Sai suka tattauna al'amarin a tsakanin su, kudin kuma suka sayi filin maginin tukwane domin makabatar baki. 8Dalilin wannan ne ake kiran wurin, “Filin jini” har yau. 9Sai abin da aka fada ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa, “Suka dauki tsabar azurfa talatin na farashin da mutanen Isra'ila suka sa a kansa, 10suka bayar domin sayen filin mai tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.” 11Sai Yesu ya tsaya a gaban gwamna, gwamna ya kuma tambaye shi, “Kai sarkin Yahudawa ne?” Yesu ya amsa, “Haka ka fada.” 12Amma da manyan firistocin da dattawan suka zarge shi, bai ce komai ba. 13Sai Bilatus yace masa, “Baka ji dukan zarge-zargen da ake yi maka ba?” 14Amma bai ce masa ko kalma guda ba, sai gwamna yayi matukar mamaki. 15To lokacin bikin idi, al'adar gwamna ne ya saki mutum guda wanda jama'a suka zaba. 16A wannan lokacin suna da wani sanannen dan kurkuku mai suna Barabbas. 17To da suka tattaru, sai Bilatus yace masu, “Wa kuke so a sakar maku? Barabbas, ko Yesu wanda ake kira Almasihu?” 18Saboda ya san sun kawo shi ne domin kishi. 19Da yake zaune a kujerar shari'a, matarsa ta aika masa cewa, “Ka fita sha'anin mutumin nan marar laifi. Saboda na sha wahala sosai a yau cikin mafarki saboda shi.” 20A lokacin nan manyan firistoci da dattawa suka rinjayi ra'ayin jama'a suce a sakar masu da Barabbas, a kashe Yesu. 21Sai gwamna ya tambayesu, “Wa kuke so a sakar maku?” Sukace, “Barabbas.” 22Bilatus yace masu, “Me zan yi da Yesu wanda ake kira Almasihu?” Sai duka suka amsa, “A gicciye shi.” 23Sai yace, “Don me, wane laifi ya aikata?” Amma suka amsa da babbar murya, “A gicciye shi” 24Amma da Bilatus ya ga ba zai iya komai ba don hargitsi zai iya barkewa, ya dauki ruwa ya wanke hannuwansa a gaban jama'a, yace, “Ba ni da laifi ga jinin mutumin nan marar laifi. Ku yi abin da kuka ga dama.” 25Duka mutanen sukace, “Bari jininsa ya kasance a kan mu da 'ya'yan mu.” 26Sai ya sakar masu da Barabbas amma yayi wa Yesu bulala ya mika shi garesu domin su gicciye shi. 27Sai sojojin gwamna suka dauki Yesu zuwa farfajiya suka kuma tara dukan rundunar sojoji. 28Suka yi masa tumbur sa'annan suka sa masa jar alkyabba. 29Sai suka yi masa rawanin kaya suka sa a kansa, suka kuma bashi sanda a hannunsa na dama. Suka rusuna a gabansa suna masa ba'a, suna cewa, “Ranka ya dade, Sarkin Yahudawa!” 30Suka kuma tofa masa yawu, suka kwace sandar suka buga masa a ka. 31Bayan sun gama masa ba'a, suka cire masa alkyabbar suka sa masa kayansa, suka jagorance shi zuwa wurin da za a gicciye shi. 32Da suka fito waje, sai suka iske wani Bakurame mai suna Saminu, wanda suka tilasta ya tafi tare dasu domin ya dauki gicciyen. 33Suka iso wani wuri da ake kira Golgotta, wanda ke nufin,”Wurin kwalluwa.” 34Suka bashi ruwan inabi da aka gauraya da wani abu mai daci. Amma da ya 'dan-'dana shi sai ya ki sha. 35Bayan da suka gicciye shi, suka kada kuri'a a kan rigarsa. 36Suka kuma zauna suna kallonsa. 37A sama da kansa suka sa abinda ake tuhumarsa da ita a rubuce, “Wannan shine sarkin Yahudawa.” 38An gicciye shi da 'yanfashi guda biyu, daya ta damansa dayan kuma ta hagunsa. 39Wadanda suke wucewa suna zaginsa, suna girgiza kai, 40suna kuma cewa, “Kai da kace zaka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, ka ceci kanka mana! In dai kai Dan Allah ne, ka sauko daga gicciyen!” 41Ta haka ma manyan firistocin suka rika yi masa ba'a, tare da marubuta da shugabannin, suna cewa, 42“Ya ceci wasu amma ya kasa ceton kansa. Shi ne sarkin Isra'ila. Ya sauko mana daga kan gicciyen, sai mu ba da gaskiya gareshi. 43Tun da ya yarda da Allah. Bari Allahn ya cece shi mana, saboda yace, “Ni dan Allah ne.” 44Hakan nan ma 'yanfashin guda biyu da aka gicciye su tare suka zage shi. 45To tun da tsakar rana sai duhu ya rufe kasar gaba daya har karfe uku na yamma. 46Wajen karfe uku, Yesu ya tada murya mai karfi yace, “Eli, Eli lama sabaktani?” wanda ke nufin, “Allahna, Allahna, don me ka yashe ni?” 47Da wadanda suke tsaye kusa suka ji haka, sai sukace, “Yana kiran Iliya.” 48Nan take wani ya ruga da gudu ya dauki soso ya tsoma cikin ruwan inabi mai tsami ya soka kan sandar kara ya mika masa ya sha. 49Sai sauran sukace, “Rabu da shi mu gani ko Iliya zai zo ya cece shi.” 50Sai Yesu ya ta da murya mai karfi yayi kuka sai ya saki ruhunsa. 51Sai labullen haikali ya yage gida biyu daga sama zuwa kasa. Kasa kuma ta girgiza, duwatsu suka farfashe. 52Kaburbura suka bude, tsarkaka kuwa wadanda suke barci da yawa suka tashi. 53Suka fito daga kaburbura bayan tashinsa, suka shiga birni mai tsarki suka bayyana ga mutane da yawa. 54Da hafsan sojan da wadanda suke kallon Yesu suka ga girgizar kasar da abinda ya faru, suka ji tsoro kwarai sukace, “Hakika wannan Dan Allah ne” 55Mata dayawa da suka bi Yesu daga Galili domin su lura da shi suka tsaya suna kallo daga nesa. 56A cikin su akwai Maryamu Magadaliya, Maryamu uwar Yesu da Yusufu, da uwar 'ya'yan Zabadi. 57Da yamma sai wani attajiri mutumin Armatiya ya zo, mai suna Yusufu wanda shi ma almajirin Yesu ne. 58Ya je wurin Bilatus ya roka a bashi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a bashi. 59Yusufu ya dauki jikin, ya rufe shi da likafani mai tsabta, 60sai ya sa shi a cikin sabon kabarinsa da ya sassaka cikin dutse. Sai ya mirgina babban dutse a bakin kofar kabarin ya tafi. 61Maryamu Magadaliya da dayan Maryamun suna nan zaune akasin kabarin. 62Washegari, wato bayan ranar Shiri, Sai manyan firistoci da Farisawa suka taru tare da Bilatus. 63Sukace, “Mai gida, mun tuna lokacin da mayaudarin nan yake da rai, yace, “Bayan kwana uku zan tashi.” 64Saboda haka, ka bada umarni a tsare kabarin na kwana uku. In ba haka ba almajiransa zasu zo su sace shi, kuma su ce wa mutane, “Ya tashi daga mattatu.” Kuma yaudarar karshe zata fi ta farko muni.” 65Bilatus yace masu, “Ku dauki masu tsaro. Kuyi tsaro iyakar karfin ku.” 66Sai suka tafi suka tsare kabarin, suka hatimce dutsen, suka sa masu tsaro.

Você sabia?

Julgamento, cruz e sepultura

  • Pôncio Pilatos foi o sexto procurador romano da Judeia, de 26 a 36 d.C. Sua sede ficava em Cesareia, mas ele subia com frequência a Jerusalém, e seu governo abrangeu os ministérios de João Batista e de Jesus. Na festa, seguia um costume romano de soltar um prisioneiro: ofereceu à multidão a escolha entre Jesus e Barrabás, um ladrão notório cujo nome significa “filho de Abba” ou “filho de um pai”, e eles exigiram Barrabás.Fontes: Pontius Pilate · Barabbas · o próprio texto bíblico
  • Quando Judas viu que Jesus fora condenado, ficou cheio de remorso, lançou as trinta moedas de prata no templo, saiu e se enforcou. Os principais sacerdotes recusaram pôr o dinheiro de sangue no tesouro e, em vez disso, compraram o campo do oleiro como lugar de sepultura para estrangeiros. Em aramaico, os judeus o chamavam de Aceldama, “campo de sangue”; fica num terraço estreito e plano na face sul do vale de Hinom, e seu nome moderno é Hak ed-damm.Fontes: Judas Iscariot · Akeldama · o próprio texto bíblico
  • Jesus foi crucificado no Gólgota, grafia grega do aramaico Gulgaltha, o mesmo nome que Calvário e ligado à palavra hebraica para “crânio”. Os evangelistas explicam o lugar como “o lugar da caveira”, um pequeno outeiro arredondado como um crânio descoberto, um ponto conhecido fora da porta e perto da cidade.Fontes: Golgotha · o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Cyrene · 32.821, 21.851 · versículo 32
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 53
  • Galilee · 32.760, 35.527 · versículo 55

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.