Nations Bible

João 9

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Da Yesu yana wucewa, sai ya ga wani mutum makaho tun daga haihuwa. 2Sai almajiransa suka tambaye shi, “Mallam, wa yayi zunubi, mutumin ne ko iyayensa, har aka haife shi makaho?” 3Yesu ya amsa, Ba mutumin ne ko iyayensa suka yi zunubi ba, amma domin aikin Allah ya bayyana a cikinsa. 4Dole mu yi aikin wanda ya aiko ni tunda rana. Dare na zuwa inda ba mai iya yin aiki. 5Yayinda ina duniya, ni ne hasken duniya.” 6Bayan da Yesu ya fadi wadannan abubuwan, ya tofa yawu a kasa, ya kwaba kasar da yawunsa, sai ya shafe idanun mutumin da kasar. 7Ya ce masa, tafi, ka wanke a tafkin Siloam (ma'anarsa: aike).” Sai mutumin ya tafi, ya wanke, ya dawo yana gani. 8Sai makwabtansa da mutanen da da suka gan shi tun can yana roko suka ce, “ Ba wannan mutum ne wanda ya ke zaune yana roko ba?” 9Wadansu suka ce, “shi ne.” Wadansu suka ce, “A'a, amma yana kama da shi.” Amma shi ya ce, “Ni ne wannan mutum.” 10Suka ce masa, “ To yaya aka bude maka idanu?” 11Sai ya amsa, “Mutumin da ake ce da shi Yesu shi ya kwaba kasa ya shafa mani a idanuna ya ce mani, 'je ka kogin Siluwam ka wanke.' Sai naje na wanke, sannan na samu gani.” 12Suka ce masa, “Ina yake?” Ya amsa, “Ban sani ba.” 13Suka kawo mutumnin da yake makaho a da wurin farisawa. 14A ranar asabar ne kwa Yesu ya kwaba kasa ya bude masa idanu. 15Har yanzu farisawan suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Ya ce masu, “Ya sa mani kasa a idanuna, na wanke, kuma yanzu ina gani.” 16Wadansu daga cikin farisawa suka ce, “Wannan mutum ba daga Allah yake ba domin ba ya kiyaye ranar Asabar. “Wadansu suka ce, “Yaya mai zunubi zai yi irin wadannan alamu?” Sai rabuwa ta shiga tsakanin su. 17Sai suka tambayi makahon kuma, “Me kake cewa game da shi dashike ya bude maka idanu?” Makahon ya ce, “ shi annabi ne.” 18Har yanzu kam Yahudawan basu yarda da makantarsa ba da ganin gari da ya samu, sai da suka kirayo iyayen shi wanda ya sami ganin garin. 19Su ka tambayi iyayen, “Wannan shine yaronku da kuka ce an haife shi makaho? Yaya yanzu ya ke iya gani?” 20Sai iyayen suka amsa masu, “Mun san wannan yaronmu ne kuma a makaho aka haife shi. 21Yadda ya ke gani yanzu, bamu sani ba, kuma wanda ya bude masa idanu, bamu sani ba. Ku tambaye shi, ba yaro ba ne. Zai iya magana don kansa.” 22Iyayensa sun fadi wadannan abubuwan, domin suna ji tsoron Yahudawan. Gama Yahudiyawan sun rigaya sun yarda duk wanda yace Yesu Almasihu ne, za a fitar dashi daga majami'a. 23Domin wannan ne, iyayensa suka ce, “Ai shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi.” 24Suka sake kiran mutumin dake makaho karo na biyu, suka ce masa, “Ka girmama Allah. Mu kam mun sani wannan mutum mai zunubi ne.” 25Sai wannan mutum ya amsa, “ Ban sani ba ko shi mai zunubi ne. Abu guda daya na sani: da Ni makaho ne, amma yanzu ina gani.” 26Sai su ka ce masa, “Me ya yi maka? Ta yaya ya bude idanunka?” 27Ya amsa, “ Na rigaya na gaya maku, amma ba ku ji ba! Don me kuke so ku sake ji? Ko kuma kuna so ku zama almajiransa, haka ne? 28Sai suka kwabe shi suka ce, “kai ne almajirinsa, amma mu almajiran Musa ne. 29Mun sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum, bamu san ko daga ina ne ya zo ba.” 30Mutumin ya amsa masu ya ce, “ Tirkashi, baku san inda ya fito ba, duk da haka shi ya bude mani idanu. 31Mun san da cewa Allah baya jin masu zunubi, amma idan wani mai ibada ne yana kuma yin nufinsa, to yana jin sa. 32Tunda duniya ta fara ba a taba jin cewa wani ya bude idanun wanda aka haifa makaho ba. 33In mutumin nan ba daga Allah yake ba, ba zai iya yin komai ba.” 34Suka amsa suka ce masa, “an haife ka cikin zunubai, yanzu kana so ka yi mana koyarwa?” Sai suka fitar da shi. 35Yesu ya ji cewa sun fitar da shi daga majami'a. Da ya same shi sai ya ce masa, “Kana bada gaskiya ga Dan Allah?” 36Sai ya amsa masa yace, “Wanene shi, Ubangiji, da zan bada gaskiya gare shi?” 37Yesu yace masa, “Ai ka gan shi, shine wanda yake magana da kai.” 38Mutumin ya ce, “Ubangiji, Na bada gaskiya.” Sai ya yi masa sujada. 39Yesu ya ce, “ Don hukunci na zo wannan duniya domin wadanda ba su gani su gani, saboda kuma wadanda suke gani su zama makafi.” 40Wadansu Farisawa wadanda suke tare da shi suka ji wadannan abubuwan, suka tambaye shi, “Muma makafi ne?” 41Yesu ya ce masu, “ Inda ku makafi ne, da ba ku da zunubi, amma yanzu kun ce, 'Muna gani', don haka zunubinku ya tabbata.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

O homem cego de nascença

  • O tanque de Siloé, para onde Jesus mandou o homem lavar-se, é explicado na narrativa como significando Enviado; uma nota sobre o lugar também traduz o nome como Enviado ou envio. Essa nota identifica o tanque com Birket Silwan, no vale inferior do Tiropeon, a sudeste do monte Sião. A água chegava até ele de modo intermitente por um canal subterrâneo sinuoso de 1750 pés, embora a distância direta fosse de apenas 1100 pés, a partir da Fonte da Virgem, e o tanque media 53 pés de norte a sul, 18 pés de largura e 19 de profundidade.Fontes: Siloam · o próprio texto bíblico
  • Os discípulos de Jesus supunham que alguém havia pecado, o homem ou os pais dele, porque ele nascera cego. Jesus respondeu que nem um nem outros haviam pecado e que isso acontecera para que as obras de Deus se manifestassem nele. Mesmo depois, alguns dos que interrogavam o homem falaram dele como nascido em pleno pecado.Fontes: o próprio texto bíblico
  • O dia em que Jesus fez lama e abriu os olhos do homem era um sábado, e os fariseus ficaram divididos: alguns diziam que ele não vinha de Deus, porque não guardava o sábado, enquanto outros perguntavam como um homem pecador poderia realizar tais sinais. Os pais do homem tiveram medo de dizer como ele agora via, porque quem confessasse Jesus como o Cristo seria expulso da sinagoga. Uma cronologia do acontecimento situa a cura em 29 d.C. e lhe atribui a duração de um dia.Fontes: o próprio texto bíblico · Blind Man Healed

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Siloam · Hoje: Pool of Siloam · 31.771, 35.235 · versículos 7, 11

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.