Nations Bible

João 8

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Yesu ya je Dutsen Zaitun. 2Da sassafe ya dawo Haikali, dukan mutane kuma suka zo wurin sa; yazauna koya masu. 3Sai marubuta da Farisawa suka kawo mace wadda aka kama ta tana zina. Su ka sa ta a tsakiya. 4Sai su ka ce da shi, “Malam, wannan mace an kama ta tana cikin yin zina. 5A cikin shari'a, Musa ya bamu umurni mu jejjefe irin wandannan mutume, kai me ka ce game da ita?” 6Sun fadi haka ne domin su gwada shi su sami abinda za su zarge shi da shi, amma Yesu ya sunkuya yayi rubutu da yatsansa a kasa. 7Sa'adda suka cigaba da tambayar sa, ya mike tsaye yace masu, “shi wanda ba shi da zunubi a cikin ku, ya fara jifar ta da dutse.” 8Ya sake sunkuyawa, ya yi rubutu da yatsansa a kasa. 9Da suka ji haka, sai suka fita dai-dai da dai-dai, kama daga babbansu. A karshe dai aka bar Yesu shi kadai, tare da matar wadda ta ke a tsakiyar su. 10Yesu ya tashi tsaye ya ce da ita, “mace, ina masu zargin ki? Ba wanda ya kashe ki? 11Ta ce, “Ba kowa, Ubangiji” Yesu ya ce, “Ni ma ban kashe ki ba. Ki yi tafiyar ki, daga yanzu kada ki kara yin zunubi.” 12Yesu ya kara yin magana da mutanen cewa, “Ni ne hasken duniya, shi wanda ya biyo ni, ba zai yi tafiya cikin duhu ba, amma za ya sami hasken rai. 13Farisawa suka ce masa, “Kana bada shaida a kan ka, shaidarka ba gaskiya ba ce.” 14Yesu ya amsa ya ce masu, “Ko ma na bada shaida a kai na, shaidata gaskiya ce, na san daga inda na fito da inda zan tafi, amma ku baku san daga inda na fito ba, baku kuma san inda zan tafi ba. 15Kuna shari'a ta son kai, ni ko ban yi wa kowa shari'a ba. 16Ko ma da na yi shari'a, shari'ata gaskiya ce domin ba ni kadai ba ne, amma ina tare da Uba wanda ya aiko ni. 17I, a cikin dokarku an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce. 18Ni ne ni ke shaidar kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta. 19Su ka ce da shi, “Ina ubanka?” Yesu ya amsa ma su ya ce, “baku san ni ba balle Ubana, in da kun san ni da kun san Uba na kuma. “ 20Ya fadi wadannan kalmomi a kusa da wurin ajiya sa'adda ya ke koyarwa a cikin haikali, kuma ba wanda ya kama shi saboda sa'arsa bata yi ba tukuna. 21Ya kara cewa da su,”Zan tafi, za ku neme ni ba za ku same ni ba, za ku mutu cikin zunubinku. Inda ni ke tafiya, ba za ku iya zuwa ba”. 22Yahudawa su ka ce,”Zai kashe kansa ne, da ya ce inda ni ke tafiya ba za ku iya zuwa ba?” 23Yesu ya ce masu ku daga kasa kuke, Ni kuwa daga bisa ni ke. Ku na wannan duniya ne, Ni kuwa ba na wannan duniya ba ne. 24Shiyasa na ce maku za ku mutu cikin zunubanku. In ba kun bada gaskiya NI NE ba, za ku mutu cikin zunubanku. 25Sai kuma suka ce da shi,”Wanene kai?” Yesu ya ce masu, “Abin da na gaya maku tun daga farko. 26Ina da a bubuwa da yawa da zan gaya maku, in kuma hukunta ku a kai. Duk da haka, wanda ya aiko ni, mai gaskiya ne, abubuwan da naji daga wurin sa, wadannan abubuwan su ni ke gaya wa duniya.” 27Ba su gane ba yana yi masu magana a kan Uban. 28Yesu ya ce, “Sa'adda kuka tada Dan Mutum sama sa'annan za ku gane NI NE, kuma ban yi komi domin kaina ba. Kamar yadda Uba ya koya mani, haka nike fadin wadannan abubuwa. 29Shi wanda ya aiko ni, yana tare da ni kuma bai bar ni ni kadai ba, domin kullum ina yin abubuwan da suke faranta masa rai.” 30Sa'adda Yesu ya ke fadin wadannan abubuwa, dayawa suka bada gaskiya gare shi. 31Yesu ya gayawa wadancan Yahudawa da suka bada gaskiya gare shi, “Idan kun tsaya a cikin magana ta ku almajiraina ne na gaskiya, 32Kuma za ku san gaskiya, gaskiya kuwa zata 'yantar da ku.” 33Suka amsa masa, “ Mu zuriyar Ibrahim ne kuma bamu taba yin bauta wurin kowa ba, yaya za ka ce, 'Za a 'yantar da ku'?” 34Yesu ya ce masu, “Hakika, hakika, ina ce maku, dukan wanda ya ke aika zunubi bawan zunubi ne. 35Bawa kuwa, ba ya zama a gida dindindin, da yana zama dindindin. 36Saboda haka, idan Dan ya 'yantar da ku zaku zama 'yantattu sosai. 37Na san ku zuriyar Ibrahim ne, kuna so ku kashe ni saboda kalma ta bata da wurin zama a cikin ku. 38Na fadi abubuwan da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abubuwan da kuka ji daga wurin ubanku.” 39Suka amsa suka ce masa, “Ibrahim ne ubanmu” Yesu ya ce masu, “Da ku 'yayan Ibrahim ne da kun yi ayukan da Ibrahim ya yi. 40Amma, yanzu kuna so ku kashe ni, mutumin da ya gaya maku gaskiyar da ya ji daga wurin Allah. Ibrahim bai yi haka ba. 41Kuna yin ayyukan ubanku. Suka ce masa, “mu ba a haife mu cikin fasikanci ba, muna da Uba daya: Allah.” 42Yesu ya ce masu, “Inda Allah Ubanku ne, da kun kaunace ni, gama na zo daga wurin Allah kuma ga ni anan, gama ba domin kaina nazo ba, shine ya aiko ni. 43Meyasa baku gane magana ta ba? Ai saboda ba za ku iya jin maganata ba ne. 44Ku na ubanku, shaidan ne, kuma kuna so ku yi nufe-nufe na ubanku. Shi mai kisan kai ne tun daga farko kuma ba ya tsayawa gaskiya saboda da babu gaskiya a cikin sa. Sa'anda yake fadin karya, yana maganar halinsa ne domin shi dama makaryaci ne da uban karya kuma. 45Dayake ina fadin gaskiya baku bada gaskiya gare ni ba. 46Wanene a cikin ku ya kama ni da zunubi? Idan na fadi gaskiya don me ba ku gaskanta ni ba? 47Shi wanda yake na Allah ya kan ji maganar Allah, ku ba kwa jin maganar Allah da yake ku ba na Allah bane,” 48Yahudawa suka amsa suka ce masa, “Bamu fadi gaskiya ba da muka ce kai Basamariye ne kuma kana da aljan?” 49Yesu ya amsa, “Ni ba ni da aljan, ina girmama Ubana, ku kuma ba kwa girmama ni.” 50Ba na neman daraja domin kaina, akwai wanda ke nema yana kuma hukuntawa. 51Hakika, hakika, iIna ce maku, dukan wanda ya kiyaye maganata, ba za ya ga mutuwa ba.” 52Sai Yahudawa su ka ce masa, Yanzu mun sani kana da aljan. Ibrahim da annabawa sun mutu, amma kai ka ce, 'dukan wanda ya yi biyayya da maganata ba zai dandana mutuwa ba'. 53Ai baka fi ubanmu Ibrahim girma ba wanda ya mutu, ko ka fi shi? Annabawa kuma sun mutu. Wa kake daukar kanka ne?” 54Yesu ya amsa, “Idan na daukaka kaina, daukaka ta banza ce, Ubana ne ya daukaka ni. Wanda kuka ce shi ne Allahnku. 55Ku kuwa ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Idan na ce ban san shi ba, na zama kamar ku kenan, makaryaci. Sai dai, Ni na san shi ina kiyaye maganarsa. 56Ubanku Ibrahim ya yi farinciki da ganin rana ta; ya gan ta kuma ya yi murna.” 57Yahudawa su ka ce masa, “Baka kai shekara hamsin ba tukuna, ka taba ganin Ibrahim?” 58Yesu ya ce masu, “Hakika, hakika, ina ce maku, kafin a haifi Ibrahim, NI NE.” 59Suka dauki duwatsu za su jefe shi, amma Yesu ya boye kansa, ya fita daga haikali.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Luz, lei e Abraão

  • João 8 começa com Jesus indo ao monte das Oliveiras e voltando, de manhã cedo, aos pátios do templo, onde se senta e ensina o povo que se reúne. O monte das Oliveiras é uma serra a leste de Jerusalém, separada da cidade pelo vale do Cedrom, e recebe esse nome por causa das oliveiras que cobrem suas encostas.Fontes: o próprio texto bíblico · Mount of Olives
  • Escribas e fariseus trazem uma mulher surpreendida em adultério e perguntam a Jesus o que ele diz sobre a ordem de Moisés, na Lei, de apedrejar tal mulher, buscando pô-lo à prova e obter base para acusá-lo. Ainda nos pátios do templo, perto do tesouro, Jesus diz mais tarde: "Eu sou a luz do mundo". Uma lista datada de eventos situa os dois episódios em 29 d.C., cada um com duração de um dia.Fontes: o próprio texto bíblico · Woman Caught in Adultery · Light of the World/I am discourse
  • Quando Jesus diz que a verdade os libertará, seus ouvintes respondem que são descendentes de Abraão e que nunca foram escravos de ninguém. Abraão é chamado "pai de uma multidão"; era filho de Terá e herdeiro das promessas. Depois que Jesus declara "antes de Abraão nascer, eu sou", eles apanham pedras para atirar nele.Fontes: o próprio texto bíblico · Abraham

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Mount of Olives · 31.778, 35.246 · versículo 1

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.