Atos 24
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Bayan kwanaki biyar, sai Ananiyas babban firist, Wasu dattawa da wani masanin shari'a mai suna Tartilus, sun tafi can. Suka kai karar Bulus gaban gwamna. 2Lokacin da Bulus ya tsaya gaban gwamna, Tartilus ya fara zarginsa yace wa gwamnan, “Saboda kai mun sami zaman lafiya; sa'annan hangen gabanka ya kawo gyara a kasarmu; 3don haka duk abin da ka yi mun karba da godiya, ya mai girma Filikus. 4Domin kada in wahalsheka, ina roko a yi mani nasiha don in yi magana kadan. 5An iske mutumin nan yana barna irir iri, yana kuma zuga jama'ar Yahudawa a dukan duniya su yi tayarwa. 6Har ma ya yi kokarin kazantar da haikali; saboda haka muka kama shi. [Mun so mu shari'anta masa bisa ga dokarmu.] 7Amma Lisiyas jami'i ya zo ya kwace shi da karfi daga hannunmu. 8Idan ka binciki Bulus game da wadannan al'amura, kai ma, zai tabbatar maka abin da muke zarginsa a kai. 9Dukan Yahudawa suna zargin Bulus cewa wadannan abubuwa gaskiya ne. 10lokacin da gwamnan ya alamta wa Bulus ya yi magana sai yace, “Yanzu na fahimci cewar da dadewa kana mulkin kasarnan, don haka da farin ciki zan yi maka bayani. 11Zaka iya tabbatarwa cewa bai kai kwana sha biyu ba tun da nake zuwa Urushalima don yin sujada. 12Da suka same ni a haikali, ban yi jayayya ko kawo rudami a tsakanin jama'a ba. 13Don haka ba su da tabbas akan abinda suke zargina a kansa yau. 14Amma na sanar da kai, bisa ga abin da suke kira darika, haka ni ma nake bautawa Allah na kakanninmu. Na yi aminci wajen kiyaye dukan abin da ke a rubuce a Attaurat da litattafan annabawa. 15Ina sa bege ga Allah, kamar yadda za a yi tashin matattu, masu adalci da miyagu; 16a kan haka kuma, nake kokarin zama mara abin zargi a gaban Allah da mutane ina yin haka cikin dukan al'amura. 17Bayan wadansu shekaru na zo in kawo wasu sadakoki da baikon yardar rai. 18Cikin kudurin yin haka, sai wasu Yahudawa daga kasar Asiya suka iske ni a cikin ka'idodin tsarkakewa a haikali, ba da taro ko ta da hargitsi ba. 19Yakamata wadannan mutanen su zo gabarka a yau, har idan suna da wani zargi a kai na. 20In kuwa ba haka ba bari mutanennan su fada in sun taba iske ni da wani aibu a duk lokacin da na gurfana a gaban majalisar Yahudawa; 21sai dai ko a kan abu daya da na fada da babbar murya sa'adda na tsaya a gabansu, 'Wato batun tashin matattu wanda ake tuhumata ake neman yi mani hukunci yau.'” 22Filikus yana da cikakken sanin tafarkin Hanyar, shi yasa ya daga shari'ar. Yace da su, “Duk sa'anda Lisiyas mai ba da umarni ya zo daga Urushalima, zan yanke hukunci.” 23Sa'annan ya umarci jarumin ya lura da Bulus, amma ya yi sassauci, kada ya hana abokansa su ziyarce shi ko su taimake shi. 24Bayan wadansu kwanaki, Filikus da mai dakinsa Druskila, ita Bayahudiya ce, ya kuma aika a kira Bulus ya saurare shi game da bangaskiya cikin Kristi Yesu. 25Amma sa'adda Bulus yake bayyana zancen adalci, kamunkai, da hukunci mai zuwa, Filikus ya firgita ya ce, “Yanzu ka tafi. Amma idan na sami zarafi an jima, zan sake neman ka.” 26A wannan lokacin, yasa zuciya Bulus zai bashi kudi, yayi ta nemansa akai-akai domin yayi magana da shi. 27Bayan shekaru biyu, Borkiyas Festas ya zama gwamna bayan Filikus, domin neman farin jini a wurin Yahudawa, ya ci gaba da tsaron Bulus a gidan yari.

Você sabia?
Paulo perante Félix
- O sumo sacerdote Ananias desceu com alguns anciãos e um advogado chamado Tértulo, que o Dicionário Bíblico de Easton descreve como um advogado romano empregado pelos judeus para apresentar a causa contra Paulo diante de Félix. Tértulo elogiou o governador e depois chamou Paulo de peste, que provocava dissensão entre os judeus por todo o mundo, de chefe da seita dos nazarenos e de homem que tinha tentado profanar o templo. O dicionário liga esse elogio inicial à limpeza que Félix fez do país, expulsando bandidos e impostores.Fontes: o próprio texto bíblico · Tertullus · Felix
- Félix, que estava bem informado a respeito do Caminho, adiou a audiência e manteve Paulo sob guarda, permitindo-lhe alguma liberdade e deixando que amigos atendessem às suas necessidades. O relato diz que ele esperava que Paulo lhe oferecesse um suborno e por isso o mandava chamar com frequência; o Dicionário Bíblico de Easton também afirma que ele parece ter esperado um suborno e, por isso, teve várias conversas com ele. Depois de dois anos, Pórcio Festo o sucedeu — o Dicionário Bíblico de Easton (1897) data essa nomeação em 60 d.C. — e, querendo fazer um favor aos judeus, Félix deixou Paulo na prisão.Fontes: o próprio texto bíblico · Felix · Portius Festus
- Alguns dias depois, Félix voltou com sua mulher Drusila, que era judia, e ouviu Paulo falar da fé em Cristo Jesus e da justiça, do domínio próprio e do juízo vindouro; Félix ficou amedrontado e o mandou embora. O Dicionário Bíblico de Easton (1897) identifica Drusila como a terceira e mais nova filha de Herodes Agripa I e diz que Félix a induziu a deixar o marido, Azizus, rei de Emesa. O mesmo verbete diz que ela e o filho morreram na erupção do monte Vesúvio em 79 d.C.Fontes: o próprio texto bíblico · Drusilla
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Caesarea · Hoje: Caesarea Maritima · 32.500, 34.892 · versículo 1
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 11, 17
- Asia · 38.400, 28.300 · versículo 18
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org