Nations Bible

Atos 23

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Bulus ya kura wa yan majalisa ido yace, '''Yan'uwa, na yi rayuwa tare da Allah da lamiri mai kyau har wannan ranan.'' 2Babban firist Hannaniya ya ba wandanda suke tsaye tare da shi urmarni su buge bakinsa. 3Bulus ya ce, “Allah zai buge ka, kai munafiki. Kana zama domin ka shari'anta ni da shari'a, kuma ka umarce a buge ni, gaba da sharia?'' 4Wanda suka tsaya a gefe suka ce, ''Kada ka zage babban firis na Allah.'' Bulus yace, ''Ban sani ba, 'yan'uwa, cewa shi babban firis ne. 5Domin a rubuce yake, Ba za ku zargi shugaban mutanenku ba.'' 6Da Bulus ya ga cewa, daya bangaren Sadukiyawa ne dayan kuma Farisawa, ya yi magana da karfi a majalisa, '''Yan'uwa, ni Bafarise ne, dan Farisawa. Don tabbacin tashin matattu ne kuna shari'anta ni.'' 7Daya fadi haka, mahawara ta fara a tsakanin Farisawa da Sadukiyawa, sai taron ya rabu kashi biyu. 8Don Sadukiyawa suka ce babu tashin matattu, babu mala'iku, babu kuma ruhohi, amma Farisawa suka ce dukan abubuwan nan sun kasance. 9Sai mahawara ta tashi, wadansu marubutan Farisawa suka tashi da mahawara cewa, ''Ba mu same mutumin nan da laifi ba sam. Ko mala'iku da ruhohi ne suka yi masa magana?'' 10Da jayayya ta tashi, babban hafsa ya ji tsoro kada su yayaga Bulus, sai ya umarce sojoji suje su kwato shi da karfi daga 'yan majalisa, su tafi da shi farfajiya. 11Da dare Ubangiji ya tsaya kusa da shi yace, ''Kada ka ji tsoro, kamar yadda ka ba da shaida game da ni a Urushalima, dole zaka sake zama shaida a Roma.'' 12Da gari ya waye, wadansu Yahudawa sun yi yarjejeniya suka dauka wa kansu la'ana: suka ce ba za su ci ba ba za su sha ba sai sun kashe Bulus. 13Mutane fiye da arba'in suka kulla wannan makirci. 14Suka je wurin manyan firistoci da dattawa suka ce, ''Mun sa wa kanmu la'ana, ba za mu ci ba, ba za mu sha ba sai mun kashe Bulus. 15Yanzu, bari majalisa ta ba wa babban hafsa izini a kawo shi a gaba, kamar zai yanke hukunci. Mu kam, a shirye muke mu kashe shi kafin ya iso nan. 16Amma dan yar'uwan Bulus ya ji suna labe, sai ya tafi ya shiga farfajiyar ya fada wa Bulus. 17Bulus ya kira daya daga cikin jarumai yace, ''Dauki saurayin nan ka kai shi wurin babban hafsa, don yana da abin da zai fada masa.'' 18Jarumin ya dauke saurayin ya kai shi wurin babban hafsa yace, ''Bulus dan sarka ne yace in kawo saurayin nan a gaban ka. Yana da abin da zai fada maka.'' 19Babban hafsa ya kai shi wani lungu, sai ya tambaye shi, “Menene kake so ka fada mani?'' 20Saurayin yace, ''Yahudawa sun yarda su roke ka ka kawo Bulus gobe a majalisa, kamar zasu kara bincike a kan al'amarin. 21Amma kada ka yarda da su, mutane fiye da arba'in suna jiransa. Sun sa wa kansu la'anna, ba za su ci ba ba za su sha ba sai dai sun kashe shi. Yanzu a shirye suke; suna jira ka ba su izini.'' 22Sai babban hafsa yace wa saurayin ya tafi, da ya gama masa magana, ''Kar ka fada wa wani al'amuran.'' 23Sai ya kira jarumai biyu yace, ''Ku shirya sojoji dari biyu, yan dawakai saba'in, masu daukar mashi dari biyu su tafi kaisariya karfe uku na dare.'' 24Ya umarta a shirya dabbobin da Bulus zai hawo da zasu kai shi lafiya wurin Filikus gwamna. 25Sai ya rubuta wasika a misalin haka: 26Gaisuwa zuwa Kuludiyas Lisiyas zuwa ga mai martaba gwamna Filikus. 27Yahudawa sun kama wannan mutumin suna shirin kashe shi, na abko masu da sojoji na kwace shi, bayan da na ji shi Barome ne. 28Inna son sani dalilin zarginsa, sai na kai shi majalisa. 29Na gane cewa ana zarginsa ne a kan tambayoyi game da shari'ansu, amma ba wani zargi da ya cancanci dauri ko mutuwa. 30Da aka sanar da ni shirin makircin, sai na tura shi wurinka ba da bata lokaci ba, na umarce masu zarginsa su kawo zarginsu wurinka. Huta lafiya.” 31Sai sojoji suka yi biyayya da umarni da aka basu: suka dauki Bulus suka kawo shi dadare a wurin Antibatris. 32Da gari ya yawe, yan dawakai suka tafi tare da shi kuma sauran sojoji suka koma farfajiya. 33Bayan da yandawakan suka isa Kaisiririya sun mika wasika ga gwamna, suka kuma danka Bulus a hanunsa. 34Da gwamna ya karanta wasikar, sai ya tambaye su daga wani yanki ne Bulus ya fito; da ya ji daga yankin kilikiya ne, 35Yace zan saurare ka sosai lokacin da masu zargin ka sun zo. Sai ya umarta a tsare shi a fadar Hiridus.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Paulo diante do Sinédrio e a caminho de Cesareia

  • Ananias era o sumo sacerdote perante quem Paulo foi levado enquanto Félix era procurador. Depois que Paulo disse que se havia conduzido diante de Deus com toda a boa consciência, Ananias ordenou aos que estavam por perto que o ferissem na boca; Paulo chamou-o de parede branqueada e, quando protestaram que ele havia insultado o sumo sacerdote de Deus, respondeu que não sabia que Ananias ocupava esse cargo. O Easton's Bible Dictionary (1897) observa que essa resposta tem ocasionado certa dificuldade.Fontes: Ananias (High Priest) · o próprio texto bíblico
  • Mais de quarenta homens se comprometeram sob juramento a não comer nem beber até que matassem Paulo, e soldados o levaram de noite de Jerusalém até Antipátride. Antipátride, construída por Herodes, o Grande, e nomeada em honra de seu pai Antipater, ficava na grande estrada romana de Cesareia a Jerusalém, a cerca de vinte e oito milhas de Cesareia. Cesareia, na costa do Mediterrâneo, a cerca de setenta milhas a noroeste de Jerusalém, era a capital da província romana da Judeia e a sede dos procuradores.Fontes: o próprio texto bíblico · Antipatris · Caesarea
  • Cláudio Lísias, descrito pelo Easton's Bible Dictionary como um grego que havia comprado a cidadania romana e tomado o nome de Cláudio, escreveu ao governador Félix que as acusações envolviam questões da lei judaica e que não havia acusação digna de morte ou prisão. Félix, o procurador romano da Judeia, perguntou de que província Paulo era; ao saber que era da Cilícia, onde Tarso, cidade natal de Paulo, era uma das principais cidades, ordenou que Paulo fosse mantido sob guarda no Pretório de Herodes até que os acusadores chegassem.Fontes: Claudius Lysias · Felix · Cilicia · o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 11
  • Rome · 41.892, 12.485 · versículo 11
  • Caesarea · Hoje: Caesarea Maritima · 32.500, 34.892 · versículos 23, 32, 33
  • Aphek · Hoje: Tell Ras el Ain · 32.105, 34.930 · versículo 31
  • Cilicia · 36.913, 34.892 · versículo 34

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.