1 João 5
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Duk Wanda ya gaskata Yesu shine Almasihu haifaffe na Allah ne. Kuma duk wanda ya kaunaci uba ya kaunaci dan da uban ya haifa. 2Haka muka sani muna kaunar 'ya'yan Allah: yayin da muka kaunaci Allah, kuma muka aikata umarninsa. 3Wannan itace kaunar Allah, cewa mu kiyaye umarninsa. Domin umarninsa ba masu nawaitawa bane. 4Duk wanda yake haifaffe na Allah yakan yi nasara da duniya. Wannan itace nasarar da ta rinjayi duniya, wato bangaskiyarmu. 5Wanene wannan mai nasara da duniya? Sai dai wanda ya gaskata Yesu Dan Allah ne. 6Wannan shine wanda yazo ta wurin ruwa da jini: Yesu Almasihu. Ya zo ba ta wurin ruwa kadai ba, amma ta wurin ruwa da jini. 7Domin akwai uku wadanda suke bada shaida: 8Ruhu, da ruwa, da kuma jini. Wadannan ukun kuwa manufarsu daya ce. 9Idan mun karbi shaidar mutane, shaidar Allah ta fi girma. Wannan ita ce shaidar Allah, wato ya bada shaida akan Dansa. 10Wanda ya gaskata da Dan Allah shaidar tana nan tare da shi. Duk wanda bai bada gaskiya ga Allah ba, ya mai da shi makaryaci kenan, domin bai gaskata da shaidar da Allah ya bayar game da Dansa ba. 11Wannan ita ce shaida: Allah ya bamu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Dansa. 12Duk wanda yake da Dan, yana da rai. Duk wanda ba shida Dan Allah kuwa bashi da rai. 13Na rubuto maku wannan ne don ku tabbata kuna da rai madawwami—a gare ku wadanda suka gaskata da sunan Dan Allah. 14Wannan shine gabagadin da muke da shi a gabansa, wato, in mun roki kome bisa ga nufinsa, zai ji mu. 15Haka kuma, in mun san yana jinmu—Duk abin da mu ka rokeshi—mun sani muna da duk abin da muka roka daga gare shi. 16Idan wani ya ga dan'uwansa ya yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yayi masa addu'a, Allah kuwa zai ba shi rai. Ina nufin wadanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yake kai wa ga mutuwa: Ban ce a yi addu'a domin wannan ba. 17Dukkan rashin adalci, zunubi ne, amma akwai zunubin da bai kai ga mutuwa ba. 18Mun sani kowanne haiffafe daga wurin Allah ba ya yin zunubi. Amma wanda ke haifaffe daga wurin Allah, ya kan kare shi, mugun nan kuwa ba zai iya yi masa illa ba. 19Mun sani mu na Allah ne, mun kuma sani dukkan duniya tana hannun mugun nan. 20Amma mun sani Dan Allah yazo, kuma ya bamu fahimta, domin mu san wanda yake shi ne mai gaskiya. Haka kuma muna cikin wannan wanda shine gaiskiya, kuma cikin Dansa Yesu Almasihu. Shine Allah na gaskiya, da kuma rai na har abada. 21'Ya'ya, ku tsare kanku daga bautar gumaka.

Você sabia?
Fé, testemunho e vida
- Este capítulo diz que todo aquele que crê que Jesus é o Cristo é nascido de Deus, e que amar o Pai também significa amar os que nasceram dele. Descreve o amor a Deus como guardar os seus mandamentos, que não são pesados, porque todo aquele que nasceu de Deus vence o mundo, e chama essa vitória de fé em Jesus como Filho de Deus.Fontes: o próprio texto bíblico
- Jesus Cristo é apresentado como quem veio pela água e pelo sangue, não somente pela água, e o Espírito é quem testifica isso, porque o Espírito é a verdade; o capítulo não explica aqui o que são a água e o sangue. Apresenta o Espírito, a água e o sangue como três que testificam em acordo, e chama o testemunho de Deus acerca do seu Filho de maior que o testemunho humano: Deus nos deu a vida eterna, e essa vida está no seu Filho. O autor diz que escreveu essas coisas para que os que creem no nome do Filho de Deus saibam que têm a vida eterna.Fontes: o próprio texto bíblico
- Os leitores são orientados a pedir a Deus por um irmão que comete um pecado que não leva à morte, enquanto o autor diz que não está dizendo que peçam a respeito de um pecado que leva à morte. Ele não nomeia nenhum dos dois pecados, embora diga que toda injustiça é pecado e que há pecado que não leva à morte. O capítulo termina dizendo aos filhinhos que se guardem dos ídolos.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org