Nations Bible

1 João 4

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Kaunatattu, kada ku amince da kowanne ruhu. Amma ku gwada ruhohi ku gani ko na Allah ne, gama annabawan karya masu yawa sun fito zuwa cikin duniya. 2Ta haka zaku gane Ruhun Allah, dukkan ruhun da ya amince Yesu Almasihu ya zo cikin jiki na Allah ne, 3kuma dukkan ruhun da bai amince da Yesu ba, ba na Allah bane. Wannan ruhun magafcin Almasihu ne, wanda kuka ji cewa yana zuwa, ya kuwa rigaya yazo cikin duniya. 4'Ya'yana kaunatattu, daga Allah ke, kuma kun rigaya kun yi nasara da su da yake wanda ke cikinku ya fi wanda ke cikin duniya girma. 5Su na duniya ne, saboda haka abin da suke fadi na duniya ne, duniya kuma tana sauraronsu. 6Mu na Allah ne, duk wanda ya san Allah yana saurarenmu. Wanda ba na Allah bane, ba ya sauraronmu. Ta haka muka gane ruhun gaskiya da ruhun karya. 7Kaunatattu, mu yi kaunar juna, gama kauna ta Allah ce, wanda yake kauna an haife shi daga wurin Allah, kuma ya san Allah. 8Mutumin da baya kauna ba na Allah ba ne, kuma bai san Allah ba, gama Allah kauna ne. 9A cikn haka aka bayyana kaunar Allah a garemu, Allah ya aiko tilon Dansa cikin duniya domin mu rayu ta wurinsa. 10A cikin wannan akwai kauna, ba mune muka kaunaci Allah ba, amma shi ya kaunace mu ya aiko da Dansa ya zama mai gafarta zunubanmu. 11Kaunatattu, da yake Allah ya kaunace mu haka, ya kamata mu kaunaci junanmu. 12Ba wanda ya taba ganin Allah. Idan muna kaunar juna, Allah yana zaune cikinmu, kuma kaunarsa tana zaune a cikinmu. 13Ta haka mun sani muna zaune a cikinsa shi kuma a cikinmu, saboda ya bamu Ruhunsa. 14Mun gani mun shaida, cewa Allah ya aiko Dan, domin ya zama mai ceton duniya. 15Duk wanda ya amince Yesu Dan Allah ne, Allah na zaune cikinsa, shi kuma a cikin Allah. 16Mun sani kuma mun gaskata da kaunar da Allah yake da ita dominmu, Allah kauna ne wanda yake zama cikin kauna yana zaune cikin Allah, Allah kuma a cikinsa. 17Dalilin wannan kauna ta kammala a cikinmu, domin mu kasance da gabagadi a ranar shari'a, domin kamar yanda ya ke haka muma muke a cikin duniyan nan. 18Babu tsoro a cikin kauna. Amma cikkakiyar kauna takan kawar da tsoro, domin kuwa tsoro na tafi tare da hukunci. Amma wanda yake da tsoro ba shi da cikkakiyar kauna. 19Muna kauna domin Allah ne ya fara kaunarmu. 20Idan wani ya ce,”Ina kaunar Allah”, amma yana kin dan'uwansa, makaryaci ne. Domin wanda baya kaunar dan'uwansa da yake gani, ba zai iya kaunar Allah da bai taba gani ba. 21Wannan ne umarnin da muke da shi daga wurinsa: Duk wanda yake kaunar Allah dole ne ya kaunaci dan'uwansa.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Provando os espíritos e o amor que vem de Deus

  • Aos leitores tratados como amados se diz que não creiam em todo espírito, mas que provem os espíritos, pois muitos falsos profetas têm saído pelo mundo. O Espírito de Deus é reconhecido quando um espírito confessa que Jesus Cristo veio em carne; todo espírito que não confessa Jesus não é de Deus e é o espírito do anticristo, que já está no mundo.Fontes: o próprio texto bíblico
  • O amor vem de Deus, e Deus é amor, de modo que quem não ama não conhece a Deus. O amor de Deus foi revelado ao enviar seu Filho único ao mundo como sacrifício expiatório pelos pecados, e aos que foram assim amados se diz que devem amar uns aos outros.Fontes: o próprio texto bíblico
  • Ninguém jamais viu a Deus, mas se amamos uns aos outros, Deus permanece em nós e o seu amor é aperfeiçoado em nós. Quem diz “Eu amo a Deus”, mas odeia seu irmão, é mentiroso, pois quem não ama seu irmão, a quem viu, não pode amar a Deus, a quem não viu, e o mandamento é que quem ama a Deus também ame seu irmão.Fontes: o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.