1 Coríntios 4
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Ga yadda za ku dauke mu, kamar bayin Almasihu da kuma masu rikon asiran Allah. 2Hade da wannan, ana bukatar wakilai su zama amintattu. 3Amma a gare ni, karamin abu ne ku yi mani shari'a, ko a wata kotu irin ta mutane. Gama bani yi wa kaina shari'a. 4Ban sani ko akwai wani zargi a kaina ba, amma wannan bai nuna cewa bani da laifi ba. Ubangiji ne mai yi mani shari'a. 5Sabili da haka, kada ku yanke shari'a kafin lokaci, kafin Ubangiji ya dawo. Zai bayyana dukkan boyayyun ayyuka na duhu, ya kuma tona nufe-nufen zuciya. San nan kowa zai samu yabonsa daga wurin Allah. 6Yan'uwa, ina dora wadannan ka'idoji a kaina da Afollos domin ku, yadda ta wurin mu za ku koyi ma'anar maganar nan cewa, “kada ku zarce abin da aka rubuta.” Ya zama haka domin kada waninku ya kumbura yana nuna fifiko ga wani akan wani. 7Gama wa yaga bambanci tsakanin ku da wasu? Me kuke da shi da ba kyauta kuka karba ba? Idan kyauta kuka karba, don me kuke fahariya kamar ba haka ba ne? 8Kun rigaya kun sami dukkan abubuwan da kuke bukata! Kun rigaya kun zama mawadata! Kun rigaya kun fara mulki- kuma ba tare da mu ba! Hakika, marmarina shine ku yi mulki, domin mu yi mulki tare da ku. 9A tunanina, mu manzanni, Allah ya sa mu a jerin karshe kamar mutanen da aka zartar wa hukuncin mutuwa. Mun zama abin kallo ga duniya, ga mala'iku, ga mutane kuma. 10Mun zama marasa wayo sabili da Almasihu, amma ku masu hikima ne a cikin Almasihu. Mu raunana ne, amma ku masu karfi ne. Ana ganin mu marasa daraja, ku kuwa masu daraja. 11Har zuwa wannan sa'a, muna masu yunwa da kishi, marasa tufafi masu kyau, mun sha kazamin duka, kuma mun zama marasa gidaje. 12Mun yi fama sosai, muna aiki da hanuwanmu. Sa'adda an aibata mu, muna sa albarka. Sa'adda an tsananta mana, muna jurewa. 13Sa'adda an zage mu, muna magana da nasiha. Mun zama, kuma har yanzu an dauke mu a matsayin kayan shara na duniya da abubuwa mafi kazamta duka. 14Ban rubuta wadannan abubuwa domin in kunyata ku ba, amma domin in yi maku gyara kamar kaunatattun yayana. 15Ko da kuna da masu riko dubu goma a cikin Almasihu, ba ku da ubanni da yawa. Gama ni na zama ubanku cikin Almasihu Yesu ta wurin bishara. 16Don haka, ina kira gare ku da ku zama masu koyi da ni. 17Shiyasa na aiko Timoti wurin ku, kaunatacce da amintaccen dana cikin Ubangiji. Zai tunashe ku hanyoyina cikin Almasihu, kamar yadda nake koyar da su ko'ina da kowace Ikilisiya. 18Amma yanzu, wadansun ku sun zama masu fahariya, suna yin kamar ba zan zo wurinku ba. 19Amma zan zo gare ku ba da dadewa ba, idan Ubangiji ya nufa. Sannan zan san fiye da maganar masu fahariya, amma kuma zan ga ikonsu. 20Gama Mulkin Allah ba magana kadai ya kunsa ba, amma ya kunshi iko. 21Me kuke so? In zo wurin ku da sanda ne ko kuwa da kauna da ruhun nasiha?

Você sabia?
Servos, despenseiros e a advertência de um pai
- Paulo aplica estas coisas a si mesmo e a Apolo, para que os coríntios aprendam a não se orgulhar de um homem em detrimento de outro. Apolo, judeu nascido em Alexandria, eloquente e versado nas Escrituras, seguiu para Corinto, onde regou a semente que Paulo havia semeado, e seus discípulos ali se apegaram muito a ele. Um breve relato de sua vida o situa com Paulo em Éfeso quando foi escrita a primeira carta aos Coríntios.Fontes: o próprio texto bíblico · Apollos
- Paulo diz que os coríntios já têm tudo o que querem, enriqueceram e se tornaram reis sem ele e seus companheiros, e deseja que eles realmente fossem reis, para que ele e seus companheiros fossem reis com eles. Escreve que lhe parece que Deus exibiu os apóstolos no fim do cortejo, como prisioneiros destinados à morte, um espetáculo para o mundo inteiro, para os anjos e também para os homens, enquanto passam fome e sede, malvestidos, sem lar e trabalhando arduamente com as próprias mãos.Fontes: o próprio texto bíblico
- Paulo diz que enviou Timóteo, seu filho amado e fiel no Senhor, para lembrar aos coríntios o seu modo de vida em Cristo Jesus, o mesmo ensino que ele transmite em toda parte, em cada igreja. Timóteo, nome que significa honrando a Deus, era um jovem discípulo que acompanhou Paulo em muitas de suas viagens, e Paulo o chamava de seu próprio filho na fé. Esse relato nada diz do pai de Timóteo, senão que era grego, e nomeia sua mãe como Eunice e sua avó como Lóide.Fontes: o próprio texto bíblico · Timotheus
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org