1 Coríntios 3
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Amma ni, yan'uwa, ba zan iya magana da ku kamar mutane masu ruhaniya ba, amma kamar mutane masu jiki, kamar jarirai cikin Almasihu. 2Na shayar da ku da Madara ba da nama ba, don baku isa cin nama ba, kuma ko yanzu ma baku isa ba. 3Gama har yanzu ku masu jiki ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu jiki ba ne, kuma kuna tafiya bisa magwajin mutane? 4Domin in wani ya ce, “Ina bayan Bulus,” wani kuma ya ce, “Ina bayan Afollos,” ashe, ba zaman mutuntaka kuke yi ba? 5To wanene Afollos? Wanene kuma Bulus? Bayi ne wadanda kuka bada gaskiya ta wurin su, kowannen su kuwa Allah ya bashi ayyuka. 6Ni nayi shuka, Afolos yayi banruwa, amma Allah ne ya sa girma. 7Don haka, da mai shukar da mai banruwan, ba komi bane. Amma Allah ne mai sa girman. 8Da mai shukar, da mai banruwan, duk daya suke, kuma kowannen su zai sami nasa lada, gwargwadon aikinsa. 9Gama mu abokan aiki ne na Allah. Ku gonar Allah ne, ginin Allah kuma. 10Bisa ga alherin Allah da aka bani a matsayin gwanin magini, na kafa harsashi, wani kuma yana dora gini a kai. Sai dai kowane mutum, ya lura da yadda yake dora ginin. 11Gama ba wanda ke iya kafa wani harsashin daban da wanda aka rigaya aka kafa, wato, Yesu Almasihu. 12Yanzu fa in wani ya dora gini a kan harashin da zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ciyawa, ko tattaka, 13aikinsa zai bayyanu, domin ranar nan zata tona shi. Gama za a bayyana shi cikin wuta. Wutar kuwa zata gwada ingancin aikin da kowa ya yi. 14Duk wanda aikinsa ya tsaya, zai karbi lada; 15amma duk wanda aikinsa ya kone, zai sha Asara, amma shi kansa zai tsira, sai dai kamar ta tsakiyar wuta. 16Ashe, baku san ku haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikin ku? 17Idan wani ya lalata haikalin Allah, Allah zai lalata shi. Gama haikalin Allah mai tsarki ne, kuma haka ku ke. 18Kada kowa ya rudi kansa. Idan wani a cikin ku na ganin shi mai hikima ne a wannan zamani, bari ya zama” wawa” domin ya zama mai hikima. 19Gama hikimar duniyar nan wauta ce a gun Allah. Gama a rubuce yake, “Yakan kama masu hikima a cin makircin su.” 20Har wa yau, “Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne.” 21haka ba sauran fariya akan mutane! Domin kuwa kome naku ne, 22Ko Bulus, ko Afollos, ko kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwa na yanzu, ko abubuwa masu zuwa. Duka naku ne, 23Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.

Você sabia?
Mestres rivais e o campo de Deus
- As frases “Eu sou de Paulo” e “Eu sou de Apolo” se referem a dois mestres que os coríntios conheciam. Apolo, um judeu de Alexandria descrito como eloquente e versado nas Escrituras, foi a Corinto depois que Áquila e Priscila o instruíram mais a fundo, e seus seguidores se apegaram muito a ele.Fontes: o próprio texto bíblico · Apollos
- Paulo transforma o trabalho dos dois numa imagem compartilhada: ele plantou a semente, Apolo a regou, e Deus a fez crescer. Chama-os de servos por meio dos quais os coríntios creram e de cooperadores com um só propósito, cada um recompensado segundo o próprio trabalho.Fontes: o próprio texto bíblico · Apollos
- Uma nota biográfica tradicional diz que Apolo estava com Paulo em Éfeso quando esta carta foi escrita. Paulo ainda fala dos dois como servos e diz aos coríntios que parem de se gloriar nos homens — Paulo, Apolo ou Cefas —, porque os coríntios pertencem a Cristo, e Cristo pertence a Deus.Fontes: Apollos · o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org