Jeremias 26
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
An yi wa Irmiya barazanar mutuwa
1A farkon sarautar Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo daga wurin Ubangiji, 2“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka tsaya a filin gidan Ubangiji ka kuma yi magana ga dukan mutanen garuruwan Yahuda waɗanda suka zo sujada a gidan Ubangiji. Ka faɗa musu kome da na umarce ka; kada ka bar wata magana. 3Wataƙila su saurara kowanne kuma ya juyo daga mugun hanyarsa. Sa’an nan in yi juyayi in kuma janye masifar da nake shirin kawo a kansu saboda muguntar da suka aikata. 4Ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, in ba ku saurare ni, ku kuma bi dokata, wadda na sa a gabanku ba, 5in kuma ba ku saurari maganganun bayina annabawa, waɗanda na aika muku sau da sau ba (ko da yake ba ku saurara ba), 6to, sai in mai da gidan nan kamar Shilo, birnin nan kuma abin la’ana a cikin al’umman duniya.’ ”
7Firistoci, annabawa da dukan mutane suka ji Irmiya yana waɗannan maganganu a gidan Ubangiji. 8Amma da Irmiya ya gama faɗar wa dukan mutanen abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa, sai firistoci, annabawa da dukan mutane suka kama shi suka ce, “Mutuwa za ka yi! 9Me ya sa ka yi annabci da sunan Ubangiji cewa wannan gida zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kango da hamada?” Sai duk mutane suka tattaru kewaye da Irmiya a cikin gidan Ubangiji.
10Da fadawan Yahuda suka ji haka, sai suka haura daga fada zuwa gidan Ubangiji suka zazzauna a wuraren zamansu a mashigin Sabuwar Ƙofar gidan Ubangiji. 11Sa’an nan firistoci da annabawa suka ce wa fadawan da dukan mutane, “Mutumin nan ya cancanci hukuncin kisa gama ya yi annabci gāba da wannan birni. Ku kun ji da kunnuwanku!”
12Sai Irmiya ya ce wa dukan fadawa da kuma dukan mutane, “ Ubangiji ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan gida da wannan birni dukan abin da na faɗa. 13Yanzu sai ku gyara hanyoyinku da kuma ayyukanku ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku. Sa’an nan Ubangiji zai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kanku. 14Game da ni dai, ina a hannuwanku; ku yi duk abin da kuka ga ya yi kyau, ya kuma dace a gare ku. 15Ku tabbata dai, cewa in kuka kashe ni, za ku jawo wa kanku alhakin jini marar laifi a kanku da a kan birnin nan da kuma a kan masu zama a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.”
16Sai fadawa da dukan mutane suka ce wa firistoci da annabawa. “Wannan mutum bai yi abin da ya isa hukuncin kisa ba, gama ya yi magana da sunan Ubangiji Allahnmu.”
17Waɗansu daga cikin dattawan ƙasar suka zo gaba suka ce wa dukan taron jama’a, 18“Mika mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya sarkin Yahuda. Ya ce wa dukan mutanen Yahuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“ ‘Za a nome Sihiyona kamar gona,
Urushalima kuwa za tă zama tsibin juji,
ƙwanƙolin dutsen haikali kuwa zai zama kurmi.’
19“Hezekiya sarkin Yahuda ko kuwa wani a Yahuda ya kashe shi? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji ya nemi tagomashinsa ba? Ubangiji kuwa bai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kansu ba? Muna gab da jawo wa kanmu muguwar masifa!”
20(To, fa, Uriya ɗan Shemahiya daga Kiriyat Yeyarim wani mutum ne wanda ya yi annabci da sunan Ubangiji; ya yi annabci irin abu ɗaya gāba da wannan birni da wannan ƙasa yadda Irmiya ya yi. 21Da sarki Yehohiyakim da dukan fadawansa da ma’aikatansa suka ji wannan magana, sai sarki ya nemi a kashe shi. Amma Uriya ya ji wannan shiri sai ya gudu zuwa Masar don tsoro. 22Sarki Yehohiyakim ya aiki Elnatan ɗan Akbor zuwa Masar, tare da waɗansu mutane. 23Suka dawo da Uriya daga Masar suka kawo shi wurin Sarki Yehohiyakim, wanda ya kashe shi da takobi aka kuma jefar da gawarsa a makabartar talakawa.)
24Bugu da ƙari, Ahikam ɗan Shafan ya goyi bayan Irmiya, saboda haka ba a ba da shi ga mutane don su kashe shi ba.

Você sabia?
O julgamento de Jeremias e os precedentes
- Quando sacerdotes e profetas exigiram a execução de Jeremias por profetizar a destruição do templo, alguns anciãos citaram o precedente de Miqueias de Moresete, ocorrido mais de um século antes. Durante o reinado do rei Ezequias, Miqueias havia proferido uma advertência semelhante contra Jerusalém, mas o rei buscou o favor do Senhor em vez de condená-lo à morte.Fontes: o próprio texto bíblico · Micah · Hezekiah
- O relato evidencia o perigo enfrentado por Jeremias ao contrastar seu caso com o de Urias, filho de Semaías, que proclamou a mesma mensagem. Ao ser perseguido por Joaquim, Urias fugiu para o Egito, mas o rei enviou oficiais para extraditá-lo, mandou executá-lo à espada e jogou seu corpo nas sepulturas do povo comum.Fontes: o próprio texto bíblico · Urijah · Jehoiakim
- Jeremias conseguiu escapar da morte em grande parte devido à proteção de Aicão, filho de Safã, um nobre influente cuja família havia auxiliado o rei Josias em suas reformas religiosas.Fontes: o próprio texto bíblico · Ahikam
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 6, 9, 18
- Shiloh · Hoje: Khirbet Seilun · 32.056, 35.290 · versículos 6, 9
- New Gate · Hoje: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 10
- Mount Zion · 31.772, 35.229 · versículo 18
- Zion · Hoje: Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 18
- Kiriath-jearim · Hoje: Deir el Azar · 31.809, 35.104 · versículo 20
- Egypt · 30.129, 31.308 · versículos 21, 22, 23
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org