Nations Bible

Jeremias 25

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

Shekaru saba’in na zaman bauta

1Magana ta zo wa Irmiya game da dukan mutanen Yahuda a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wadda ta kasance shekara ta fari ta Nebukadnezzar sarkin Babilon. 2Saboda haka Irmiya annabi ya ce wa dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima. 3Shekaru ashirin da uku, daga shekara ta goma sha uku ta Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda har zuwa wannan rana, maganar Ubangiji ta zo mini na kuma yi muku magana sau da sau, amma ba ku saurara ba.

4Ko da yake Ubangiji ya aika dukan bayinsa annabawa gare ku sau da sau, ba ku saurara ba, ba ku kuma kula ba. 5Sun ce, “Ku juye yanzu, kowannenku, daga mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku, za ku kuwa iya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku da kuma kakanninku har abada abadin. 6Kada ku bi waɗansu alloli don ku bauta ku kuma yi musu sujada; kada ku tsokane ni in yi fushi da abin da hannuwanku suka yi. Sa’an nan ba zan kawo muku lahani ba.”

7“Amma ba ku saurare ni ba,” in ji Ubangiji, “kun tsokane ni da abin da kuka yi da hannuwanku, kuka kuma kawo lahani wa kanku.”

8Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Domin kun ƙi ku saurara ga maganata, 9zan kira dukan mutanen arewa da bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon,” in ji Ubangiji, “zan kuma kawo su su yi gāba da wannan ƙasa da mazaunanta da kuma gāba da dukan al’ummai da suke kewaye. Zan hallaka su sarai in kuma mai da su abin bantsoro da abin dariya, za su kuma zama kufai har abada. 10Zan kawar da muryoyin farin ciki da murna daga gare su, muryoyin amarya da na ango, ƙarar dutsen niƙa da hasken fitila. 11Dukan wannan ƙasa za tă zama kango, kuma waɗannan al’ummai za su bauta wa sarkin Babilon shekaru saba’in.

12“Amma sa’ad da shekaru saba’in ɗin suka cika, zan hukunta sarkin Babilon da kuma al’ummarsa, ƙasar Babiloniyawa, saboda laifinsu,” in ji Ubangiji, “in kuma mai da ita kango har abada. 13Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abubuwan na yi magana a kanta, dukan abubuwan da aka rubuta a wannan littafi, abubuwan da Irmiya kuma ya yi annabci a kan dukan al’ummai. 14Su kansu al’ummai da sarakuna masu yawa za su bautar da su; zan sāka musu bisa ga ayyukansu da aikin hannuwansu.”

15Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa mini, “Ka karɓi kwaf ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al’umman da na aike ka gare su, su sha. 16Sa’ad da suka sha, za su yi ta tangaɗi su kuma yi hauka saboda takobin da zan aika a cikinsu.” 17Saboda haka na karɓi kwaf daga hannun Ubangiji na sa dukan al’ummai waɗanda ya aiko ni wurinsu su sha.

18Urushalima da garuruwan Yahuda, sarakunan da fadawanta, don su mai da su kufai da kuma abin bantsoro da ba’a da la’ana, yadda suke a yau;

19Fir’auna sarkin Masar, ma’aikatansa, fadawansa da dukan mutanensa, 20da dukan baƙin da suke can;

dukan sarakunan Uz;

dukan sarakunan Filistiyawa (waɗannan na Ashkelon, Gaza, Ekron da mutanen da aka bari a Ashdod);

21Edom, Mowab da Ammon;

22dukan sarakunan Taya da Sidon;

sarakunan bakin teku a ƙetaren teku;

23Dedan, Tema, Buz da dukan waɗanda suke a manisantan wurare;

24dukan sarakunan Arabiya da dukan sarakunan baƙin da suke zama a hamada;

25dukan sarakunan Zimri, Elam da Mediya;

26da kuma dukan sarakunan arewa, nesa da kuma kusa, bi da bi, dukan mulkokin duniya.

Bayan dukansu kuma, sai sarkin Sheshak ma yă sha.

27“Sa’an nan na faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku sha, ku bugu ku kuma yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku ƙara tashi saboda takobin da zan aiko muku.’ 28Amma in suka ki su karɓi kwaf ɗin daga hannunka su sha, ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa dole ku sha! 29Ga shi, na sa masifa tă yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana, kuna gani za ku tafi ba hukunci? Ba za ku tafi ba hukunci ba, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’

30“Yanzu ka yi annabcin dukan waɗannan maganganu a kansu ka kuma ce musu,

“ ‘ Ubangiji zai yi ruri daga bisa;

zai yi tsawa daga mazauninsa mai tsarki

ya kuma yi ruri da ƙarfi a kan ƙasarsa.

Zai yi ihu kamar waɗanda suke matsin ’ya’yan inabi,

yi ihu a kan dukan waɗanda suke zaune a duniya.

31Hayaniya za tă taso har iyakar duniya,

gama Ubangiji zai kawo tuhume-tuhume a kan al’ummai;

zai kawo shari’a a kan dukan ’yan adam

ya kuma kashe mugaye da takobi,’ ”

in ji Ubangiji.

32Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,

“Duba! Masifa tana yaɗuwa

daga al’umma zuwa al’umma;

hadari mai girma yana tasowa

daga iyakar duniya.”

33A lokacin waɗanda Ubangiji ya kashe za su kasance a ko’ina, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Ba za a yi kuka dominsu, ba za a tattara su don a binne ba, amma za su zama kamar juji da an tsiba a ƙasa.

34Ku yi kuka ku kuma yi makoki, ku makiyaya;

ku yi ta birgima a ƙura, ku shugabannin garke.

Gama lokacin da za a yanka ku ya zo;

za ku fāɗi ku kuma farfasa kamar tukunyar yumɓu mai kyau.

35Makiyaya ba za su sami wurin da za su gudu su tafi ba,

shugabannin garke ba za su sami wurin kuɓuta ba.

36Ji kukan makiyaya,

kururuwan shugabannin garke,

gama Ubangiji yana hallaka wurin kiwo.

37Rafi mai gudu a hankali zai zama kango

saboda zafin fushin Ubangiji.

38Kamar zaki zai bar wurin ɓuyarsa,

ƙasarsu kuma za tă zama kufai

saboda takobin masu danniya

da kuma saboda zafin fushin Ubangiji.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Setenta anos de exílio e o cálice da ira

  • A profecia é datada especificamente no quarto ano do rei Jeoaquim de Judá, coincidindo com o primeiro ano de Nabucodonosor, rei da Babilônia. Jeremias destaca que vinha proclamando os avisos de Deus continuamente há vinte e três anos, desde o décimo terceiro ano do rei Josias.Fontes: o próprio texto bíblico · Jeremiah · Jehoiakim · Nebuchadnezzar
  • Este capítulo apresenta a profecia marcante de que Judá e as nações vizinhas serviriam ao rei da Babilônia por setenta anos. O texto também prediz que, cumpridos esses setenta anos, a própria Babilônia e a terra dos caldeus seriam punidas e reduzidas à desolação.Fontes: o próprio texto bíblico · Babylon
  • A visão de julgamento se estende muito além de Judá por meio do símbolo de um cálice de ira entregue a vários povos vizinhos. Entre eles estavam o Egito, cidades filisteias como Ascalom, Gaza e Asdode, além de vizinhos regionais como Edom e Moabe.Fontes: o próprio texto bíblico · Ashdod · Ashkelon · Gaza

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Babylon · 32.543, 44.422 · versículos 1, 9, 11, 12, 14
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 2, 18, 29
  • Chaldea · 30.962, 46.104 · versículo 12
  • Egypt · 30.129, 31.308 · versículos 19, 20
  • Ashdod · Hoje: Tel Ashdod · 31.757, 34.658 · versículo 20
  • Ashkelon · Hoje: Tel Ashkelon · 31.664, 34.546 · versículo 20
  • Ekron · Hoje: Tel Miqne · 31.777, 34.852 · versículo 20
  • Gaza · Hoje: Tell Harube · 31.504, 34.464 · versículo 20
  • Ammon · 31.955, 35.934 · versículo 21
  • Edom · 30.746, 35.604 · versículo 21
  • Moab · Hoje: Moab 1 · 31.181, 35.701 · versículo 21
  • Sidon · Hoje: Sandikli archaeological site in Sidon · 33.561, 35.372 · versículo 22
  • Tyre · 33.271, 35.196 · versículo 22
  • Tema · Hoje: Tayma · 27.630, 38.552 · versículo 23
  • Arabia · Hoje: Arabian Peninsula · 23.000, 46.000 · versículo 24
  • Elam · 32.189, 48.258 · versículo 25
  • Media · 34.806, 48.516 · versículo 25
  • Sheshach · Hoje: Babylon · 32.543, 44.422 · versículo 26

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.