Hechos 28
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Sa'adda muka sauka lafiya, sai muka ji cewa sunan tsibirin Malita. 2Mutanen garin sun nuna mana alheri matuka don sun hura wuta don mu ji dimi, saboda ruwan sama da sanyin da ake yi. 3Amma sa'adda Bulus ya tara kiraruwa don hura wuta, sai maciji saboda zafin wuta, ya fito ya nade hannuwansa. 4Da mazaunan garin suka ga maciji ya nade hannuwansa, sai suka cema junansu, “Ba shakka wannan mutumin mai kisan kai ne, koda shike ya tsira daga Teku, sharia baza ta barshi da rai ba”. 5Amma ya karkade macijin cikin wuta ba tare da ya cutar da shi ba. 6Sun saurara su gani ko zai kumbura ko ya fadi matacce. Amma da suka jira dan lokaci basu ga wata matsala ta same shi ba sai suka canza tunaninsu sukace shi wani allah ne. 7A kusa da wannan wurin tsibirin akwai wasu gonakin wani babban mutumin tsibirin, mai suna Babiliyas. Ya karbe mu ya biya bukatun mu har kwana uku. 8Ana nan ashe mahaifin Babiliyas yana fama da zazzabi da atuni. Bulus ya shiga, yayi masa addu'a, ya dibiya masa hannu, ya sami warkarwa. 9Sa'adda wannan ya faru, sauran marasa lafiya da ke tsibirin sun zo sun sami warkarwa. 10Mutanen sun mutunta mu kwarai. Yayin da muke shirin tafiya, sun bamu duk abinda muke bukata. 11Bayan watanni uku, mun shiga jirgin Iskandariya wanda tun da hunturu yake a tsibirin mai zane kamannin Tagwaye Maza. 12Bayan saukar mu a birnin Sirakus, mun yi kwana uku a wurin. 13Daga nan sai muka tafi, har muka zo birnin Rigiyum. Bayan kwana daya iska mai karfi daga kudu ta taso, a cikin kwana biyu muka iso Butiyoli. 14A can muka iske wasu 'yan'uwa suka roke mu mu zauna tare da su har kwana bakwai. Ta wannan hanyar ce muka zo Roma. 15Daga can da 'yan'uwa suka ji labarin mu, suka fito don su tarbe mu tun daga Kasuwar Abiyas da kuma Rumfuna Uku. Da Bulus ya gan su, ya yi wa Allah godiya ya kuma sami karfafawa. 16Sa'adda muka shiga Roma, aka yardar wa Bulus ya zauna shi kadai tare da sojan da ke tsaronsa. 17Ana nan bayan kwana uku, Bulus ya kira shugabannin Yahudawa. Bayan da suka taru, sai ya ce masu, “Yan'uwa, ko da shike ban yi wa kowa laifi ko keta al'adun Ubanninmu ba, duk da haka an bashe ni daurarre tun daga Urushalima zuwa ga hannunwan mutanen Roma. 18Bayan tuhumata, sun yi kudirin saki na, domin ban yi laifin da ya cancanci mutuwa ba. 19Amma da Yahudawa suka tsaya a kan ra'ayin su, ya zama dole in daukaka kara zuwa ga Kaisar, ba domin ina da wani dalilin da zan yi karar al'ummata ba ne. 20Saboda wannan ne na bukaci ganinku in yi magana da ku. Saboda begen da Isra'ila suke da shi ya sa nake daure da wannan sarkar”. 21Sai suka ce masa, “Bamu karbi wasiku daga Yahudiya game da kai ba, babu kuma wani daga cikin 'yan'uwa wanda ya kawo mana wani rahoto ko wata magana game da kai. 22Amma muna so mu ji daga gare ka abin da kayi tunani ka kuma gani game da wannan darikar, gama mun sani ana kushenta a ko'ina.” 23Sa'adda suka sa masa rana, mutane da dama suka same shi a masaukinsa. Ya gabatarda zantattukan a gare su, yana tabbatar da bayyanuwar mulkin Allah. Har ya nemi ya rinjaye su a kan zancen Yesu, tun daga attaurat ta Musa zuwa litattafan annabawa, ya yi wannan tun daga safiya har yamma. 24Wasu sun kawar da shakkar abin da aka fada, amma wadansu basu gaskanta ba. 25Da shike ba su yarda da junansu ba, sai suka tafi bayan da Bulus ya fadi kalma daya, “Ruhu Mai Tsarki ya yi magana ta bakin annabi Ishaya zuwa ga kakanninku. 26Ya ce, 'Jeka wurin al'umman nan ka ce, cikin ji zaku ji amma ba zaku fahimta ba; zaku gani amma ba zaku gane ba. 27Amma zuciyar mutanen nan ta yi kanta, kunnuwansu sun ji da kyar, sun rufe idanunsu; don kada su gani su gane, su kuma ji da kunuwansu, kuma su fahimta da zuciyarsu, domin su juyo ni kuma in warkar da su.” 28Saboda haka, sai ku sani cewa wannan ceto na Allah an aikar da shi zuwa ga Al'ummai, za su kuma saurara.” 29[Sa'adda ya fadi wannan zantattuka, Yahudawa suka tashi, suna gardama da junansu.] 30Bulus ya zauna shekaru biyu a cikin gidan hayarsa, yana marabtar duk wadanda suka zo wurinsa. 31Yana wa'azin mulkin Allah, yana koyarwa da al'amuran Ubangiji Yesu Kristi gaba gadi. Ba wanda ya hana shi.

¿Sabías que…?
Del naufragio en Malta hasta Roma
- La isla que los viajeros supieron que se llamaba Malta es la isla del Mediterráneo también conocida como Melita, la Malta actual. El Easton's Bible Dictionary (1897) dice que fue colonizada primero por fenicios, a quienes identifica con los “bárbaros” de Hechos 28:2, y que los griegos la tomaron en 736 a. C., después de lo cual pasó a los cartagineses. Pablo y sus compañeros permanecieron allí tres meses, hasta que pasó la temporada de tormentas.Fuentes: Melita · Publius · el propio texto bíblico
- Cerca había una propiedad de Publio, el principal de la isla, que recibió al grupo náufrago y lo hospedó con generosidad durante tres días. El Easton's Bible Dictionary (1897) señala que algunos suponen que la palabra griega protos, traducida como “hombre principal”, era propiamente un término maltés, el título oficial del gobernador.Fuentes: Publius · el propio texto bíblico
- Después de tres meses zarparon en un barco alejandrino que había invernado en la isla. Permanecieron tres días en Siracusa, en la costa sureste de Sicilia, que el Easton's Bible Dictionary (1897) describe como distinguida por su tamaño y esplendor; luego llegaron a Regio, en el estrecho de Mesina, y a Puteoli, que ese diccionario describe como el gran puerto de los barcos alejandrinos de grano, a unas 170 millas de Roma. Desde Puteoli siguieron hacia Roma por la Vía Apia, y unos hermanos salieron a su encuentro hasta el Foro de Apio y las Tres Tabernas.Fuentes: Syracuse · Rhegium · Puteoli · el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Malta · 35.933, 14.412 · versículo 1
- Alexandria · 31.183, 29.896 · versículo 11
- Syracuse · 37.064, 15.293 · versículo 12
- Puteoli · Hoy: Pozzuoli · 40.826, 14.121 · versículo 13
- Rhegium · Hoy: Reggio Calabria · 38.109, 15.644 · versículo 13
- Rome · 41.892, 12.485 · versículos 14, 15, 16, 30
- Forum of Appius · Hoy: Forum Appii · 41.466, 12.998 · versículo 15
- Three Taverns · 41.562, 12.874 · versículo 15
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 17
- Judea · Hoy: Judea 1 · 31.777, 35.234 · versículo 21
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org