Nations Bible

Hechos 27

Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

1Bayan da aka amince zamu tafi Italiya, sun mika Bulus tare da wadansu daurarru a hanun wani jarumi mai suna Yuliyas, daga batalian Agustas. 2Muka shiga Jirgin ruwa daga Adramatiya, wanda ke shirin tashi zuwa kusa da gefen tekun Asiya. Sai muka je teku. Aristakus mutumin Tasalonika a Makidoniya ya tafi tare damu. 3Washegari muka sauka birnin Sidon, inda Yuliyas ya nuna wa Bulus karamci ya kuma yarda abokansa su bi shi don ya kula da su. 4Daga wurin, muka bi teku muka tafi ta Tsibirin Kubrus, domin matsananciyar iska da ke gaba damu. 5Sa'adda muka ketare ruwa zuwa sassan Kilikiya da Bamfiliya, muka zo Mira ta birnin Lisiya. 6Anan, jarumin ya sami jirgin ruwa daga Iskandariya wanda za shi Italiya. Ya samu cikinsa. 7Kwana da kwanaki muna tafiya a hankali a karshe da kyar muka sauka kusa da Sinidus, iska ta hana mu tafiya, sai muka ratsa ta Karita, kusa da Salmina. 8Da wahala muka bi ta makurda har muka zo wani wuri da ake kira Mafaka Mai Kyau wanda ke kusa da birnin Lasiya. 9Yanzu mun dauki dogon lokaci, gashi lokacin azumin Yahudawa ya wuce, tafiyar kuma ta zama da hatsari. Bulus ya gargade su, 10ya ce, “Jama'a, na gane tafiyarmu zata zamar mana da barna da asara mai yawa, ba ga kaya da jirgin kadai ba amma har da rayukan mu.” 11Amma jarumin ya fi mai da hankali ga maganar shugabansa da mai jirgin ruwan, fiye da abubuwan da Bulus ya fadi. 12Da shike tashar ba za ta yi dadin zama da hunturu ba, mafi yawa sun ba da shawara a bar wurin, in maiyiwuwa ne muga mun kai birnin Finikiya, don mu yi hunturu a can. Finikiya tashar jirgin ruwa ce a Karita, tana fuskantar arewa maso gabas da kudu maso gabas. 13Sa'adda iska daga kudu ta huro a hankali, sun tsammaci bukatarsu ta biya. Sai suka janye linzamin jirgin ruwan sukabi ta Karita kusa da gaba. 14Amma bayan wani dan lokaci sai iska mai karfi da ake kira Yurokilidon, ta fara bugun mu daga tsibirin. 15Sa'adda Jirgin ruwan ya kasa fuskantar iskar, sai muka bi inda iskar ta nufa. 16Sai muka bi ta inda muka sami kariya kusa da wani dan tsibiri wanda ake kira Kauda; kuma da wahala muka daure karamin jirgin a jikin babban. 17Bayanda suka daga shi, sun yi amfani da igiyoyi don su daure jirgin don gudun fadawa kan yashin Sirtis, suka bar jirgin yana ta korarsu. 18Mun yi ta fama da hadari ba kadan ba, da gari ya waye ma'aikatan jirgin suka fara zubar da kaya daga jirgin. 19A rana ta uku, ma'aikatan jirgi suka jefar da kaya daga cikin jirgin da hannuwansu. 20Kwanaki dayawa ba mu ga hasken rana da taurari a bisan mu ba. Babban hadari kadai ke dukanmu, duk mun fidda zuciya zamu tsira. 21Sa'adda sun dade basu ci abinci ba, sai Bulus ya tashi a gaban ma'aikatan jirgi yace, “Jama'a, da kun saurare ni, da bamu tashi daga Karita ba, balle mu fuskanci wannan barna da asarar. 22Yanzu fa ina karfafa ku kuyi karfin hali, domin ba wanda zai rasa ransa a cikinku, sai dai jirgin kadai za a rasa. 23Domin daren da ya gabata mala'ikan Allah wanda ni nasa ne, wanda kuma nake bautawa -mala'ikansa ya tsaya kusa dani 24ya ce, “Kada ka ji tsoro, Bulus, dole ka tsaya gaban Kaisar, duba kuma, Allah cikin jinkansa ya baka dukan wadannan da ke tafiya tare da kai. 25Domin haka, jama'a, kuyi karfin hali, domin na gaskanta da Allah, kamar yadda aka fada mani haka zai faru. 26Amma lallai dole ne a jefa mu kan wani tsibiri”. 27Sa'adda dare na goma sha hudu ya yi, ana ta tura mu nan da can a cikin tekun Adriyat, wajen tsakar dare, ma'aikatan jirgin sun tsammaci sun kusanci wata kasa. 28Da suka gwada sai suka iske kamu ashirin; bayan dan lokaci kadan, sun sake aunawa sai suka iske kamu sha biyar ne. 29Tsoro ya kama su ko watakila a jefar da mu kan duwatsu, sai suka jefa linzami hudu daga karshen jirgin suka yi addu'a don gari ya waye da sauri. 30Ma'aikatan jirgin ruwan suna neman hanyar da za su rabu da jirgin kuma sun jefa karamin jirgin a cikin teku. Suka yi kamar zasu jefa wasu linzamai daga gaban jirgin. 31Amma Bulus ya ce ma jarumi da sojojin, “Idan mutanen nan ba zasu tsaya cikin jirgin ba, ba zaku tsira ba”. 32Sai sojojin suka yanke igiyoyin jirgin suka kuma barshi ya fadi. 33Da gari ya fara wayewa, Bulus ya roke su duka su dan ci abinci, ya ce, “Yau kwana goma sha hudu kenan ba ku ci kome ba. 34Saboda haka na roke ku ku ci abinci, domin wannan saboda lafiyarku ne; kuma ko gashin kanku daya baza ku rasa ba”. 35Da ya fadi haka sai ya dauki gurasa ya yi godiya ga Allah a idanun kowa. Sai ya gutsutsura gurasa ya fara ci. 36Sai dukansu suka karfafu suka kuma ci abinci. 37Mu mutane 276 (dari biyu da saba'in da shida) ne cikin jirgin. 38Da suka ci suka koshi, suka zubar da alkamar cikin teku domin su rage nauyin jirgin. 39Da gari ya waye, basu fahimci kasar ba, amma suka hangi wani lungu a gacci, sai suka yi shawara tsakaninsu ko su tuka jirgin zuwa cikin lungun. 40Sai suka yanke linzaman suka bar su cikin tekun. Cikin lokaci guda suka kwance igiyoyin da ke juya jirgin, suka saki filafilan goshin jirgi suka nufi gabar tekun. 41Da suka iso inda ruwa biyu suka hadu, sai jirgin ya tsaya kasa. Gaban jirgin ya kafe a nan, ba damar matsawa, sai kuma kurar jirgin ta fara kakkaryewa saboda haukan rakuman ruwa. 42Shirin sojojin ne su kashe 'yan kurkukun domin kada su yi iyo su tsere. 43Amma shi hafsan ya so ya ceci Bulus, sai ya tsai da shirin su, ya ba da umarni, duk masu iya iyo su yi tsalle su fada ruwa su kai gacci. 44Sa'annan sauran mazajen su biyo baya, wadansu a kan karyayyun katakai, wadansu akan abubuwan da ke a jirgin. Ta haka ne dukanmu muka kai gacci lafiya.

Ilustración artística: una interpretación, no un registro histórico.

¿Sabías que…?

Tormenta y naufragio camino a Roma

  • Pablo y los demás prisioneros no navegaron directo a Italia. En Cesarea abordaron un barco de Adramitio, ciudad de la costa de Misia, en Asia Menor, con rumbo a puertos a lo largo de la costa de Asia, nombre que el Easton's Bible Dictionary entiende en este versículo probablemente como Asia Menor, y ese barco los llevó solo hasta Mira, en Licia. Allí el centurión los hizo subir a un barco alejandrino que navegaba hacia Italia; el diccionario señala que era raro que un barco zarpara de cualquier puerto de Palestina directo a Italia.Fuentes: Adramyttium · Asia · el propio texto bíblico
  • Los prisioneros fueron entregados a Julio, centurión del Regimiento Imperial. El Easton's Bible Dictionary lo identifica como centurión de la cohorte Augusta, o de la guardia personal del emperador, y describe el trato cortés que tuvo con Pablo. En Sidón, a unas veinticinco millas al norte de Tiro, le permitió visitar a sus amigos y recibir atención; más tarde impidió el plan de los soldados de matar a los prisioneros, para que se salvara la vida de Pablo.Fuentes: Julius · Sidon · el propio texto bíblico
  • Después de Gnido, el barco avanzó a lo largo de Creta, una de las islas más grandes del Mediterráneo, de unas 140 millas de largo y 35 de ancho, que Pablo visitó en este viaje a Roma. El relato dice que el viaje ya se había vuelto peligroso porque era después del Ayuno, y que Buenos Puertos no era adecuado para invernar. Una cronología fecha el inicio del viaje a Roma en el año 56 d.C. y el naufragio en la tormenta en el 57 d.C.Fuentes: Crete · Journey to Rome begins · Paul is shipwrecked by a storm · el propio texto bíblico

Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.

Lugares de este capítulo

  • Italy · 41.892, 12.485 · versículos 1, 6
  • Adramyttium · Hoy: Oren · 39.501, 26.933 · versículo 2
  • Asia · 38.400, 28.300 · versículo 2
  • Thessalonica · Hoy: Thessaloniki · 40.638, 22.946 · versículo 2
  • Sidon · Hoy: Sandikli archaeological site in Sidon · 33.561, 35.372 · versículo 3
  • Cyprus · 35.000, 33.000 · versículo 4
  • Cilicia · 36.913, 34.892 · versículo 5
  • Lycia · 36.733, 29.900 · versículo 5
  • Myra · 36.259, 29.985 · versículo 5
  • Pamphylia · 37.000, 31.000 · versículo 5
  • Alexandria · 31.183, 29.896 · versículo 6
  • Cnidus · 36.686, 27.375 · versículo 7
  • Crete · 35.310, 24.893 · versículos 7, 8, 12, 13, 14, 21
  • Salmone · Hoy: Cape Sideros · 35.316, 26.312 · versículo 7
  • Fair Havens · Hoy: Kaloi Limenes · 34.930, 24.800 · versículos 8, 12
  • Lasea · Hoy: Lasaea · 34.941, 24.811 · versículo 8
  • Cauda · Hoy: Gavdos · 34.833, 24.083 · versículo 16
  • Syrtis · Hoy: Sidra · 31.500, 18.000 · versículo 17
  • Adriatic Sea · Hoy: Adriatic and Ionian Seas · 38.000, 19.000 · versículo 27

Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Habla con nosotros

Cuéntanos desde dónde lees, cómo te ha ayudado la Biblia o qué podemos mejorar. Leemos todos los mensajes.