Nations Bible

Hechos 13

Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

1A cikin iklisiyar da take Antakiya, akwai annabawa da malamai. Sune su Barnabas, Saminu (wadda ake kira Baki) da Lukiya Bakurame da Manayin (wanda aka yi renon su tare da sarki Hiridus mai mulki) da Shawulu. 2Sa'adda suke bauta wa Allah tare da azumi, sai Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku kebe mani Barnaba da Shawulu domin aikin da na kiraye su”. 3Bayan taron sun yi addu'a da azumi, sai suka sa masu hannu, su suka sallame su. 4Sai Shawulu da Barnabas suka yi biyayya da Ruhu Mai Tsarki suka tafi Sulukiya; daga nan suka ketare zuwa tsibirin Kuburus. 5Sa'adda suke garin Salami, suka koyar da maganar Ubangiji a majami'un Yahudawa, suna kuma tare da Yahaya Markus mai taimakonsu. 6Bayan sun zaga tsibirin duka har Bafusa, nan suka iske wani Bayahude mai suna Bar-yeshua mai tsafi kuma annabin karya. 7Wannan mai tsafin wanda ke tare da Makaddas, shi Sarjus Bulus mutum mai basira ne. Wannan kuwa ya kira Shawulu da Barnaba domin yana so ya ji maganar Allah. 8Amma Elimas “mai tsafi” (fasarar sunansa kenan) ya yi adawa da su; yana so ya baudar da Makaddashin daga bangaskiya. 9Amma Shawulu wanda ake ce da shi Bulus yana cike da Ruhu Mai Tsarki ya kafa masa ido. 10Sai ya ce, “Kai dan iblis, kana cike da kowace irin yaudara da mugunta. Kai abokin gabar kowanne irin adalci ne. Ba za ka daina karkata mikakkakun hanyoyin Ubangiji ba? 11Yanzu ga hannun Ubangiji bisa kanka, zaka zama makaho. Ba za ka ga rana ba nan da dan lokaci.” Nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi ya fara yawo yana neman mutane su yi masa jagora. 12Bayan da Makaddashin ya ga abin da ya faru ya ba da gaskiya saboda ya yi mamakin koyarwa game da Ubangiji. 13Bulus da abokansa suka shirya suka ketare a jirgin ruwa daga Bafusa zuwa Firjiya a Bamfiliya. Amma Yahaya ya bar su ya koma Urushalima. 14Bulus da abokansa suka tafi daga Firjiya zuwa Antakiya na kasar Bisidiya. Nan suka shiga majami'a ran Asabaci suka zauna. 15Bayan karatun dokoki da annabawa, shugabanin iklisiyar suka tura sako cewa, “'Yan'uwa, idan kuna da wani sakon karfafawa ga jama'a ku fadi.” 16Bulus kuwa ya tashi ya yi alama da hannunsa ya ce, “Mutanen Isra'ila da ku wadanda kuke girmama Allah, ku ji. 17Allahn Isar'ila ya zabi kakkaninmu ya kuma ribabbanya su sa'adda suke kasar Masar da kuma madaukakin iko ya fito da su daga cikinta. 18Ya yi hakuri da su a jeji har na tsawon shekara arba'in. 19Bayan ya hallaka kasashe bakwai a kasar Kan'ana, ya ba kakkaninmu kasar nan gado. 20Duk wadanan abubuwan sun faru shekaru dari hudu da hamsin da suka wuce. Bayan wadannan, Allah ya ba su alkalai har sai da annabi Sama'ila ya zo. 21Sai jama'a suka roka a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Saul dan Kish, mutumin kabilar Binyamin ya zama sarki har na tsawon shekara arba'in. 22Allah kuwa ya cire shi daga kan kujerar sarauta, ya daga Dauda ya zama sarkinsu. A kan Dauda ne Allah ya ce, 'Na sami Dauda dan Yessi, mutumin da zuciyata ke so; zai yi duk abin da nake so'. 23Daga zuriyar mutumin nan Allah ya fito da mai ceto, Yesu, kamar yadda aka alkawarta zai yi. 24Wannan ya faru kafin Yesu ya zo, Yahaya ya yi shelar baftimar tuba ga jamma'ar Isra'ila. 25Sa'adda Yahaya ya gama aikin sa, sai ya ce, 'Wanene ni a tsamanin ku? Ba nine shi ba. Amma ku saurara, akwai wani mai zuwa bayana wanda maballin takalminsa ban isa in kwance ba.' 26Yan'uwa 'ya'ya daga zuriyar Ibrahim, da wadanda ke bautar Allah a cikinku, saboda mune aka turo sakon ceto. 27Saboda wadanda ke zaune cikin Urushalima, da masu mulkinsu, ba su gane shi ba, kuma sun cika fadin annabawa da a ke karantawa kowace ranar Asabaci ta wurin kashe shi. 28Duk da cewa ba su sami dalilin mutuwa a kansa ba, suka roki Bilatus ya kashe shi. 29Bayan sun gama duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka sauke shi daga giciye suka sa shi a cikin kabari. 30Amma Allah ya tashe shi daga matattu. 31Mutanen da suka zo tare da shi daga Galili da Urushalima kuwa suka yi ta ganinsa har kwanaki da yawa. Wadanan mutane kuma sune shaidunsa ga jama'a a yanzu. 32Mun kawo maku labari mai dadi game da alkawaran da aka yi wa kakkaninmu. 33Ubangiji ya bar mana alkawaran. Don haka ya ta da Yesu daga matattu. Kamar yadda ya ke a littafin zabura ta biyu: ''Kai da na ne yau na zama mahaifinka.'' 34Kuma dalilin tayar da shi daga matattu shine saboda kada jikinsa ya rube, ya yi magana kamar haka: ''Zan baku albarkun Dauda masu tsarki tabatattu.'' 35Wannan shine dalilin da ya yi magana kuma a wata Zabura, 'Ba za ka bar Mai Tsarkinka ya rube ba.' 36Bayan Dawuda ya yi wa Allah bauta a cikin zuciyarsa da kuma abin da Allah yake so, ya mutu, aka binne shi tare da kakkaninsa, ya kuma ruba, 37amma wanda Allah ya tayar bai ga ruba ba. 38'Yan'uwa, ku sani cewa ta wurin mutumin nan aka yi maku wa'azin gafarar zunubai. 39Ta wurinsa ne duk wanda ya ba da gaskiya zai kubuta daga dukan abin da dokar Musa bata 'yantar da ku a kai ba. 40Saboda haka ku yi hankali da abubuwan da annabawa suka fada kada su faru a kanku: 41'Ku masu reni, za ku rude don mamaki, ku kuma shude; saboda ina aiki a cikin kwananakinku, aikin da ba za ku yarda ba ko da wani ya gaya maku.” 42Da Bulus da Barnaba suna fita kenan, sai jama'a suka rokesu, su sake yin irin wannan magana ranar Assabaci mai zuwa. 43Bayan da sujadar ta kare, Yahudawa da yawa da kuma wadanda suka shiga addinin Yahudanci suka bi Bulus da Barnaba, sai suka gargade su da su cigaba da aikin alherin Allah. 44Da Asabaci ta kewayo, kusan dukan garin suka taru domin su ji maganar Ubangiji. 45Sa'adda Yahudawa suka ga taron jama'a, sai suka cika da kishi suna karyata abubuwan da Bulus ya fada suka kuma aibata shi. 46Amma Bulus da Barnaba sun yi magana gabagadi suka ce, “Dole ne a fara fada maku maganar Allah. Amma da yake kun ture ta, kun nuna baku cancanci rai madawwami ba soboda haka zamu juya ga al'ummai. 47Don haka Ubangiji ya umarce mu, cewa, 'Na sa ku haske ga al'ummai, saboda ku kawo ceto ga iyakar duniya.'” 48Da al'ummai suka ji haka, sai suka yi murna suka kuma yabi kalmar Ubangiji. Dukan wadanda aka kaddarawa samin rai madawwami suka tuba. 49Kalmar Ubangiji kuwa ta bazu a kowanne bangaren yankin. 50Amma Yahudawan suka zuga wadansu mata masu sujada, masu daraja da kuma shugabannin mazan garin. Wannan ya tayar da tsanani ga Bulus da Barnaba har suka fitar da su daga iyakar garinsu. 51Amma Bulus da Barnaba suka kade masu kurar kafarsu. Suka tafi garin Ikoniya. 52Amma almajiran suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.

Ilustración artística: una interpretación, no un registro histórico.

¿Sabías que…?

La misión enviada desde Antioquía

  • El Diccionario Bíblico de Easton (1897) describe a Antioquía de Siria como la tercera ciudad en importancia del Imperio romano, después de Roma y Alejandría; fue la iglesia de allí la que apartó a Bernabé y a Saulo. Entre sus profetas y maestros estaban Simeón, llamado Níger, un sobrenombre que significa negro, quizá por su tez oscura, y Lucio de Cirene, en el norte de África.Fuentes: Antioch (Syria) · el propio texto bíblico · Simeon · Lucius
  • En Pafos, capital de Chipre y residencia del gobernador romano, un hechicero judío llamado Barjesús, también conocido como Elimas, un nombre árabe que significa mago o hechicero, intentó apartar de la fe al procónsul Sergio Paulo. Es aquí donde Saulo también es llamado Pablo; el Diccionario Bíblico de Easton (1897) dice que el nombre Pablo probablemente le fue dado en la infancia para usarlo en el mundo gentil, mientras que Saulo era su nombre hebreo de casa.Fuentes: Paphos · Elymas · Paul · el propio texto bíblico
  • Enviados desde Antioquía, bajaron a Seleucia, el puerto de la ciudad cerca de la desembocadura del Orontes, y navegaron hasta Chipre; después desembarcaron en Perge, capital de Panfilia, a orillas del río Cestro. Allí Juan los dejó y regresó a Jerusalén; su nombre romano, Marcos, poco a poco llegó a reemplazar su nombre judío, y era primo de Bernabé.Fuentes: Seleucia · Perga · John Mark · el propio texto bíblico

Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.

Lugares de este capítulo

  • Antioch · Hoy: Antioch on the Orontes · 36.227, 36.172 · versículo 1
  • Cyrene · 32.821, 21.851 · versículo 1
  • Cyprus · 35.000, 33.000 · versículo 4
  • Seleucia · Hoy: Seleucia Pieria · 36.124, 35.922 · versículo 4
  • Salamis · 35.185, 33.902 · versículo 5
  • Paphos · Hoy: New Paphos · 34.756, 32.404 · versículos 6, 13
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 13, 27, 31
  • Pamphylia · 37.000, 31.000 · versículo 13
  • Perga · 36.960, 30.854 · versículos 13, 14
  • Antioch · Hoy: Antioch in Pisidia · 38.306, 31.189 · versículo 14
  • Pisidia · 38.306, 31.189 · versículo 14
  • Egypt · 30.129, 31.308 · versículo 17
  • Canaan · 32.767, 35.333 · versículo 19
  • Galilee · 32.760, 35.527 · versículo 31
  • Iconium · Hoy: Konya · 37.872, 32.492 · versículo 51

Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Habla con nosotros

Cuéntanos desde dónde lees, cómo te ha ayudado la Biblia o qué podemos mejorar. Leemos todos los mensajes.