Hechos 12
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1A lokacin nan Sarki Hiridus ya sa wa wasu masu bi hannu domin ya musguna masu. 2Ya kashe Yakubu dan'uwan Yahaya da takobi. 3Bayan da ya ga hakan ya gamshi Yahudawa, sai ya kama Bitrus ma. 4Bayan ya kama shi, sai ya tsare shi a kurkuku ya kuwa sa sojoji hudu su dinga tsaron sa; yana niyyar kawo shi gaban mutanen a bayan Idin katarewa. 5To, Bitrus na tsare a kurkuku, amma 'yan'uwa na iklisiya suna yin addu'a ga Allah sosai domin sa. 6Ana kamar gobe Hiridus zai fitar da shi, a wannan daren, Bitrus yana barci a tsakanin sojoji biyu, daure da sarkoki biyu; sojoji kuma na gadi a bakin kurkukun. 7Ba zato, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gareshi, haske ya haskaka dakin. Ya taba Bitrus a gefe ya tashe shi kuma ya ce, “Tashi da sauri.” Sai ga sarkokin suka zube daga hannunsa. 8Mala'ikan ya ce masa, “Yi damara ka sa takalmanka.” Bitrus kuwa yayi haka. Mala'ikan ce ma sa, “Yafa mayafinka, ka biyo ni.” 9Bitrus kuwa ya bi mala'ikan suka fita waje. Bai gane abin da mala'ikan ke yi zahiri ne ba. Yana zaton ko yana ganin wahayi ne. 10Bayan da suka wuce masu tsaron fari da na biyu, sun kai kofar da aka yi da karfe wadda ta mike zuwa cikin gari; ta bude masu da kanta. Suka fita sun bi titin, kuma nan take kuma sai mala'ikan ya bar shi. 11Da Bitrus ya komo hayyacin sa, ya ce, “Hakika yanzu na gane Ubangiji ya aiko da mala'ikansa don ya kubutar da ni daga hannun Hiridus da abin da Yahudawa suke zato.” 12Da ya gane haka, ya zo gidan Maryamu mahaifiyar Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus; masu bi da yawa sun taru a can suna addu'a. 13Da ya kwankwasa kofar gidan, sai baiwar gidan mai suna Roda ta zo don ta bude kofar. 14Da ta gane muryar Bitrus, don farin ciki ta kasa bude kofar; maimakon haka, ta koma daki a guje, don ta basu labari Bitrus na tsaye a bakin kofa. 15Suka ce mata, “Kin haukace.” Amma ta nace da cewa haka ne. Suka ce, “Mala'ikansa ne.” 16Amma Bitrus ya ci gaba da kwankwasawa, da suka bude kofar, sai suka ga ai shine, suka sha mamaki kwarai. 17Bitrus kuwa ya yi masu hannu yana, masu alama su yi shuru. Sai ya gaya masu labarin yadda Ubangiji ya kubutar da shi daga kurkukun. Ya ce, “Ku gaya wa Yakubu da dukan 'yan'uwa abin da ya faru.” Sai ya bar su, ya tafi wani wuri. 18Sa'anda gari ya waye ba karamar hargowa ce ta tashi a cikin sojojin ba, game da abin da ya faru da Bitrus. 19Bayan da Hiridus ya neme shi kuma bai same shi ba, sai ya tambayi masu tsaron kuma ya bada umarni a kashe su. Sai ya gangara daga Yahudiya zuwa Kaisariya ya yi zamansa a can. 20Yanzu kuwa Hiridus ya yi fushi sosai da mutanen Taya da Sidon. Suka tafi wurinsa tare. Suka roki Bilastasa, mataimakin sarkin, ya taimake su. Sai suka nemi sasantawa don suna samun abinci daga kasarsa ne. 21A ranan da aka kayyade, Hirudus ya sha damara da kayan saurata kuma ya zauna akan kursiyi; ya yi masu jawabi. 22Mutanen suka yi ihu, “Wannan muryar allahce, ba ta mutum ba!” 23Nan take mala'ika Ubangiji ya buge shi don bai ba Allah daukaka ba, nan take tsutsotsi suka cinye shi har ya mutu. 24Maganar Allah ta yadu tana ta ribabbanya. 25Bayan Barnaba da Shawulu sun gama aikin su a Urushalima. Suna dawowa, suka zo tare da Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus ne. [Barnaba da Shawulu suka koma Urushalima.]

¿Sabías que…?
La huida de Pedro y la muerte de Herodes
- El rey Herodes de este capítulo es Herodes Agripa I, nieto de Herodes el Grande, que con el tiempo llegó a poseer todo el reino de su abuelo y el título de rey. Hizo matar a Santiago y encarceló a Pedro. El Diccionario Bíblico de Easton (1897) dice que, en el segundo día de una fiesta en honor del emperador Claudio, Agripa apareció en el gran teatro de Cesarea con magníficas vestiduras de plata; era temprano, y los rayos del sol deslumbraban a quienes lo veían.Fuentes: Herod Agrippa I · el propio texto bíblico
- El Santiago muerto a espada era Santiago, hijo de Zebedeo, hermano del apóstolo Juan, un pescador que había trabajado como socio de Pedro. El Diccionario Bíblico de Easton (1897) lo presenta como el primero de los apóstoles en ser muerto y dice que Herodes Agripa lo hizo decapitar. El Santiago a quien Pedro pide que se avise a los creyentes es otro hombre: el mismo diccionario lo identifica como el Santiago que encabezaba la iglesia en Jerusalén.Fuentes: James (Son of Zebedee) · James (Brother of Jesus) · el propio texto bíblico
- Cuando comprendió que estaba libre, Pedro fue a la casa de María, madre de Juan Marcos, en Jerusalén, que el Diccionario Bíblico de Easton (1897) llama lugar habitual de reunión de los discípulos; mucha gente estaba reunida allí orando. La sirvienta que acudió a la puerta exterior se llamaba Rode, nombre que significa una rosa; llena de alegría al oír su voz, corrió adentro para anunciarlo y olvidó abrir la puerta. Juan, llamado también Marcos, era hijo de María —Marcos, su nombre romano, poco a poco reemplazó al nombre judío Juan— y más tarde salió de Jerusalén con Bernabé y Saulo.Fuentes: Mary (Mother of John Mark) · Rhoda · John Mark · el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Caesarea · Hoy: Caesarea Maritima · 32.500, 34.892 · versículo 19
- Judea · Hoy: Judea 1 · 31.777, 35.234 · versículo 19
- Sidon · Hoy: Sandikli archaeological site in Sidon · 33.561, 35.372 · versículo 20
- Tyre · 33.271, 35.196 · versículo 20
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 25
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org