1 Corintios 9
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Ni ba yantacce bane? Ni ba Manzo ba ne? Ban ga Ubangijinmu Yesu ba? ba ku ne aikin hannuna cikin Ubangiji ba? 2Idan ni ba Manzo ba ne ga wadansu, hakika ni Manzo ne a gare ku. Ai kune shedar manzanci na cikin Ubangiji. 3Ga kariya ta zuwa masu zargi na, 4Ba mu da 'yanci mu ci mu sha? 5Ba mu da 'yanci mu dauki mace mai bada gaskiya kamar sauran manzanni da Kefas da 'yan'uwan Ubangiji? 6ko ni da Barnabas ne kawai muka cancanci aiki? 7Wake aikin soja daga aljihunsa? Wake shuka gonar inabi baya ci daga 'ya'yan ta ba? Ko kuwa wake kiwon tumaki ba ya shan madarasu? 8Ina wannan zance da ikon mutum ne? Doka bata fadi haka ba? 9Gama a rubuce yake a attaura ta Musa cewa, Takarkari mai tattake hatsi kada a sa masa takunkumi. Amma shanu ne Ubangiji ke zance a kai? 10Ba don mu yake magana ba? An rubuta domin mu ne. Domin wanda yake noma, yayi cikin bege. mai tattake hatsi kuma yayi da begen samu. 11Idan mun yi shuka ta ruhaniya a rayuwarku, mai wuya ne mu girbi kayan ku na jiki? 12Idan wadansu sun mori wannan 'yanci a gurin ku, ba mu fi su cancanta ba? duk da haka bamu yi amfani da wannan 'yancin ba, maimakon haka, mun yi jimriya da duk abin da zaya hana bisharar Yesu Almasihu. 13Baku sani ba masu bauta a haikali suna samun abincinsu ne daga haikalin? Baku sani ba masu bauta a bagadi, suna da rabo daga abin da ake kawowa kan bagadin? 14Haka kuma Ubangiji ya umarta masu aikin bishara zasu ci abincinsu ta hanyar bishara. 15Amma ban yi amfani da wannan 'yanci ba, ba kuma ina rubuta maku domin ayi mani wani abu bane, na gwanmace in mutu maimakon wani ya hana ni wannan fahariya. 16Ko nayi shelar bishara, ba ni da dalilin fahariya domin ya zama dole in yi. Kaito na idan ban yi shelar bishara ba 17Idan na yi hidimar nan da yardar zuciyata, ina da sakamako, idan kuma ba da yaddar zuciyata ba, harwa yau akwai nauwaya akai na. 18To menene sakamako na? shi ne in yi shelar bishara kyauta, da haka ba zan yi amfani the 'yanci na cikin bishara ba 19Ko da shike ni 'yantacce ne ga duka, amma na mai da kaina bawan kowa domin in ribato masu yawa, 20Ga yahudawa, na zama bayahude, domin in ribato yahudawa, ga wadanda ke karkashin shari'a, na maishe kaina kamarsu, domin in ribato wadanda ke karkashinta. Na aikata wannan ko da shike bana karkashin shari'a 21Ga wadanda basu karkashin shari'a, na maishe kaina kamar su. Ko da shike ban rabu da shari'ar Allah ba. Amma ina karkashin dokar Almasihu. Na yi haka ne domin in ribato wadanda ba sa karkashin shari'a. 22Ga marasa karfi, na maishe kaina kamar marar karfi, domin in ribato raunana. Na mai da kaina dukan abu ga dukan mutane domin in sami zarafin da zan ribato wadansu zuwa ceto. 23Ina dukan abu sabili da bishara, domin kuma in sami albarkar da ke cikinta 24Baku sani ba mutane da dama suna shiga tsere amma daya neke karbar sakamakon, saboda haka ku yi tsere domin ku karbi sakamako. 25Dan wasa yana motsa jiki da kame kansa. Yana yi saboda ya karbi wannan sakamako mai lalacewa, amma muna tsere domin mu karbi sakamako marar lalacewa. 26Saboda haka ba na tsere ko fada haka nan kamar mai bugun iska. 27Amma ina matse jiki na in maishe shi bawa, kada bayan na yi wa wadansu wa'azi ni kuma a karshe a fitar da ni.

¿Sabías que…?
Un apóstol que rechaza el sustento
- La tradición de la Iglesia atribuye este capítulo a Pablo, quien defiende su apostolado ante quienes lo examinan, llama a sus lectores el sello de su apostolado en el Señor y reclama el derecho a la comida y a la bebida y a una esposa creyente, como hacen los demás apóstoles, los hermanos del Señor y Cefas. Dice que no ha usado ese derecho, y que prefiere ofrecer el evangelio sin costo antes que ponerle un obstáculo.Fuentes: el propio texto bíblico
- Pregunta si él y Bernabé son los únicos que deben trabajar para vivir, en lugar de ser sostenidos por el evangelio. Bernabé, "hijo de consolación", era el sobrenombre de Joses, un levita natural de Chipre, que vendió un terreno que poseía allí; el diccionario bíblico de Easton (1897) también dice que Bernabé presentó a Pablo a los apóstoles cuando Pablo regresó a Jerusalén después de su conversión.Fuentes: el propio texto bíblico · Barnabas
- Para sostener la parte del trabajador en la cosecha, cita la Ley de Moisés: "No pongas bozal al buey mientras trilla el grano", y dice que el que ara y el que trilla deben esperar participar de la cosecha. Añade que los que trabajan en el templo comen de su alimento y los que sirven al altar participan de las ofrendas, y que el Señor ha dispuesto el mismo tipo de sustento para quienes predican el evangelio.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org