1 Corintios 8
Litafi Mai-tsarki · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
1Game da abinci da ake yiwa gumakai hadaya: Mun sani cewa, “Dukanmu muna da ilimi.” Ilimi ya kan kawo takama, amma kauna tana ginawa. 2Idan wani yana tunanin ya san wani abu, wannan mutumin bai rigaya ya san abinda ya kamata ya sani ba. 3Amma idan wani yana kaunar Allah, to ya san da wannan mutum. 4Game da abincin da aka yiwa gumakai hadaya: Mun san cewa, “Gunki a duniyan nan ba wani abu bane,” kuma cewa” Babu wani Allah sai guda daya.” 5To wata kila ma a ce wadanda ake kira alloli sun kasance, ko a cikin sama ko duniya, kamar yadda akwai wadanda ake ce dasu “alloli dabam dabam a duniya ko a sama,” kamar yadda akwai “alloli da iyayengiji” da yawa. 6“Amma a wurin mu, Allah daya ne, Uban dukan duniya, daga wurinsa aka halita dukan abu, domin sa muke rayuwa, Ubangiji Yesu Almasihu daya, wanda ta wurin sa kome ya kasance, mu kuma daga wurinsa muke.” 7Amma ba kowa ke da wannan ilimi ba. Shi ya sa tun da, wadan su na bauta wa gunki, kuma suna cin wannan abincin kamar abin da aka mika wa gunki. Lamirin su ya kazantu sabo da yana da rauni. 8Amma ba abinci ke bamu tagomashi a wurin Allah ba. Ko mun ci, bamu kara karbuwan mu ba, ko ba mu ci ba, ba mu rage karbuwan mu ba. 9Amma, ka yi hatara kada 'yancin ka ya zama sanadiyar tuntuben wani mai rarraunar bangaskiya. 10Anar misali, idan wani mai rarraunar lamiri ya hango ka mai ilimi, kana cin abincin da aka mika wa gunki, ai ba ka bashi kwarin gwiwa kenan yaci abincin da aka mika wa gunki ba? 11Sabili da ganewar ka akan yanayin gumaka, dan'uwa rarrauna wanda Yesu ya mutu domin sa ya hallaka. 12Saboda haka, idan ka saba wa 'yan'uwa masu raunin a lamiri, ka yi zunubi a gaban Almasihu. 13Idan abinci zai sa dan'uwa na yayi tuntube, zan huta cin nama, domin kada in jawo wa 'yan'uwana faduwa.
¿Sabías que…?
Comida sacrificada a los ídolos
- El capítulo comienza poniendo el conocimiento junto al amor: el conocimiento envanece, pero el amor edifica. Dice que quien cree saber algo todavía no conoce como es debido conocer, mientras que quien ama a Dios es conocido por Dios.Fuentes: el propio texto bíblico
- Sobre comer comida sacrificada a los ídolos, el capítulo dice que un ídolo no es nada en el mundo y que no hay más Dios que uno, aunque se hable de muchos llamados dioses y señores. No todos tienen este conocimiento: algunos siguen tan acostumbrados a los ídolos que comen ese alimento como si fuera sacrificado a un ídolo, y su conciencia débil queda contaminada.Fuentes: el propio texto bíblico
- El capítulo advierte que la libertad puede convertirse en un tropiezo para los débiles. Si alguien de conciencia débil ve a una persona bien informada comiendo en el templo de un ídolo, esa persona puede ser animada a comer comida sacrificada a los ídolos. Quien escribe dice que, si lo que él come hace tropezar a su hermano, no volverá a comer carne.Fuentes: el propio texto bíblico
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Créditos y licencia de esta traducción
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fuente: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org