Nations Bible

Romans 9

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Gaskiya ne nake gaskiya nake fada cikin Almasihu. Ba karya nake yi ba. Lamirina, na shaida a cikin Ruhu Mai Tsarki. 2cewa ina da matukar bakin-ciki da takaici marar karewa a zuciyata. 3Dama ace, a la'anta ni, in rabu da Almasihu saboda 'yan'uwana, wato dangina da suke zuriyata bisa ga jiki. 4Sune Isra'ilawa, sun sami karbuwa, da daukaka, da baiwar shari'a, da yi wa Allah sujada, da alkawarai. 5Dukkan ubanni nasu ne daga cikinsu Almasihu ya fito bisa ga jiki- wanda shi ke Allah bisa kowa. Yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin. 6Amma ba wai alkawarin Allah ya kasa ba ne, ba dukkan Isra'ilawa ne suke Isra'ilawa na gaskiya ba. 7Haka nan, ba dukkan zuriyar Ibrahim ne 'ya'yansa ba. Amma ''ta wurin Ishiyaku ne za'a kira zuriyarka.'' 8Yana nuna mana cewa ba 'ya'yan jiki su ne 'ya'yan Allah ba. Amma 'ya'yan alkawari ne ake kirga su, kuma aka kebe su. 9Wanna ce kalmar alkawari, ''badi warhaka zan dawo, Saratu kuwa zata sami da.'' 10Amma ba wannan kadai ba, bayan Rifkatu ta dauki ciki daga gun mijinta, ubammu Ishiyaku. 11Yaran nan kafin ma a haife su, balle ma a ce sun yi wani abu mai kyau ko laifi, saboda zaben da Allah yayi, bai danganta da abin da suka yi ba, ko don aiki ba, amma don shine mai kira— 12kamar yadda Ya ce, mata, “babban zaya yiwa karamin bauta,'' haka nassi yace, 13''Kamar yadda aka rubuta: “Yakubu na ke kauna, amma Isuwa na ki shi.” 14To me zamu ce kenan? Allah ya yi rashin adalci kenan? Ko kadan. 15Gama ya ce wa Musa, ''Ina nuna jinkai ga wanda zan yi wa jinkai, zan ji tausayi ga wanda zan tausaya masa.'' 16Saboda haka, ba don wanda ke da aniya ba ne, ko kuwa wanda yake kokari ba, amma saboda Allah mai nuna jinkai. 17Gama nassi ya ce da Fir'auna, '' Saboda wannan dalilin ne, na tada kai, don in nuna ikona mai karfi a kanka, don sunana ya yadu ga dukkan duniya.'' 18Ta haka Allah ya nuna jinkansa ga wanda ya so, ya taurarar da zuciyar wanda ya ga dama. 19Za kuce mani, to don me, ''Yake kama mu da llaifi? Wa ya taba yin jayayya da nufinsa?'' 20In ma mun duba, kai mutum wanene kai da zaka ja da Allah? Ko abin da aka gina zai ce wa magininsa, ''Don me yasa ka ginani haka?'' 21Ko maginin ba shi da iko akan yimbu daya da zai gina tukunya mai daraja, wata kuma tukunyar don kowanne irin aiki? 22In ace Allah, dake niyyar nuna fushinsa da ikonsa, ya sanu, sai ya jure da matukar hakuri mai yawa da tukwanen fushi da ya shirya don hallakarwar fa? 23To ko ma ya yi haka don ya nuna yalwar daukakarsa da take dauke da alheri, wanda ya shirya don daukakarsa tun farko? 24Zai yiwu ma ya yi haka ne domin mu, mu da ya kira, ba ma daga cikin Yahudawa kadai ba, amma har ma daga cikin al'ummai? 25Kamar yadda ya ce a cikin littafin Yusha'u: ''zan kira wadanda ba mutanena ba mutanena, da kuma kaunatattunta wadanda ba kaunatattu ba. 26Zai zama kuma a inda aka ce da su, “ku ba mutanena bane, za a kisa su 'ya'yan Allah mai rai.”' 27Ishaya ya yi kira game da Isra'ila, ''in a ce yawan 'ya'yan Isra'ila zasu zama kamar yashi a bakin teku, ragowarsu ne kawai za su sami ceto. 28Ubangiji zai tabbatar da cikar kalmarsa a duniya, ba kuwa da dadewa ba. 29Yadda Ishaya ya rubuta ada, ''In da ba Ubangiji mai runduna bai bar mana zuriya ba, da zamu zama kamar Saduma, da kuma an maida mu kamar Gomarata. 30To me za mu ce kenan? Ko al'ummai, da ba sa neman adalci, sun samu adalci ta wurin bangaskiya. 31Amma Isra'ila, wadanda suka nemi adalcinsu ta wurin shari'a, ba su kai ga gaci ba. 32To don me? don ba su neme shi da bangaskiya ba, amma ta ayyuka. Sun yi tuntube a kan dutse da zai sa laifi. 33Kamar yadda aka rubuta, “Ga, shi na ajiye dutse a kan Sihiyona dutsen tuntube mai sa laifi. Ga wanda ya bada gaskiya gare shi ba zai ji kunya ba.”

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Israel and the Children of the Promise

  • These verses argue that God's word has not failed: not all who are descended from Israel are Israel, and not all of Abraham's descendants are his children. Isaac was Abraham's only son by Sarah, and the promise quoted here follows that line: offspring would be reckoned through Isaac, and at the appointed time Sarah would have a son. The name Sarah, meaning princess, was given when it was announced that she would be the mother of the promised child.Sources: the Bible text itself · Isaac · Sarah
  • The argument then turns to Rebecca's twins, conceived by one man, Isaac. Esau, the first-born, was also called Edom, "red," from the red lentil pottage for which he sold his birthright; Jacob, the younger, bears a name meaning one who follows on another's heels, or supplanter. Before the twins were born or had done anything good or bad, Rebecca was told that the older would serve the younger, and it is written, "Jacob I loved, but Esau I hated."Sources: the Bible text itself · Esau (Edom) · Jacob (Israel)
  • Isaiah, the son of Amoz, is quoted about a remnant: though the Israelites were like the sand of the sea, only the remnant would be saved, and without descendants left by the Lord of Hosts they would have become like Sodom and resembled Gomorrah. Sodom, a city in the vale of Siddim, was destroyed by fire from heaven, a destruction this chapter recalls, and no trace of it or of the other cities of the plain has been found. The chapter ends with a stumbling stone laid in Zion, the south-eastern hill of Jerusalem, which David took from the Jebusites, where he built a citadel and a palace, and which became the city of David.Sources: the Bible text itself · Isaiah · Sodom · Zion

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Zion · Today: Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 33

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.