Romans 10
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1'Yan'uwana, muradin zuciyata da dukkan addu'oi na ga Allah dominsu shine don su sami ceton. 2Domin na shaida game da su cewa suna da kwazo game da Allah, amma ba a kan sani ba. 3Don, ba su da sani akan adalcin Allah, suna kokarin tabbatar da adalcin kansu. Ba su bada kan su ga adalcin Allah ba. 4Gama Almasihu shi ne cikar doka zuwa ga adalci ga dukkan wadanda suka gaskata. 5Musa kam ya rubuta game da adalci da zai samu ta shari'a: ''mutumin da ya aikata adalcin shari'a, zai rayu ta wurin wannan adalcin.'' 6Amma adalcin da ya zo ta wurin bangaskiya yace, ''Kada ku ce a zuciyarku, wa zai hau zuwa sama?''(don ya sauko da Almasihu kasa). 7Kada ku ce, ''Wa zai gangara zuwa kasa?'' (Wato wa zai fito da Almasihu daga cikin matattu). 8Amma me yake cewa? “ kalmar tana kusa da kai a cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka.” Wato kalmar bangaskiya, wadda muke shaidawa. 9Don idan da bakinka, ka shaida Yesu Ubangiji ne, kuma ka gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto. 10Don da zuciya ne mutum yake gaskatawa zuwa ga adalci, da kuma baki ne yake shaida zuwa ga ceto. 11Don nassi na cewa, ''Duk wanda ya gaskata da shi ba zai ji kunya ba,'' 12Gama ba bambanci tsakanin Bayahude da Ba'al'ume. Gama dukkansu Ubangijinsu daya ne, Shi mayalwaci ne ga dukkan wanda ya kira shi. 13Duk wanda ya kira sunan Ubangiji zai sami ceto. 14To ta yaya zasu kira ga wanda basu gaskata ba? Kuma ta yaya zasu gaskata ga wanda ba su taba jin labarinsa ba? 15Kuma ta yaya zasu ji in ba ayi masu wa'azi ba? Kuma ta yaya zasu yi wa'azin in ba an aike su ba? - Kamar yadda yake a rubuce, “Ina misalin kyau na kafafun wadanda ke shaida labarin farin ciki na abubuwa masu kyau!” 16Amma ba dukkansu ne suka ji bishara ba. Gama Ishaya ya ce, ''Ubangiji, wa ya gaskata da sakon? 17Saboda haka bangaskiya na zuwa ta wurin ji, jin kuwa daga maganar Almasihu. 18Amma na ce, “ko basu ji ba ne? I, tabbas'' muryarsu ta kai dukkan duniya, kuma kalmominsu sun kai har karshen duniya.'' 19yau, na ce, ''Ko Isra'ila basu sani ba ne?'' Da farko Musa ya ce, “Zan sa kuyi fushi da kishi da abin da ba al'umma ba. Abin da nake nufi nan shine al'ummar da basu da fahinta, zan more su, in tayar maku da hankali.'' 20Amma Ishaya da karfin hali ya ce, ''Ga wadanda basu neme ni ba suka same ni. Na bayyana ga wadanda basu nemi ni ba. 21''Amma ga Isra'ila kam ya ce, '' na mika hannu na ga masu rashin biyayya dukkan tsawon rana, domin su mutane ne masu taurin kai.''

Did you know?
Righteousness by Faith
- The chapter opens with a heart's desire and a prayer to God for the Israelites' salvation. The writer testifies that they are zealous for God, but not on the basis of knowledge: because they were ignorant of God's righteousness and sought to establish their own, they did not submit to God's righteousness. Christ, it says, is the end of the law, to bring righteousness to everyone who believes.Sources: the Bible text itself
- On the righteousness that is by the law, Moses writes, "The man who does these things will live by them." The righteousness that is by faith says instead that the word is near, in the mouth and in the heart—the word of faith being proclaimed: if you confess with your mouth, "Jesus is Lord," and believe in your heart that God raised him from the dead, you will be saved. There is no difference between Jew and Greek, for the same Lord is Lord of all.Sources: the Bible text itself
- The chapter quotes Isaiah, "Lord, who has believed our message?" and Isaiah's bold words, "I was found by those who did not seek Me," and, concerning Israel, "All day long I have held out My hands to a disobedient and obstinate people." Isaiah was the son of Amoz and prophesied during the reigns of Uzziah, Jotham, Ahaz, and Hezekiah. Easton's Bible Dictionary (1897) says he probably began his career in 762 B.C.Sources: the Bible text itself · Isaiah
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org