Nations Bible

Mark 16

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Bayan ranar assabaci, Maryamu Magadaliya da Maryamu uwar Yakubu da Salomi, suka sayo man shafawa mai kamshi domin shafe jikin Yesu saboda jana'iza. 2Da safiyar ranar farko ta mako sai suka tafi kabarin a dai dai fitowar rana. 3Suna magana a tsakaninsu suna cewa, wanene zai gangarar da dutsen da aka rufe bakin kabarin da shi?” 4Da suka daga ido, sai suka ga an riga an gangarar da dutsen, domin yana da girma. 5Da suka shiga cikin kabarin sai ga wani saurayi saye da farar tufa, yana zaune a hannun dama, suna mamaki. 6Sai ya ce masu, “Kada ku ji tsoro. Kuna neman Yesu banazare, wanda aka giciye. Ya tashi! Baya nan. Ku duba wurin da aka kwantar dashi. 7Sai ku je, ku gaya wa almajiransa da Bitrus cewa ya rigaya ya yi gabanku zuwa Galili. A can zaku ganshi, kamar yadda ya fada maku.” 8Suka fita daga cikin kabarin da gudu suna rawar jiki da mamaki, ba su cewa kowa komai ba domin suna jin tsoro. 9Da safiyar ranar farko ta mako ya fara bayyana kansa ga Maryamu Magadaliya wadda ya kori aljannu guda bakwai daga cikinta. 10Sai ta tafi ta shaida wadanda suke tare da shi suke makoki da kuka. 11Sai suka ji cewa ya tashi kuma ta ganshi, amma basu gaskata ba. 12Bayan wadannan al'amura ya bayana kansa ta wata siffa ga mutum biyu sa'ilin da suke tafiya akan hanya. 13Sai suka tafi suka gaya wa sauran almajiransa, duk da haka basu gaskata ba. 14Bayan wani lokaci, Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa su goma sha daya, ya tsauta masu saboda rashin gaskatawa da taurin zuciya, bayansun ji daga wadanda suka ganshi bayan ya tashi daga matattu. 15Sai ya umarcesu cewa “Ku tafi cikin duniya ku yi bishara ga dukan halitta. 16Wanda ya ba da gaskiya aka kuma yi masa baftisma, zaya sami ceto, wanda baya bada gaskiya ba za ya hallaka. 17Wadannan alamu za su kasance da wadanda suka gaskata; a cikin sunana, za su fidda aljannu, za su yi magana da sabbin harsuna. 18Za su dauki macizai da hannayesu, idan sun sha guba ba ta cutar dasu ba, za su dibiya hannayensu ga marasa lafiya, za su sami warkaswa.” 19Bayan Ubangiji ya gama magana da su, sai aka dauke shi zuwa sama in da zai zauna a hannun dama na Allah. 20Almajiransa kuma suka tafi ko'ina suna sheilar bishara. Ubangiji kuma yayi aiki tare da su, yana tabbatar da kalma ta wurin ayukan al'ajiba tare da su.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

The Empty Tomb and the Risen Jesus

  • When the Sabbath was over, Mary Magdalene, Mary the mother of James, and Salome bought spices so they could anoint Jesus’ body, and they went to the tomb just after sunrise. Salome was the wife of Zebedee and the mother of James and John; she had witnessed the crucifixion and was present with the other women at the tomb.Sources: the Bible text itself · Salome
  • The name Mary Magdalene comes from Magdala, her birthplace, and was used to distinguish her from the other Marys of the Gospels. Easton's Bible Dictionary (1897) notes that a mistaken notion has identified her with the woman called a sinner in Luke 7. This chapter says that Jesus had driven seven demons out of her and that, after he had risen, he appeared first to her.Sources: Mary Magdalene · the Bible text itself
  • A young man in the tomb calls Jesus “the Nazarene” and tells the women that he is going ahead of the disciples into Galilee, where they will see him. Nazareth, the home of Joseph and Mary, is not mentioned in the Old Testament; its name is generally supposed to be the Greek form of the Hebrew netser, “shoot” or “sprout,” though some connect it with the hill behind the town and the Hebrew notserah, “one guarding or watching.” Galilee means “circuit,” and because it long remained occupied by its original inhabitants it came to be called “Galilee of the Gentiles.”Sources: the Bible text itself · Nazareth · Galilee

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Nazareth · 32.702, 35.298 · verse 6
  • Galilee · 32.760, 35.527 · verse 7
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 12

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.