Nations Bible

Luke 1

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

About this book

About Luke

  • Easton's Bible Dictionary (1897) presents the evangelist Luke as a Gentile; the date and circumstances of his conversion are unknown. According to his own statement, Easton notes, he was not an eyewitness and minister of the word from the beginning. Easton thinks it probable that he was a physician in Troas, converted there by Paul, to whom he then attached himself.Sources: Easton: Luke
  • That dictionary does not date the Gospel. It places Luke with Paul at Philippi, later as his companion on the journey from Philippi to Jerusalem, then absent during the imprisonments at Jerusalem and Caesarea, and present again when Paul set out for Rome, remaining until the close of the first imprisonment; the last notice of the beloved physician is in 2 Timothy 4:11.Sources: Easton: Luke
  • Under the Romans in the time of Jesus, Judea was the southernmost of the three divisions of Palestine and part of the province of Syria. Pontius Pilate, sixth procurator of Judea from A.D. 26 to 36, had his headquarters at Caesarea and often went up to Jerusalem; his rule covered the ministries of John the Baptist and of Jesus. Herod Antipas, Herod's son by Malthace, is named in Luke's narrative.Sources: Judea · Pontius Pilate · Herod Antipas
  • Luke's opening narrative concerns John the Baptist, of priestly descent: his father Zacharias was a priest of the course of Abia, and his mother Elisabeth was of the daughters of Aaron; John's birth came six months before Jesus's. Mary, wife of Joseph, of the tribe of Judah and the lineage of David, was living at Nazareth when the angel Gabriel announced that she would be the mother of the Messiah; she afterward visited her cousin Elisabeth. The entry on Mary states that her genealogy is given in Luke 3.Sources: John the Baptist · Mary (Mother of Jesus) · Nazareth
  • Easton cites many passages in Luke's writings and in Paul's letters as showing the extent and accuracy of Luke's medical knowledge. After Jesus was expelled from Nazareth, Capernaum, a Galilean city not mentioned in the Old Testament, became his own city and the scene of many acts of his life. Galilee had long been known as Galilee of the Gentiles.Sources: Easton: Luke · Capernaum · Galilee

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

1Mutane da dayawa sun yi kokarin rubutu akan abubuwan da suka cika a tsakaninmu, 2kamar yanda suka danka mana su, wadanda tun daga farko suka zama shaidu da idanunsu kuma manzanni ne na sakon. 3Sabili da haka, ni ma, bayan da na yi bincike da kyau akan yanayin wadannan abubuwa tun da farko na ga ya yi kyau in rubuta wadannan abubuwa bi da bi ya mafi girmaTiyofilas. 4Ya zama haka domin ka san gaskiyar abin da aka koya maka ne. 5A cikin zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, akwai wani firist mai suna Zakariya, daga yankin Abija. Matarsa daga cikin yaya mata na zuriyar Haruna ce, kuma sunan ta Alisabatu ne. 6Dukan su biyu masu adalci ne a gaban Allah; marasa zargi a tafiyarsu cikin dukan dokoki da farilan Ubangiji. 7Amma ba su da da, domin Alisabatu ba ta haihuwa, kuma a wannan lokacin dukansu sun tsufa kwarai. 8Ya zama kuma a lokacin da Zakariya yana gaban Allah, yana yin hidimar sa ta firist bisa ga tsari da ka'idar aikinsa. 9Bisa ga al'adar zaben firist da zai yi hidima, an zabe shi ta wurin kuri'a ya shiga cikin haikalin Ubangiji domin ya kona turare. 10Dukan taron Jama'a suna addu'a a waje a sa'adda ake kona turaren. 11A lokacin, mala'ikan Ubangiji ya bayana a gare shi yana tsaye a gefen daman bagadi na turaren. 12Zakariya ya firgita sa'adda ya gan shi; tsoro ya kama shi. 13Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya, domin an ji addu'ar ka. Matar ka Alisabatu za ta haifa maka da. Za ka kira sunansa Yahaya. 14Za ka yi murna da farin ciki, kuma da yawa za su yi murna da haifuwarsa. 15Domin zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba zai sha ruwan inabi ba ko wani abu mai sa maye, kuma zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun daga cikin cikin mahaifiyarsa. 16Kuma mutanen Isra'ila da yawa za su juya zuwa ga Ubangiji Allahnsu. 17Zai yi tafiya a gaban Unbangiji a cikin ruhu da ikon Iliya. Zai yi haka domin ya juya zuciyar Ubanni zuwa ga 'ya'yansu, domin marasa biyayya su yi tafiya a cikin tafarkin adalai. Don ya shirya wa Ubangiji mutanen da aka shirya dominsa.” 18Zakariya ya ce wa mala'ikan, “Ta yaya zan san wannan? Ga shi na tsufa kuma matata tana da shekaru da yawa.” 19Mala'ikan ya amsa ya ce masa, “Nine Jibra'ilu, wanda ke tsaye a gaban Allah. An aiko ni in gaya maka wannan labari mai dadi. 20Kuma duba, za ka zama bebe, ba za ka iya magana ba, sai ran da wadannan abubuwa suka cika. Ya zama haka domin ba ka gaskanta da kalmomina ba, wadanda za su cika a daidai lokacin.” 21Sa'adda mutane suke jiran Zakariya. Sun yi mamaki yadda ya dauki lokaci sosai a cikin haikali. 22Amma da ya fita, bai iya yin magana da su ba. Sun gane da cewa ya ga wahayi lokacin da yake cikin haikali. Ya ci gaba da yi masu alamu, ba ya magana. 23Ya zama bayan da kwanakin hidimarsa suka kare, ya tafi gidansa. 24Bayan kwanakin nan, matarsa Alisabatu ta samu juna biyu. Ta boye kanta har na watani biyar. Ta ce, 25“Wannan shi ne abin da Allah ya yi mani da ya dube ni domin ya dauke kunyata a gaban jama'a.” 26A cikin watan ta na shidda, an aiki Mala'ika Jibra'ilu daga wurin Allah zuwa wani birni a Galili mai suna Nazarat, 27zuwa ga wata budurwa wanda aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu. Shi dan zuriyar Dauda ne, kuma ana kiran budurwar Maryamu. 28Ya zo wurin ta ya ce, “A gaishe ki, ke da ki ke da tagomashi sosai! Ubangiji yana tare da ke. 29Amma ta damu kwarai da wadannan kalmomi sai ta yi tunani ko wacce irin gaisuwa ce wannan. 30Mala'ikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, domin kin samu tagomashi a wurin Allah. 31Duba, za ki sami juna biyu, za ki haifi da. Za ki kira sunansa 'Yesu'. 32Zai zama mai girma, kuma za a ce da shi Dan Allah Madaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dauda. 33Zai yi mulkin dukkan gidan Yakubu har abada, kuma mulkinsa ba shi da iyaka.” 34Maryamu ta ce wa mala'ikan, “Yaya wannan zai faru, tun da shike ni ban san namiji ba?” 35Mala'ikan ya amsa ya ce mata, “Ruhu Mai-tsarki zai sauko a kan ki, kuma ikon Madaukaki zai lullube ki. Sabili da haka, za a kira mai tsarkin da za ki haifa Dan Allah. 36Ki kuma duba, ga 'yar'uwarki Alisabatu ta samu juna biyu a tsufanta. Watannin ta shida kenan, ita wadda aka kira ta bakarariya. 37Gama babu abin da ba shi yiwuwa a wurin Allah.” 38Maryamu ta ce, “To, ni baiwar Ubangiji ce. Bari ya faru da ni bisa ga sakonka.” Sai mala'ikan ya bar ta. 39Sai Maryamu ta tashi da sauri a cikin kwanakin nan, zuwa kasa mai duwatsu, zuwa wani birni a Yahudiya. 40Ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Alisabatu. 41Ya zama sa'adda Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, sai dan da ke cikinta ya yi tsalle, an cika Alisabatu kuma da Ruhu Mai Tsarki. 42Ta daga murya, ta ce, “Mai albarka kike a cikin mata, kuma mai albarka ne dan cikinki. 43Kuma don me ya faru da ni da uwar Ubangijina ta ziyarce ni? 44Kuma duba, da na ji karar gaisuwan ki sai dan ciki na ya yi tsalle domin murna. 45Kuma mai albarka ce wadda ta gaskanta cewa abubuwan da aka alkawarta mata daga wurin Ubangiji za su cika. 46Maryamu ta ce, “Zuciyata ta yabi Ubangiji, 47kuma ruhu na ya yi murna da Allah mai ceto na.” 48Domin ya dubi kaskancin baiwarsa. Duba, daga yanzu, dukkan tsararraki za su ce da ni mai albarka. 49Domin shi madaukaki ya yi mani manyan abubuwa, kuma sunansa Mai Tsarki ne. 50Jinkansa ya tabbata daga tsara zuwa tsara wadanda suke girmama shi. 51Ya nuna karfinsa da hannuwansa; ya warwatsa ma su girman kai game da tunanin zuciyarsu. 52Ya nakasar da magada daga kursiyoyinsu, ya kuma fifita nakasassu. 53Ya ciyar da mayunwata da abubuwa masu kyau, amma ya aiki attajirai wofi. 54Ya ba da taimako ga bawan sa Isra'ila, domin ya tuna ya kuma nuna jinkai 55(kamar yanda ya fada wa ubaninmu) ga Ibrahim da zuriyarsa har abada.” 56Maryamu ta zauna da Alisabatu tsawon watanni uku sai ta koma gidanta. 57Da lokaci yayi da Alisabatu za ta haifi danta, ta kuma haifi da namiji. 58Makwabtanta da 'yan'uwanta sun ji cewa Ubangiji ya ribanbanya jinkansa akanta, sai suka yi murna tare da ita 59Ya zama akan rana ta takwas, sun zo domin a yi wa yaron kaciya. Da sun kira sunansa “Zakariya” kamar sunan ubansa, 60amma mahaifiyarsa ta amsa ta ce, “A'a, za a kira shi Yahaya.” 61Suka ce mata, “Babu wani a cikin danginku wanda ake kira da wannan suna.” 62Sun nuna alama ga ubansa bisa ga yanda ya ke so a rada masa suna. 63Ubansa ya nemi a ba shi allon rubutu, sai ya rubuta, “Sunansa Yahaya.” Dukan su suka yi mamaki kwarai da wannan. 64Nan take, sai bakinsa ya bude kuma harshensa ya saki. Ya yi magana ya kuma yabi Allah. 65Tsoro ya kama dukan wadanda suke zama kewaye da su. Sai labarin ya bazu cikin dukan kasar duwatsu ta Yahudiya. 66Kuma dukan wadanda suka ji su, sun ajiye su a cikin zuciyarsu, suna cewa, “To me wannan yaro zai zama ne?” Domin hannun Ubangiji yana nan tare da shi. 67Ruhu Mai-tsarki ya cika mahaifinsa Zakariya sai ya yi anabci cewa, 68“Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra'ila domin ya zo ya taimaki mutanen sa kuma ya yi aikin ceto domin su.” 69Ya ta da kahon ceto dominmu daga gidan bawansa Dauda, daga zuriyar Dauda bawansa, 70kamar yadda ya fada ta bakin annabawansa tsarkaka tun zamanin zamanai. 71Zai kawo mana ceto daga magabtan mu da kuma daga hannun makiyanmu. 72Zai yi haka domin ya nuna jinkai ga ubaninmu ya kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki, 73rantsuwar da ya fada wa ubanmu Ibrahim. 74Ya rantse zai yardar mana, bayan da an kubutar da mu daga hannun makiyanmu, mu bauta masa ba tare da tsoro ba, 75a cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakin ranmu. 76I, kai kuma, yaro, za a kira ka annabi na Madaukaki, domin za ka tafi gaban fuskar Ubangiji ka shirya hanyoyinsa, ka shirya mutane domin zuwansa, 77domin ba mutanensa ilimin ceto ta wurin gafarar zunubansu. 78Wannan zai faru ne domin girman jinkan Allahnmu, sabili da hasken rana daga bisa za ya zo wurinmu, 79domin haskakawa akan wadanda ke zaune a cikin duhu da kuma cikin inuwar mutuwa. Zai yi hakan nan domin ya kiyaye kafafunmu zuwa hanyar salama. 80Yaron ya yi girma ya kuma zama kakkarfa a cikin ruhu, yana kuma cikin jeji sai ranar bayyanuwarsa ga Isra'ila.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Announcements of John and Jesus

  • Zechariah served in the priestly division of Abijah, the eighth of the twenty-four courses into which David had divided the priests. Only four of those groups returned from the Exile and were then redistributed under the old names. Priests served at the temple twice a year, for one week at a time, and lots were drawn each day for the solemn offering of incense.Sources: Zacharias · the Bible text itself
  • The angel who stood at the right side of the altar of incense named himself Gabriel and said that he stands in the presence of God. The same name designates the angel sent to Daniel to explain the vision of the ram and the he-goat and to give the prediction of the seventy weeks, and Gabriel also announced to Mary that she would bear a son.Sources: Gabriel · the Bible text itself
  • Elizabeth was a descendant of Aaron. Mary, of the tribe of Judah and the line of David, was connected with her by marriage and went from Nazareth in Galilee, a town not mentioned in the Old Testament, to visit her in the hill country of Judah.Sources: Elisabeth · Mary (Mother of Jesus) · Nazareth · the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Judea · Today: Judea 1 · 31.777, 35.234 · verses 5, 39, 65
  • Holy Place · Today: on Mount Moriah · 31.778, 35.236 · verses 9, 21, 22
  • Galilee · 32.760, 35.527 · verse 26
  • Nazareth · 32.702, 35.298 · verse 26

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.