Matthew 11
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa gargadi, sai ya bar wannan wuri, ya tafi biranensu domin yayi koyorwa, da wa'azi. 2Da Yahaya mai baftisma ya ji daga kurkuku irin ayyukan da Yesu ke yi, sai ya aika sako ta wurin almajiransa. 3Ya ce masa. “Kai ne mai zuwa”? ko mu sa ido ga wani. 4Yesu ya amsa ya ce masu, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da ku ka gani da abin da ku ka ji. 5Makafi suna samun ganin gari, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na jin magana kuma, ana tada matattu, mabukata kuma ana ba su bishara. 6Kuma mai albarka ne wanda baya tuntube sabili da ni. 7Bayan wadannan sun tafi, sai Yesu ya fara wa jama'a jawabi game da Yahaya mai baftisma, yana cewa, “Me ake zuwa gani a jeji - ciyawa ce da iska ke busawa? 8Shin menene kuke zuwa gani a jeji - mutum mai sanye da tufafi masu laushi? Hakika, masu sa tufafi masu laushi suna zaune ne a fadar sarakuna. 9Amma me ku ke zuwa gani, annabi? Hakika ina fada maku, fiye ma da annabi. 10Wannan shine wanda aka rubuta game da shi, 'Duba, ina aika manzona, wanda za ya tafi gabanka domin ya shirya maka hanya inda za ka bi'. 11Ina gaya maku gaskiya, cikin wadanda mata suka haifa, babu mai girma kamar Yahaya mai baftisma. Amma mafi kankanta a mulkin sama ya fi shi girma. 12Tun daga kwanakin Yahaya mai baftisma zuwa yanzu, mulkin sama yana shan gwagwarmaya, masu husuma kuma su kan kwace shi da karfi. 13Gama dukan annabawa da shari'a sun yi annabci har zuwa lokacin Yahaya. 14kuma in zaku karba, wannan shine Iliya wanda za ya zo. 15Wanda ke da kunnuwan ji, ya ji. 16Da me zan kwatanta wannan zamani? Ya na kamar yara masu wasa a kasuwa, sun zauna suna kiran juna 17suna cewa mun busa maku sarewa baku yi rawa ba, mun yi makoki, baku yi kuka ba. 18Gama Yahaya ya zo, baya cin gurasa ko shan ruwan inabi, sai aka ce, “Yana da aljannu”. 19Dan mutum ya zo yana ci yana sha, sai aka ce, 'Duba, ga mai hadama, mashayi kuma, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!' Amma hikima, ta wurin aikin ta ake tabbatar da ita. 20Sannan Yesu ya fara tsautawa biranen nan inda ya yi yawancin ayukansa, domin ba su tuba ba. 21“Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka. 22Amma zai zama da sauki a kan Taya da Sidon a ranar shari'a fiye da ku. 23Ke kafarnahum, kina tsammani za a daukaka ki har zuwa sama? A'a za a saukar da ke kasa zuwa hades. Gama in da an yi irin al'ajiban da aka yi a cikin ki a Sodom, da tana nan har yanzu. 24Amma ina ce maku, za a saukaka wa Sodom a ranar shari'a fiye da ku.” 25A wannan lokaci Yesu ya ce, “Ina yabon ka, ya Uba, Ubangijin sama da kasa, domin ka boye wa masu hikima da fahimta wadannan abubuwa, ka bayyana wa marasa sani, kamar kananan yara. 26I, ya Uba gama wannan shine ya yi daidai a gare ka. 27An mallaka mani dukan abu daga wurin Ubana. Sannan babu wanda ya san Dan, sai Uban, babu kuma wanda ya san Uban, sai Dan, da duk wanda ya so ya bayyana masa. 28Ku zo gare ni, dukanku masu wahala da fama da nauyin kaya, ni kuma zan ba ku hutawa. 29Ku dauki karkiya ta ku koya daga gare ni, gama ni mai tawali'u ne da saukin hali a zuciya, sannan zaku sami hutawa ga rayukanku. 30Gama karkiyata mai sauki ce, kaya na kuma ba shi da nauyi.”

Did you know?
John's question and the cities that did not repent
- From prison, John sent his disciples to ask whether Jesus was the one who was to come. Jesus told the crowds that John was more than a prophet—the messenger sent ahead to prepare the way—and, if they were willing to accept it, the Elijah who was to come. A Bible dictionary calls John the forerunner and says his mission was already the subject of prophecy, citing Isaiah 40:3 and Malachi 3:1; it also introduces Elijah as the Elias of the New Testament.Sources: the Bible text itself · John the Baptist · Elijah
- Jesus then denounced Chorazin, Bethsaida, and Capernaum, where most of his miracles had been performed, because they did not repent. A dictionary identifies Chorazin with modern Kerazeh, about two and a half miles up the Wady Kerazeh from Capernaum, and says that Capernaum, absent from the Old Testament, became Jesus' own city after he left Nazareth. It places Bethsaida on the east side of the lake, two miles up the Jordan in Gaulonitis, enlarged by Philip the tetrarch and named Julias after the emperor's daughter, though some have supposed there was only one Bethsaida, near where the Jordan enters the lake.Sources: the Bible text itself · Chorazin · Capernaum · Bethsaida
- He set those cities against Tyre and Sidon, which he said would have repented long ago in sackcloth and ashes, and against Sodom, which he said would have remained to this day. Sidon, on the Mediterranean coast about twenty-five miles north of Tyre, was the oldest Phoenician city there and the mother city of Tyre. A dictionary says the commerce of the whole world was gathered into Tyre's warehouses, and that Sodom, in the vale of Siddim, was destroyed by fire from heaven so completely that no trace of it has been found.Sources: the Bible text itself · Sidon · Tyre · Sodom
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Galilee · 32.760, 35.527 · verse 1
- Sidon · Today: Sandikli archaeological site in Sidon · 33.561, 35.372 · verses 21, 22
- Tyre · 33.271, 35.196 · verses 21, 22
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org