Nations Bible

Matthew 10

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Yesu ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da kazaman ruhohi, su warkar da kowacce irin cuta da rashin lafiya. 2To yanzu ga sunayen manzanin nan goma sha biyu. Na farkon shine, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, da Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya; 3Filibus, da Bartalamawus, da Toma da Matiyu mai karbar haraji da Yakubu dan Halfa, da Taddawus; 4Saminu Bakairawane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi. 5Sha biyun nan su ne Yesu ya aika, ya yi masu umarni ya ce, ''Kada ku shiga wajen al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa. 6Sai dai ku je wurin batattun tumaki na gidan Isra'ila. 7Sa'adda kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, 'Mulkin Sama ya kusato'. 8Ku warkar da marasa lafiya, ku tada matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljanu. Kyauta kuka samu ku ma ku bayar kyauta. 9Kada ku rike zinariya, ko azurfa, ko tagulla a jakarku. 10Kada kuma ku dauki zabira a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci abincin sa. 11Kowanne birni, ko kauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma zauna a wurin har lokacin da za ku tashi. 12In za ku shiga gida ku ce, salama a gareku. 13Idan gidan akwai dan salama, salamarku za ta ta tabbata a gare shi. Idan kuwa babu, salamarku za ta komo maku. 14Ga wadanda su ka ki karbar ku ko sauraron ku, idan za ku fita garin ko gidan, sai ku karkade kurar kafafunku. 15Hakika, ina gaya maku, a ranar shari'a za a fi rangwanta wa kasar Saduma da ta Gwamrata a kan wannan birni. 16''Duba, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai, don haka sai ku zama masu wayo kamar macizai, da kuma marasa barna kamar kurciyoyi. 17Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi maku bulala a majami'unsu. 18Za su kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku bada shaida a gabansu, da kuma gaban al'ummai. 19Idan har sun bada ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku fada, domin za a ba ku abin da za ku fada a lokacin. 20Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku. 21Dan'uwa zai ba da dan'uwansa a kashe shi, uba kuwa dansa. 'Ya'ya kuma za su tayarwa iyayensu, har su sa a kashe su. 22Kowa kuma zai ki ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har karshe, zai tsira. 23In sun tsananta maku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Hakika ina gaya maku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Dan Mutum zai zo. 24Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba yafin ubangijinsa. 25Dai dai ne almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira mai gida Ba'alzabuba, za su kuma bata mutanen gidansa! 26Don haka kada kuji tsoron su, domin ba abin da yake boye da ba za a bayyana ba. 27Abin da nake fada maku a asirce, ku fada a sarari. Abin da kuma kuka ji a cikin rada, ku yi shelarsa daga kan soraye. 28Kada ku ji tsoron masu kisan jikin mutum, amma ba sa iya kashe rai. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon kashe jiki ya kuma jefa rai cikin jahannama. 29Ba 'yan tsuntsaye biyu ake sayarwa akan kobo ba? Ba ko daya a cikin su da zai fadi kasa ba tare da yardar Ubanku ba. 30Ai, ko da gashin kan ku ma duk a kidaye yake. 31Kada ku ji tsoro. Gama darajarku ta fi ta tsuntsaye masu yawa. 32''Saboda haka duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, ni ma zan yi shaidar sa a gaban Ubana wanda ya ke cikin Sama. 33Amma duk wanda ya yi musun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi musun sanin sa a gaban Ubana da yake cikin Sama.'' 34''Kada ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. Ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi. 35Domin na zo ne in hada mutum da ubansa gaba, 'ya da uwatarta, mata da kuma surukarta. 36Zai zama na kuma magabtan mutum su ne mutanen gidansa. 37Dukan wanda ya fi son mahaifinsa ko mahaifayarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son dansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. 38Wanda kuma bai dauki gicciyensa ya biyo ni ba, bai cancanci zama nawa ba. 39Dukan mai son ya ceci ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, yana ceton sa ne. 40''Wanda ya marabce ku, ya marabce ni ke nan. 41Wanda ya marabce ni kuwa, ya marabci wanda ya aiko ni. Wanda ya marabci annabi domin shi annabi ne, zai karbi lada kamar na annabi. Wanda kuma ya marabci mai adalci saboda shi mai adalci ne, zai sami lada kamar na mai adalci. 42Kowa ya ba daya daga cikin 'yan kananan nan, ko da kofin ruwan sanyi ya sha, domin shi almajirina ne, hakika, Ina gaya maku, ba zai rasa ladarsa ba.''

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

The Twelve Sent on Mission

  • Simon, called Peter, and his brother Andrew—the first pair named among the twelve—were fishermen from Bethsaida, on the western coast of the Sea of Galilee. James and John, listed next, were sons of Zebedee, a Galilean fisherman who had his own boats and hired servants.Sources: the Bible text itself · Simon Peter · Andrew · Zebedee
  • Matthew, identified in the list as the tax collector, was the son of Alphaeus and had formerly been known as Levi; he collected taxes at Capernaum, and the name Matthew means “gift of God.” Thomas, named beside him, was also called Didymus, the Greek equivalent of the Hebrew name, meaning “twin.” Bartholomew means “son of Tolmai” and is generally supposed to have been the same person as Nathanael.Sources: the Bible text itself · Matthew · Thomas · Bartholomew
  • Jesus warns that the day of judgment will be more bearable for Sodom and Gomorrah than for a town that refuses the twelve apostles. Easton's Bible Dictionary (1897) describes those cities of the plain of Siddim as destroyed by fire and proverbial for wickedness, and places them, probably close together, near the northern end of what is now the Dead Sea.Sources: the Bible text itself · Sodom · Gomorrah

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.